← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 146

Sashe 125

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✍️
*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA.*
*SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA*.

*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES*

*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTU MASU MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.

*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.
*08032773332*.

Na farfado ne na gan ni ana k'ara mini ruwa sai fifita suke mini tare da kuka dukkansu.
Baki na rawa na ce "Babah ni din musulma ce! Ki fad'a mini Tijjani ya rasu ne?"
Da rawar murya ta ce "Bai ce ya mutu ba Yabi. Amma dai akwai abin da ya same shi marar dad'in ji, tunda har Aliyu ya jinjina lamarin".
Na fizge k'arin ruwan na zabura na ture su na tashi. Hijabi na raruma na yi hanyar waje ba tare ma da na saka ba.
Yaya Ummi ta ruk'o ni tana fad'in "Ina zaki a wannan halin Yabi?"
Da kuka sosai na ce "Kano ba zan tab'a samun nutsuwa ba, matukar ban san halin da yake ciki ba".
Fuskar kowa k'walla ce da tashin hankali. Hatta Mama jikinta a sanyaye yake ainun.
Da k'yar suka tirsasa ni na hak'ura na zauna. Sai ambaton Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai nake yi. A fili nake fad'in Allah ka kaddara mini na ga dawowar Tijjani cikin gidan nan, ko da ba akan kafafunsa ba ne. Fatana ace yana numfashi. Ubangiji ka rufa mini asiri ni da y'aya'na".
Ba abin da yake sake tayar mini da hankali irin yadda Babah ta kasa tsayar da hawayen ta.
Akai akai take share hawaye babu kakkautawa.
Kwanaki biyu muna cikin wani irin zullimi mai tsananin gaske. Domin duk asibiti da yake cikin Kano su Aliyu sun karade a kwanakin nan amma babu Tijjani babu labarin sa. Kowa ya karaya. A ranar Baban Marina ya taho Bauchi tare da Gwaggo. Nasiha kan nasiha suka shafe lokaci suna yi mini akan yarda da kaddara na yi hak'uri mu bishi da addu'ar idan a raye yake Ubangiji ya tsare mana shi, ya kuma bayyana shi. Idan kuwa rai ya yi halinsa to Allah ya sanar da mu, ya kuma jik'an sa.
Na rarrafa na fad'a jikin Baba cikin matsanancin kuka na ce "Sai yaushe zan huta, yaushe ne zan ji dad'in da ake ta fad'in zai same ni? Gabad'aya walagigi yafi yaws a rayuwata Baba! Kalli k'ananun y'aya'n Tijjani wa zai taya ni tarbiyarsu da wahalarsu Baba?"
Muryarsa na rawa ya ce "Ubangiji da ya baki su shine jagoran da zai taya ki kulawa da su. Sannan matukar ina numfashi ko y'aya' nawa kika haifa zan kula da su iyakar yadda zan iya, tamkar y'aya'n da na haifa!
Yadda ya kare maganar da kuka ya sanya Gwaggo fara kuka duk kuwa da yadda take da jarumta mai yawa. Kowa na falo kuka yake, hatta Mama kuka kuma na gaske ba na ganin ido ba.
Tsawon lokaci muna kuka tamkar an tabbatar Tijjani ya k'are.
Hanif ya ce "Ku yi hak'uri" Hamim kuwa ya ce "Baban 2 zai dawo a motarsa bai b'ata ba."
Gabadaya yaran sun rasa kuzari da karsashi a tare da su.
Da yamma mun idar da sallar la'asar Yaya Salisu ya kira Baban Marina da yake zaune a cikinmu tamkar mace.
A sanyaye ya ce "Mun samu labarinsa, mun je mun gan shi".
Gabadaya dakin muka hau fad'in Alhamdulillah Alhamdulillah!
Sai dai Innalillahi wa inna ilaihir rajiun din da Baban Marina yake fad'i ya yi matukar tsorata mu, mussaman ni da zuciyata tamkar ta fad'o k'asa.
Na kasa fahimtar bayanin da ake masa. Nasan dai na ji ya ce mun gan shi.
Gumi ya dinga keto mini. Ina tambayar zuciyata wanne ibtilai ne ya samu Bulkachuwa irin haka?.
Sai da Baban ya ajiye wayar. Tsawon mintina bai iya ce wa komai ba. Gabadaya ya jike da zufa.
A sanyaye Gwaggo ta ce "Alhaji fad'a mana halin da ake ciki kada zullimi ya karasa kassara mu.
Murya babu amo ya ce "Yana hannun jami'an tsaro. Tun shekaranjiya suke tsare da shi. Kuma damln tsabar raina talakan k'asa suka kashe wayarsa bare wani nasa ya ji halin da yake ciki."
Na saki nannuyar ajiyar zuciya, da kuka nake fad'in Allamdulillah!
Domin sai na ji tamkar an dauke mini k'atuwar masifar da ta nannad'e ni.
Tunda yana da ransa komai mai s'auki ne. Domin ban fahimci ana iya yiwa mutum talala ya zama ba shi da yancin yin komai a rayuwarsa ba.
Na kasa yin walwala a dalilin yadda Baban Marina ya yi laushi. Na tabbatar Tijjani na cikin k'ak'ani ka yi.
*Toro*
Baban kasuwa da Baban Tsakiya zaune a gaban Dada da take kuka face face tana fad'in "Ubangiji ka kare mai sunan manya, ka bayyana shi".
Baban Tsakiya ya ce "Ki daina damuwa sai ciwon ya tashi ne? An ce miki a gan shi. Sai dai fitowarsa sai ikon Allah. Tunda laifin da aka kama shi da shi idan a wata k'asar ne take za'a tabbatar masa da haddin kisa."
Hannun biyu ta d'ora aka tana kururuwa tana ce wa "Allah ka yi mini dan ma'aiki. Alfarmar Shehu Amadu Tijjani mai karama ka saukakawa wannan yaro".
Baban kasuwa ya ce "Allah ne ya yi sakayya ya toni asirinsa. Wai Tijjani ya rasa wadanda zai wulakanta sai mu? A fili yake nuna wa Yaya Sani ne kawunsa da zai yiwa hidima. Akan idonmu zai ta d'orawa yara kayan abinci da kayan miya ana kai wa kofarsa amma mu wayam. Wai shi mai suruki. Alhalin ba akan son ramasa ya bashi auren iblishiyar yarinyar nan ba. Mune muka so a bashi"..
Baban Tsakiya ya yi k'uta tare da ce wa "Allah ke nan! Ai duk mai gilli mai son ya wulakanta na gaba da shi ya dinga ganin jarraba ke nan."
Dada dai kuka take bil hakki. Domin tun farko tana son Bulkachuwa. Da ya samu wadata kuma ya jiyar da ita dad'i duk da dai ce wa take yi bashi yake biyan ta. Tunda dukiyarta da ya salwantar mata runduna ce babba.

Washagari muka dunguma Kano tare da Baban Marina. A babbar hedikwatar y'an sanda ta bonfai muka tarar da shi cikin mawuyacin hali. Hawaye ya tsinke mini. Domin gabad'aya ya fita a hayyacinsa. Babu alamun duka a tare da shi. Amma ya jigata k'warai da gaske. Abin mamaki a wajen muka tarar da su Yaya Jabir ya zo daga Kaduna da kuma Yaya Ammar yayan Nasiba. Duk da shi ma a BAUCHI yake aiki a gidan Yari. Tunda su Yaya Salisu suka fada musu, suka bar komai suka biyo su Kano dan sanin halin da Tijjani yake ciki.
Cikin tashin hankali Tijjani ya ke fad'in "Wallahi bana harkar. Ina gida aka mini waya akan na biya na karbi sako a Wunti. Ashe wiwi da koken ce ga shi an kasa samun lambar da aka kira ni da ita. Wallahi ba kayana ba ne, ba ni da alak'a da ita".
Ya fad'a idonsa ya kad'a ainun tamkar na rikakken mashayi.
Na rushe da kuka riris. Domin dai na riga na gane mun fad'a cikin garari mai girma. Kallon sa na yi na gane iyakar gaskiyarsa yake fad'a babu alamun karya ko kwaskwarima domin ya riga ya bani damar da na fahimci gaskiyar sa da kunbiya kunbiyarsa.
Babah ta kasa magana, yayin da Baban Marina ya ce "Tijjani ka fadamana gaskiyar magana, dan musan ta yadda zamu b'ullowa wannan azal d'in. Kasan wahalar da shari'a ma laifi ne babba."
Murya na rawa ya ce "Wallahi gaskiyar magana na fad'a. Bana harkar, ba ni da alak'a da kayan da aka kama ni da shi Baba".
Gauron numfashi Baba ya yi tare da ambaton "Subhanallah!
Baba ta kasa magana duk da idonta a soye yake babu alamun kuka. Na sani kuma tana cikin damuwa ne mai yawa.
Na tsugunna a gabansa ya sassauta murya ya ce "Asiya na rantse miki ba ni da alak'a da wannan al'amarin sharrin magauta na had'u da shi. Kaddarar da azal ce ta hau kaina".
Na zuba masa ido tamkar ba a gaban iyayenmu muke ba. Shi ma ya zuba mini nasa, tsawon lokaci muna kallon juna. A cikin wannan kallon na tabbatar Tijjani bai aikata laifin da aka jingina masa ba. Na kuma gasgata shi akan gaskiya yake amayarwa.
Ni na fara janye idanuwana da hawaye suka cika su taf. Da rawar murya na ce "Na gasgata ka Baban 2! Ina baka tabbas din ko baka samu mutum daya da ya gasgata ka ba. Ni Yabi na yarda bak'in k'azafi aka yi maka, tare da hak'a maka ramin mugunta. Dan haka ina tare da kai cikin ko wanne bigire har mu ga me Ubangiji zai zartar mana".
Daga hakan na fara kuka sosai. Yaranmu da suke jikinsa suka yi tsuru tsuru suna kallon yadda nake kuka sosai, shi kuma ya susuce ido ya kad'a.
Sai lokacin Babah ta ce "Allah ya warware maka, ya bayyana gaskiyar al'amarin".
Yaya Ummi kuwa da Mama kuka suke yi. Gwaggo ce bata um bata um tunda ta yi jaje cikin rauni da kasala bata sake iya magana ba.
Muna kallo da lokacin da suka bamu ya cika suka iza keyarsa hannunsa dauke da ankwa tamkar kasurgumin mai laifi.
Ni dai har muka dawo BAUCHI ban iya daina kuka ba.
Tun ana bani bakin na yi shiru har aka zuba mini ido.
Maimakon mu yada zango a BAUCHI sai Baba ya ce a wuce Toro kawai.
A k'ofar gida muka tarar da su Baban Tsakiya. Na kalle su na gasgata ce wa Baban Marina ne kawai ubanmu. Ba wanda ya bi bayan Tijjani ko na ahalinsa a cikinsu.
Dukkanmu a gaban Dada muka zube tamkar masu neman gafara. Tana kuka, matan cikinmu muna yi, tamkar dai mutuwar fuju'a Tijjani ya yi.

*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA.
*SABO LITTAFIN TA ZAI ZO BA DA JIMAWA BA*
Chapter 125 · 0% Book details