← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 146

Sashe 121

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*Bauchi*.
Ina falo kan sallaya na idar da la'asar ina jan tasbaha. Hawaye kuma sai sintiri suke yi. Yayin da Tijjani yake zaune babu sukuni a tare da shi. Yara kuma suna islamiya.
Na daga hannuwana sama a fili na ce "Allah kai ne mai sarrafa zuciya, Ubangiji ka sarrafa mini ita ta zama mai hak'uri, Allah ka mini baiwa da juriyar shanye ko wacce irin damuwa ba tare da hakan ya tab'a imanina da lafiyata ba. Ina rokon a cire mini damuwa akan wannan al'amarin domin na zama cikin masu imani da abin da ka hukunta. Allah ka warware mini dukkan abin da zai tunkare ni na sharri. Allah ka bawa Mijina lafiya, ka k'ara masa arziki, ka kare shi daga dukkan mummunar kaddara. Ina rokon a shirya zuriata, a tsare mini su, a kuma sanya su a cikin bayi na gari. Allah ka jik'an iyayena ka musu tukuici da aljanna."
Na sake yin salatai da istigifati sannan na shafa.
Na jingina da bango ina ta sakin ajiyar zuciya domin gabad'aya ji nake tamkar na ciro ta, ko na huta da azababben ciwon da nake ji.
Ya sassauta murya ya ce "Asiya na gode miki. Ki cigaba da yi mini addu'a dan Allah. Ina ji a jikina bani da lafiya. Na kasa gane kaina, ki yi hakuri da ikon Ubangiji komai zai faru bazan bar ki ba Asiya".
Cikin kuka na ce "Bari na nawa Tijjani? Sau nawa zaka ga ina kuka ka banzantar da ni, sau nawa kake sanadin sa ni kuka? A da na dauka duk lalacewar giwa ta fi k'arfin kiyashi ya ja ta. Ashe sannu a hankali idan suka yi taron dangi sai su jata su kacaccalata. Amma babu komai na barwa Allah ya zame mini garkuwa."
Ya tsugunna a gabana ya ruko hannuna a tausashe ya ce "Ba dan ki gamsu ba, ina rantse miki da Ubangijin Al-arshi bana jin so ko wacce mace da sunan soyayya ko sha'awa a zuciyata sai ke Asiya. Amma bansan me yasa nake jin zuciyata na tafarfasa a dalilin Nasiba ba. Ina jin idan ban aure ta ba bazan samu nutsuwa ba har abada. Ki yi hak'uri kada ki juya mini baya a cikin wannan halin da nake ciki. Masifu sun dabaibaye ni, ikon Allah kad'ai yake rik'e da tunanina. Amma gabadaya bani da sukuni.
A gida babu nutsuwa a tsakaninmu, a wajen sana'a ta jifana ake yi. Ga shi an kulle mini zuciya da tunanina. Babban tashin hankalina yadda Baban Marina ya shirya kwace mini ke. Dan Allah little kada ki barmu ni da twins. Ya ya ake son mu yi, k'arfin hali kawai nake yi, amma ni yanzu har na fara fatan mutuwa ta dauke ni na huta da wannan dambarwar".
Na kasa kwace hannuna. Wani irin abu ya dinga taso mini. Na gasgata ina son Tijjani k'warai da gaske. Domin saukowar da ya yi, ya mini magana ta rarrashi da tausayawa sai na ji k'ullin zuciyata ya fara kunce wa.
Na fara kuka na ce "Ta ya ya zan yarda kana sona Tijjani alhalin kullum sai ka mini abin da zai sa ni kuka? Yaushe rabon da ka zauna ka ji damuwata, hatta yaran nan sun san ka canja mini. A gabansu kake rufe ido ka tsigale ni haka siddan. Kullum a cikin yi musu karyar baka da lafiya na ke dan kada su kullace ka. Yaushe rabon ka da nemi wani abu a tare da ni, me kake so na fahimta tunda nasan baka da hak'uri a wannan fagen?".
Ya tsananta rikon da ya yi mini ya ce Na gode da kike rufa mini asiri a idon y'aya'na. Allah ya yi miki albarka. Sannan Allah ne shaidar furucin Baban Marina da yake nuni zai k'wace mini ke ya sanya na rasa k'arfi a tare da ni. Wallahi bana aikata komai na b'arna Asiya".
Ban ce komai ba ya sake sassauta murya ya ce "Kin tab'a mini alkawarin ba zaki sake fita daga gidan nan ba sai da izinina, ina son ki samar mini da nutsuwa ta hanyar tabbatar mini har yanzu ma ba zaki fita babu yardata ba. Wallahi Asiya ke ce Tijjani. Ke ce nutsuwata, ke ce rufin asirina idan har kika bar ni, ina tabbatar miki komai zai kwace mini. Masu son nawa ma sai sun guje ni, saboda zan rasa abin da suke so a tare da ni."
Na kalle shi hawaye na sintiri akan fuskarsa. Ya jani jikinsa ya rungume yana fad'in "Dan Allah ki yafe mini, ki fahimce ni, ki mini uzziri, ki tsananta yi mini addu'a ".
Muka dinga kuka babu mai rarrashin wani. Dukkan jarumtar Tijjani ta k'are gabad'aya. Na kuma gasgata ba a haiyacinsa yake yi mini wani wulakancin ba. A haka yaran suka dawo suka tarar da mu.
Hamim ya zuba mana ido. A hankali Tijjani ya sake ni tare da dabarar dauke hawayen sa. Yayin da nawa ya kasa tsayuwa.
Hanif ya ce "Ammi Baban 2 yau ma ba shi da lafiyar ne, ya sake yi miki wani abu ne?"
Kafin mu amsa masa Hamim ya ce "Lafiyarsa k'alau fa. Ammi ce take ce mana ba shi da lafiya, marar lafiya yana yin fad'a ne?"

✍️
*Y'ar uwa, ya mukaji da bubukuwa?* *Daga nan fa har january kusan ko wanne sati akwai biki, in ba na kusa ba akwai na nesa, ban da tunanin gudunmuwa da ma kudin man da zakaje bikin ga tunanin abunda zaka saka.*
*Balle ace maaikaciya ce ko CEO ce kina business din ki, kinsan all eyes on you🧐, ke ba sayen atamfa ba komi tsadanta anyo copynta, shima lace haka, cabdi! To albishirinki yar uwa!*
*UMM NIHLA malaysianfabrics ta dauke miki damuwa, tana da fabrics kala kala masu sauki da inganci kuma babu inda zaki samesu in ba wurinta ba, kije taro ki haska kowa sai ya tambaye ki me kika saka ina kika samu💃 maza garzaya gurinta kusa labule.* https://wa.me/message/F3EWRSHQPQAAH1

*Oriflame products*
*Daga make up artist din Guduyo*
*Idan kina bukatar Oriflame products ko wanne irin ne, ko Kuma kina sha'awar yin register da su*. *Ki tuntubemi babbar dealer din su Aisha lame*
*Ina kuma fad'a muku akwai da daddan ganyen shayi na Lame Tea*
*Akwai pop corn*
*07036662633*.
Chapter 121 · 0% Book details