Sashe 5
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*3&4* K'aramar hukumar Toro tana cikin k'ananun hukumomin jahar Bauchi. Duk wani mai nazari yasan yadda Ubangiji ya wadata Toro da girman k'asa. Ita ce k'aramar hukuma mafi girma a dukkan fa'din tarayyar Nigeria dama Africa ta yamma gaba'daya. Garin Toro an kasa shi zuwa Gundumomi uku. Gundumar Toro, gundumar Jama'a da gundumar Lame. Sannan akwai kabilu daban daban bayan Hausawa da Fulani. A karkashin jahar Bauchi ta ke amma tafi makwbataka da jihar Filato. Shi yasa garin kewaye yake da ni'imomin kayan itatuwa da rashin zafin rana sosai. Ba dan ina y'ar garin ba, Ubangiji ya dabaibaye garin Toro da tarin faloli Alhamdulillah. Dare ne amma ba ainun ba, mafi yawa mun ha'du a kofar Kakarmu Dada ana ta hira da tatsuniya. Kannenmu kuma sai wasan d'an dunmi suke yi. Dukkanmu y'anmata mu bakwai da muke kai d'aya muna zaune akan tabarma, idan aka dauke shalele Nasiba da take kishingi'de a jikin Dada. Sannu a hankali Dada take taunar goron bakinta tana mulmulawa. Kyakkawar dattijuwa mai kyakkawan jiki. Asalin Bafulatanar Lame ce, kowa kuma yasan asalin mutanan wannan garin fulanin Mali ne da kiwo ya saka suka tsallako Nigeria suka yi sansani a yankin na Lame. Wani ikon Allah mafi yawa na ahalinta sun samu kyawun halittar fulanin Lame. Haka muke y'an gidanmu son kowa k'in wanda ya rasa. Wani irin kallo take mana na kurillah. Ta kasa ha'kuri ta ce "Na fa'da muku dukkanku ku zauna cikin shirin ko ta kwana. Domin kuwa ba zaku fi haka gandare wa a gabanmu ba. Dukkanku abubuwa sun cika muku k'irji. Ko wacce a cikin ku wanki take yi a gabanmu, ina kallon zamani ni Binta! Muna cikin alhini. Allah yasa intingifarin da muke nacin yi mun samu rabauta ana karban sallarmu". Dariya ta kama mafi yawanmu. Ni da nake da kaud'i na ce "Dada Ashe ba'a karban sallarku ne?" Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Ai matu'kar kana da yarinyar da ka yi saken da ta fa'di a gabanka, to kuwa babu makawa sallarka bata isa gaban zati, daga bakin k'ofa ake dakatar da ita!" Nasiba ta ce "Allah ya kawo mafita. Yanzu biya mana karatun na yau". Nan da nan ta furzar da goron bakinta dan girmama karatun da zata d'ora mana. Ta tsume ta ce "Mu karanto na jiya". Muka ha'da baki wurin rera karatu cikin sigar wake muka ce "Idan attishawa ta sauko mana, idan wani bawa a kusa da mu ya ce mana "Rai ya hadu da Gafarar Allah!" Sai mai attishawa ya ce "Ya-hadi kumalle. Idan kuwa zamu ci adda'ami. Zamu fara da ambaton Allah. Idan koshi ya zo mana sai mu ce "Sawaba ta sauka akan me nemo wa da mai dafa wa". Dada ta murmusa tabbacin ta gamsu mun ri'ke karatun nata da kyau. Ta ce "Madallah!". Cikin alfaharin muna da fikirar fahimtar karatun da take yi mana. Ta muskuta ta ce "yau karatun yiwa kai rigakafi daga shaidanu da makarai zan dora muku". Muka ha'da baki wajen fa'din "Mun gode Dadarmu, Allah ya kara miki nasibi. Annabi yasan da ke". Ta numfasa ta ce "Ameen, a kuma tsananta yi mini rokon dacewa da shiga cikin masoyan SHEHU". Na kasa jure wa na ce "Ashe Dada ba zaki bar zancen Shehu ba? Kowa ya bar Allah da ma'aiki ai ya bar hanyar tsira." Nan da Nan ta fusata ta ce "kaico da Yabi! Yabi ba zaki tsira ba, waya yake inkari da jikan Manzo? Tabbas sai gafalalle". Na ci je na sake ce wa, Annabi dai aka ce mu ri'ke ba waninsa ba Dada, iyalan gidansa suna da girma da hakkin mu so su mu kare mutuncinsu. Amma ba'a ce a kai su wani bigire da zai iya zama halaka ba. Da kansa ya ce "Zan bar muku kura'ani da sunnata wato (Hadisansa) idan kuka bisu kun tsira. Amma ku kun shure komai, kun dauko shehu kuna neman mayar da shi abin bauta?". Ai kuwa ta sake harzuka ta ce "Wahalar rayuwa akan ki Yabi! Mai gadon taurin rai da kafiya, kaicon ki, kaicon ki! Da yi mini izgilanci Asiya". Jikina ya sabe da rawa a dalilin ba irin jan kunnena da Gwaggo bata yi mini ba, akan kada na sake na janyo abin da Dada zata dinga yi mini mugun fata. Ga shi ban ji ba, na yi sanadin da take fatan na dauwama cikin wahalar rayuwa. Kafin na ce komai sai ga Tijjani wanda mafi yawa an fi k'iransa da sunan garinsu Bulkachuwa. Wani irin zabgegen saurayi. Dogon gaske har d'an rankwafa wa ya yi ka'dan. Fari ne tas, irin fulanin Bulkachuwa, a murde yake, shi ba siriri ba, kuma ko ka'dan baya cikin masu kiba. Ga dogon hanci da ya k'awata doguwar fuskarsa. Baya ga hakan manyan idanuwansa ka'dai sun isa abin burge wa. Ban ta'ba ganin namiji mai jajayen lebe ba sai Tijjani kyakkawan gaske. Wani irin mutum mai saurin fishi, da k'arfin zuciya. Amma mai saurin saukowa da mantuwa. Illarsa d'aya manemin mata ne, a yadda a ke fa'da. Na shaida kuma duk wata budurwa ballagaza a Toro to kuwa budurwarsa ce ko kuma suna d'asa wa, shiyasa kowa yake jan kunnen y'arsa a kansa, barin ma ni, kullum ne sai Gwaggo ta ce kada na sake na bashi fuskar da zamu dinga doguwar magana. Gaba'daya dabi'unsa na tantiran yan-iska ne, sannan k'azami ne, baya damuwa da yin wanki sai kayansa sun k'are. A hakan kuma shashan y'anmata suke sonsa, ko da yake baya yarda ya fita da dattin sosai, yana wanke wa ya jira su bushe, guga ce sai ya samu ku'di, sai ya bayar da kayan ma a wanko a gogo masa, amma da wahalar gaske ya yi guga da kansa. Duk yadda Dada take kulafacinsa, matu'kar ya shigo muna nan sai sun haura da shi, domin yafi kowa takalarmu da magana, yana yi yana lumshe ido ta yadda zai sure zuciyoyinmu. A hakan ya yi nasarar yin wuf da zuciyar Nasiba. Idan Dada ta ga yana sakin maganganu ko lumshe ido a gabanmu ta dinga bagarar da shi, ko ta tsiri aiken sa, ko kuma ta ce mu je ta sallame mu, duk yadda take sonsa to bata son doguwar magana a tsakaninmu, kazalika kuma bata son a k'i gaishe shi. Burgar da yake yiwa mata ya sanya har yanzu bai bar dauke dauke ba, komai ya gani zai dauka ya siyar ya kashe wa budurwa ku'di. Amma iya kayan Dada yake dauka. A duk sadda take yi masa fa'da kuma zai waske ya ce bashi ba ne, ko kuma sharri ta yi masa, haka kuma sai ya d'auke mata wuta, har sai ta nemo shi ta bashi ha'kuri. Bayan soyayyar da take yi masa, yana sake samun alfarma a wajenta saboda sunan SHEHU ne da shi. Kullum bakin ta akan ya nutsu ne, ya bar shiririta ya kawo matar aure, tunda ga Yaya Salisu nan da yake sa'an sa tuni ya yi aurensa har matar ta haihu, amma shi ko maganar aure baya yi saboda sharholiya da mutuwar zuciya. Duk da k'arancin shekaruna ina tambayar kaina ko waye zai iya d'aukar y'arsa ya bawa Bulkachuwa aurenta? Tabbas sai idan yarinyar ta kasance shasha ce irinsa. Na tabbatar mahaifiyar Nasiba ba zata ta'ba bari a bashi ita ba, domin kuwa kowa nasa yake so, bare idan maganar gaskiya za'a yi bai cancanci a bashi ba, domin bashi da sana'a, gashi manemin mata, shiyasa kowa yake masa kallon shasha. A duk sadda Dada take yi masa fa'dan shigar da yake yi ta gajerun wanduna yana yawo a gari babu kunya, ko tara suma ya gegareta daga gefe, ko kuma wani zubin ya sauya launinta bayan ya mayar da ita cibiri cibiri. "Akan kunnena na sha jin tana ce wa "Saboda bamu da mutunci a idonka shiyasa kake iya zuwa gabana a hakan ko kuma gaban kawunanka". Ba jin nauyi yake ce wa "Tunda nake yin sallah a hakan, ai kin ga bai zama aibu dan kun gan ni a hakan ba. Domin Ubangijina ma a hakan yake gani na, kin takura mini fa Tsohuwa" Nan da nan ta zabura ta ce "Imaninika ai a makogaro yake shi yasa kake hakan, amma da za'a jarrabe ka da son wata yarinyar ba zaka yarda ka je mata a hakan ba. Alfarmar Shehu sai ka samu wacce sonta zai hanaka yin wannan shakiyancin. Tunda ka ki daina wa saboda Allah da Ma'aikinsa." Dariyar iyashege yake yi ya ce "Ni da nake da y'anmata kamar jamfa a Jos suna bina dan na so su, shine har son wata zai canja ni? Lah! Ba dai Bulkachuwa ba". Da wani kuma a Cikinmu ko a cikin samarin gidan matu'kar ba Yaya Anwar ba ne zai saka musu baki, a take Dada zata nuna wa mutum shine bare a tsakaninsu. Tana kuma sake kambaba shi da kawar masa da kai saboda alfarmar mai sunansa ne, domin ko ta yi masa sababi, sai ta yi ta tuba tana kamun kafa da mai asalin sunan akan a saka mata jikanta cikin shirayayyu. Hatta shi kansa dariya take bashi akan yadda take tuba idan ta saki harshe a kansa. Amma wani ikon Allah jarumi ne na gaske. Idan na ce jarumi ina nufin zai tsaya ya fafata da kowa akan hakkinsa, matu'kar kuma ya sanya kansa zai yi abu, to duk tsananin wahalar abin sai ya ga abin da ya turewa buzu nad'i. Baya ga hakan kuma tausayi ne da shi, duk zafinsa inda zai ga kana kuka to zaka ga ya bar yi maka tijara. Sai dai kallon marowa ci nake yi masa na gaske, ni dai ban ta'ba ganin ya yi kyauta ba. Ko garinsu ya je ya dawo, duk abin da zai samo ba dai ya kawo gidanmu ba. Amma kullum a cikin karbe wa jama'a nasu yake, mussaman Dada da ko ta hana shi a k'arshe take kasa juriyar ganinsa cikin rashin sukuni, sai kawai ta bashi. Mazan gidan kuwa basa bashi duk irin yadda zai karyar da kai yana fa'din bashi da lafiya, tunda suka gane matu'kar ku'di ya shiga hannunsa y'anmata banza yake kashe wa, sai kowa ya kulle bakin aljihunsa dama kuma masu k'aramar niyya ne. Sai dai gara shi ma suna bashi, amma da a ce