Sashe 34
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
albarkar iyaye, sannan su kansu matan naka ba gode wa kokarinka zasu yi ba, kullum zaka zauna ne cikin zullumin zarge zargensu." Yana dasa aya Yaya J ya ce "Zan jure Baba, zan iya, da sannu Ubangiji zai hore mini su gaba'daya. Sannan ina fatan sanadin wannan auren ya zama silar daidaita al'amura a gidan nan". Ga mamakina sai jin muryar Baban Marina na yi cikin kaushi ya ce "Jabiru ba zan baka ba, na rok'e ka, kar ka kuma dosa ta da wannan tatsuniyar domin ko mak'oshina bata je ba, bare ta shiga zuciyata. Bana son na yi maka abin da zaka mini kallon marar kirki, ko na rashin inganta zumunci, amma idan ka cigaba da dagewa to ba shakka zaka sha mamaki, domin kuwa na riga na haramta soyayyarku a zuciyata, dan haka kai ma ka shafe ta domin ba rayayya bace". Bamu gama fita da mamakin maganganun Baba ba, Yaya J ya sake shayar da mu wani sabon mamakin ta hanyar cewa "To Baba idan kuma Allah bai shafe ta ba, ya raya ta fa?" Takaicinsa ya k'ume Baba ya kasa ce masa komai domin bai ta'ba zaton Yaya J zai iya fada masa hakan ba tunda mutum ne mai biyayya, mai kuma gudun zuciya. A sanyaye ya ce "Kowa ya ki fahimtar halin da nake ciki, me yasa zaka biyesu wajen yin watsi da zumunci Baba? Annabi cewa ya yi mu yiwa wanda basu yi mana ba". A matu'kar zafafe Baban Marina ya ce "To dai ni ne uban Yabi! Ni kuma shari'a ta girmama ta mayar a hakku ya za'ba mata miji, idan kuwa hakane, ko mutuwa ce ta riske ni gabannin na aurar da ita da kaina. To waliyyinta baza su baka ita ba, bare kuma ina fatan a ara mini dama na aurar da ita da kaina. Ka je ka yiwa Mahaifinka biyayya, na gode sosai da soyayyarka. Mu cigaba da addu'a da sannu komai zai dai-daita mana. Amma Yabi kam ba matarka ba ce". Tsawon lokaci bai amsa ba. Ni dai daga sama na ji muryarsa yana cewa "Sai da safe Baba". Ajiyar zuciya mai nauyi na ji Gwaggo ta yi tare da cewa "Alhamdulillah! Ubangiji ka sake nisanta wannan al'amarin kamar yadda ka nisanta gabas da yamma." Na kasa magana, amma dai zuciyata ta yi nauyi, na kuma gamsu da gaske Yaya J yana sona da dukkan zuciyarsa. Gefe guda kuma ina gasgata tsinkayen Nazira da ta ce Baban Marina ma ba zai bashi aurena ba. Na k'udire bazan sake bari mu hadu ba, bare zuciyata ta dinga karaya a dalilin ta so mini da soyayyarsa da nake ta kokarin danne wa da dukkan iya wa ta. Washagari na tashi sukuku ba wanda ya tayar da maganar. Da yamma sai ga kwamshina ya zo, sai da ya fara zuwa wajen Baban Marina a wajen sana'arsa, ya sanar masa nan da kwanaki biyar zai zuro a yi maganar aure da saka rana gaba'daya. Shi yake fa'da mini hakan. A wannan ranar ma kayan da ya kawo mini ba k'aramin yawa ne da su ba. Tunda ga kan sutura, ga provisions tamkar wacce nake rike da kaina. Sai kuma dalleliyar waya da zoben gold wai a matsayin tukuicin amincewa da shi. Tuni Baba ya sallama ya bar ni ina rike waya. Wadanccan ma da ya rike tuni ya fito mini da abina. Dama k'ananu ne sai kawai na ce ya bawa iyayenmu mata tunda uku ne dama. Ni bansan me yake faruwa ba, ashe Yaya J bai fasa sintiri a wajen Mahaifinsa da Dada ba. Da ya kasa samun tallafinsu, sai kawai ya doshi Baban kasuwa mahaifin Maijidda. Nan ma fatattakarsa ya yi tare da alwashin idan mummunar k'addara ta afko aurenmu ya tabbata, to kuwa ya kwana da sanin sai dai ya sako masa Maijidda. Hankali ya fara tashi domin gaba'daya Yaya J ya susuce ya rasa nutsuwa har ta kai Maijidda ta dawo gida a dalilin zaman nasu babu da'di sam, ita kuma ta gaza ha'diye damuwa ta taho, da k'yar Dada ta mayar da ita. Baban Marina da kansa ya fa'da wa Dada da yan'uwansa cewar ranar asabar za'a zo neman auren Yabi, kada su yi nisa. Daga Baban Tsakiya har na Kasuwa suka gabatar da uzzirin suna da daurin aure muhimmi a wannan ranar. A wannan karon hankalin Baban Marina ba k'aramin tashi ya yi da wula'kancin da suke yi masa ba. Ya gabatar da korafinsa gaban Dada cikin kankan da kai ya ce "Ba zai yiwu na dauko wasu daga waje su marabci masu neman auren y'ata ba. Alhalin ga y'anuwana ban da ransu da lafiyarsu, har wanne daurin aure zasu je da yafi al'amarina muhimmanci Dada? Ki shiga cikin wannan maganar, ina jin tsoron kada na kasa jurewa fa." Ita da kanta ta sani ba'a kyautata masa ko ka'dan amma da yake bata iya tsawatar wa wadanccan shiyasa bata iya magana, har komai ya rincab'e. Da rashin walwala ta ce "Zamu zauna da daddare dukkanmu". Da daddare kuwa dukkansu uku suka hadu a gaban mahaifiyarsu, a sanyaye take gabatar da k'orafin da yayansu ya zo da shi. Babu kunya dukkansu suka ce suna kan matsayarsu ba yadda za'a yi suna cikin hankalinsu su jagoranci bawa mai saka d'agaggen wando aure, kema da za'a fito k'arara a fa'da miki ainihin yadda ak'idarsa take da kin k'yamace lamarin wannan mutumin. Mun yi shiru ne kawai dan kada ace hassada muke yi. Ko bamu da kirki, amma waye a jahar nan bai san yadda Mustapha Zaki ya yi k'aurin suna wajen yiwa masu akidar yin maulidi kafar ungulu ba. Duk wani masallaci indai ba na yan kungiyarsa bane sai ya durkushe shi, ke kan ki da yasan yadda kike son shehu da ya d'aure ki saboda zuciyarsa babu alheri." Dada ta kad'u kwarai da gaske. Domin babban b'acin ranta a nemi ta'ba mata mutuncin ra'ayinta. Ita din mai mai zazzafar akida ce akan hakan. Ta fara tafa hannu tana cewa "Ashe hakane? Allah na gode maka da ka kubutar da jinina fa'da wa hannun wanda zai yi mata sanadin rashin samun rabo ranar gobe". Sai ta hau kuka tana sake godiya ga Allah da Annabi. Jikin Baban Marina ya yi matu'kar yin sanyi ta yadda yan'uwansa suka shammace shi, suka gabatar da hujjar da ba mai kankareta a zuciyar Mahaifiyarsu. Ya tabbatar sun dade da kitsa maganar dan sun tabbatar auren ya rushe gaba'daya, kuma wannan hanya ita ce mafi sau'ki da zasu ja hankali gyatumarsu ta lalata komai. A zuciyarsa ya dinga ayyana shin wanne irin zamani muke ciki wanda dan-uwanka ma baya son ya ganka a inuwa? Me ya tare musu ne? Shi ka'dai ne yake fuskantar irin wannan tsananin ko kuwa a ko wacce zuria ce? "Allah kai ne mai zamani, a kawo mana mafita, da sassauci" ya fa'da a ransa. Ya sake kallonsu, yana ganin sun hade sun bar shi daban, sai dai a zahiri ne suke shiri a bad'ini kuwa ba wani taimakon juna a tsakaninsu, tunda kowa iya y'ay'an da ya haifa ne dolensa. Sannan kowannensu boye wa dan-uwansa wadatarsa yake yi. Ya sauke gauron numfashi kafin ya yi magana ya ji Dada tana fa'din "matu'kar ina da iko akan ka ba za'a bashi aure ba, idan kuwa ka kafe sai dai na barka da Ubangijin gizagizai ya bi mini kadina a wajenka". A ki'dime ya ce "Har abada maganar ta mutu, Allah ya yanke mata wahala ya fito mata da wani mafi alheri wanda za'a yi alfahari da shi". Dada ta goge idonta tana fa'din "Ameen". Baban Tsakiya kuwa ya ce "ai y'ar fariya ce , ba zata tsaya a matsayinta ba, dama ya ta kasance? bare yanzu da wannan tsohon banzan ya sake kambaba burinta. Ai idan ba tashi aka yi akan ta ba, sai ta tsofe tana gabanmu tana zuba d'ibar albarka, ko yanzu tana ganin sakamakon hatsabibanci, tunda duk kintsatsse ba zai zo wajenta ba. Har yau ta k'i barin Jabir ya fuskanci matarsa sosai, da sun fara zama lafiya idan har ya yi tozali da Yabi zai gigice. Gashi kuma Maijidda matarsa ce, tunda cikine da ita, idan ba'a bashi aurenta da ake ta munafurci ba, ta ya ya ake so wannan rabon ya bayyana?" Baban kasuwa ya ce " Ai ha'kuri Muna cikinsa, amma sai ace mune da laifi, ban da sha'anin jini tasirinsa yawa ne da shi ai wata shari'a sai a lahira kawai." Dada ta ce "To ni kam ba zaku bar gun nan ba sai an samo wanda za'a ba shi auren Yabi. Domin na fuskanci matsalar gidan nan tana 'damfare da ita." Baban Tsakiya ya sake cafe wa da cewa "Kinsan dai ni da Iliya bamu da mutuncin da zamu yi irin wannan ikon da ita, wannan maganarki ce da ubanta." Cikin rawar murya irin ta sare wa da lamari Baban Marina ya ce "Yau muna watan Safar ko Dada? To matu'kar rayuwata ta kai, watan jibi na gaban maulidi ke nan, zan aurar da ita. Domin ina da wadanda zan basu aurenta su kar'ba, sannan ita ma Ubangiji ya hore mini ita zata ta yi mini biyayya. Ubangiji kuma zai duba manufar kowa a nan ya cusa wa wanda zan ba shi auren ya kar'ba da dukkan zuciyarsa". Dada ta ce "Allah ya tabbatar ya nuna mana lokacin, amma ba za'a tashi ba sai ka fadi wanene, d'an wacce haular ce? Gudun kada a sake kitso da kwarkwata." Baban Tsakiya ya ce "yarinyar nan fa ta riga ta rik'a, idan aka kai ta wani wajen ma mutuncin gidanmu zata zubar, me zai hana a lallaba a bawa wannan yaron kawai, tunda shima yana da tambarin da aure zai yi masa wuyar samu wa?" Baban Kasuwa ya ce "Ni ma tuntuni nake son na fa'di hakan, to amma ina jin tsoron sharrin zuciyar da take raina alheri, yanzun nan sai a juya magana a ce da mugun nufi aka yi kaza". Dada ta ce"Ku yi magana sosai mana, ni duk kun saka ni a duhu ban gane wa kuke nufi ba?"