Sashe 145
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kwa aki uku kacal aka ba shi ya huta.
Gidan Marina ya kacame da murna kowa ya boye aibu da gilli aka dinga tseren yi mana murna. Baban Tsakiya da na Kasuwa washagari suka zo sai dai tafiyar kowa daban.
Dukansu maganganunsu suna nuni.tare da tuni sune suka had'a auremmu dan mu gane oron alherin da suka yi mana. Baban Tsakiya cikin rauni ya ce "Tijjani danuwanka dai yana zaune babu aiki. Jabiru naka. A duba, ga yaranmu nan ka yiwa Allah ka dubasu. Ka rage banbanci Tijjani. Allah ya shirya zuria."
Da zai tafi ya bude murya ya ce "Ina Hajiya Yabin?"
Gabana ya Fadi ni ce Hajiya Kuma?"
Na saka hijabi na fito na tsugunna na ce ga ni Baba".
Ya ce "To ku kula. Ki kuma dage da yiwa mijiki addu'a kinga dai fad'i tashin da muka yi har asirin da aka ta jifanku ya karye. Kada na ji, kada na ga ni. Ki dinga tunawa mijinki game da rashin aikin yayanki Jabiru. Ki kuma cigaba da hak'urin aure nasara tana gaba. Alhaji Babba mura yake shiyasa bamu taho tare ba".
Da mamaki na ce"wanene ke nan?"
Ya ce "Baban Marina mana"
A sanyaye na ce "Ai to, Allah ya bashi lafiya."
Ya ce "Ameen."
Yafi away da tafiya minda Tijjani bamu iya cewa komai ba. Domin ni tunanin fad'i tashin d Aya ambata sun yi nake yi. A hakan Baban Kasuwa ya iso shima ya gama kamun kafarsa da borin kunyarsa. Abin da yake bani mamaki yadda suka fi karkata akan ni naga farinsu fiye da Tijjani ya ga ni. Na fahimci sun riga sun yi nisa a wajen imani da ce wa sai ina son mutum da Tijjani ya taimake shi.
A wannan loakcin mun barji soyayya. Kusan salon gwamna Tijjani ya dauka na wajen ririta ni da mutunta lamarina.
Tuni ya canja wa twins makaranta ya kai su wacce ta amsa sunanta. Aikina kuwa bai hana ni ba. Haka nan na kan yi kunshi amma ba irin na da ba. Domin a yanzu mai kololuwar daraja nake yi. First lady da mukarrabanta kad'ai sai ko Hajiyar da ta yi mini sanadin zuwana gidan gwamnati.
Watanni uku kafin Tijjani ya gane kan ma'aikatar. Cikin sa'a ya samarwa Yaya J da Yaya Rabiu aiki. Ya daga darajar aikin Yaya Salisu. Hatta Yaya Musa da ya zama shasha ya samo masa aikin security a babban asibitin Bauchi. Ya biyawa Anas da k'aninsa Nasiru karatu suka tafi Sweden karatu. Anas digiri zai yi, Nasiru kuwa PhD.
Ba jimawa azumi ya zo, ya tisa ni a gaba da yara muka tafi Umrah da kuma Babah da abokiyar zamanta hadi da Aliyu da matarsa.
Fad'in irin jin dad'in da muka yi ma bata lokaci ne.
Babah Maryo ce ta kasa zuwa inda muke har yau. Hatta Nasiba ta zo yi mana murna. Ta Kuma ro'ke shi ya sama mata aiki duk da a Jos take. Ya mata alkawri zai saka a bata rubuta kati a asibiti.
Domin mijin nata babu. Na kuma san Tijjani zai yi mata wannan kokarin. Domin ma riga da na fahimci shi mutum ne mai saurin afuwa da sassauci. A yanzu haka ya yi amfani da kujerarsa ya fito da Alhji Auta. Ya gyara masa gidansa. Ya mayar da y'ayamsa makaranta. Ya kuma saka masa albashi duk wata.
Ya yiwa babbar y:arsa da take da hankali hanyar samun aiki in tunda ta yi karatu. Kuka ba irin wadda Alhaji Auta bai yi ba.
Lokacin aikin hajji na zuwa ya biya mini ni da shi, da Aliyu da Yaya Ummi. Da Kuma babbar yarsa da suke uba d'aya. Na so ace Ya biyawa Inna tunda itace babanmu bai samu sukunin kai ta ba.
Ya ce zata je amma sai ya kai Gwaggo Umrah ta dawo. Domin ya sani ta taka muhimmiyar rawa wajen dannata a loakcin da shaid'anu da mugaye suka so yin tasiri a rayuwar aurenmu.
Ummi kuwa mutumiyarsa ce. Kafin ya kai kowa Hajj sai ya kai ta a gidan Marina.
Haka muka dunguma ni da Yaya Ummi muka tafi tare da shi.
Duk da yanzu ba a iya cewa komai akanmu akan gidan Marina sai da aka yi yamididin yan dakinmu na ware masa ta kai. Da azumi ya kai Iklma an kasa gane ba dan ni ya kai ta ba,dabida Aliyu ne. Ko wata ce matar.kuwa zata je. Yaya Ummi kuwa ko ba ni ce matarsa ba zai kai ta. Cikin kankanin lokaci sunan Baban Marina ya koma Alhaji babba a wajen yan'uwansa. Ko yaransu ne zasu yi abu zasu ce basu da ta ce wa sai abin da Alhaji Babba ya zartar. Tun ana ganin abin daban har aka saba. Shekarar Bulkachuwa d'aya a matsayin kwaishina ya rushe gidan Marina. Ya yi gini na alfarma na zamani. Kowa part dinsa aka kawata shi, aka zamantar da shi. Kowa anmasa bene. Gefen Dada ne babu bene, gini mai suna hini aka yi. Hatta can ciki inda akace ya zauna da Yabi loakcin auren sai da ka rushe shi aka tamfatsa gini. Gidan Marina ya sake yin fice a Toro. Shi kuwa Juwad g.r.a yake nasa ginin na alfarma. Wanda ha siya da nufin ya saka Nasiba a ciki ya ce ya bawa Yabi halak malak.
Gidansu na Bulkachuwa ma ya sha gyara tunda gini ne mai kyau mai aminci. Gata na ban mamaki yake yiwa magaitda abokiyar zamanta. Koami tare yake kai musu sai abin da baaytasa ba. Haka nan sisters dinsa mata ko wacce ya sama mata abin yi,.ya dauki yaransu ya kaisu makarantu daban daban.
Ta bangarena hankalina ya kwnata domin na daina zullimi akan sha'anin Tijjani. Hatta saka masa idon da na yi akan sha'anin mata yanzu na janye domin aiyukan da suke gabansa bashi da sukunin wannan lamarin. Na murje na ciko. Na mallaki dukkan abubuwan k'awa na ado da kwalliya. Gwala gwalai manya suturu. Malaysia fabrics na Umm Nihla. Mota. Ga yarana suna karatunsu cikin nutsuwa. A yanzu haka cikine da ni na watanni biyar. Husna ta yi shekaru uka.
Ya dankara mana gida mun tare tun bara. Tun lokacin kuma ya dawo da Dada kusa da mu. Part dinta daban. Idan ta gaji sai ta tafi Toro. Haka idan ta gaji da Toro sai ta taho wajenmu.
*Yajin Annur duniya ne Hajiya domin na jarraba shi, akwai na garlic, akwai marar garlic, akwai na daddawa, tana yi ga masu jego*.
*Akwai man shanu, akwai garin danwake*.
*08039183880*
A yanzu kowa Hajiya yake ce mini. Burina ya cika. Na kai Gwaggo Umrah, na kaita hajji. Nazira ta je, da su Yaya Salamatu. Mama ta je Umrah. Inna kuwa aikin hajji ta je bara.
Baban Kasuwa da na Tsakiya suma sun je Umrah da azumi. Shi kuwa Alhaji babba ta bakinsu duk azumin duniya tunda muka samu dama a can yake yi. Sau uku ke nan. Duk shekara idan zai tafi, zai tafi da matarsa daya. Haka Babah da abokiyar zamanta.
Kowa ya yi hakuri da sake saken zuciyarsa, ya yarda da hukuncin Allah baya canjawa zai ga alheri mai yawa. Babah Maryo da kanmu muka kai mata ziyara bisa umarnin Babah. Ta saka ya gyara mata gidanta. Aka sanya y'aya'n ta a makaranta. Tunda Yaya Ammar ne kawai ya yi karatu mai zurfi. Nasiba kuwa tuni ta samu aikinta tana cikin rufin asiri. Haka nan Tijjani ya yi k'ok'ari an daga darajar Ammar a wajen aiki.
Amma kunya gabad'aya ta hana Baba Maryo sakewa. Umrar bana ma tare Babah ta ce zasu tafi. Hakan kuwa aka yi.
Babah da Bulkachuwa da Baban Marina sun fahimtar da ni yadda saka alheri idan an yi maka sharri na matukar tasiri a dukkan mu'amala mussaman ma a harkar zumunci.
Duk yadda lokaci ya yiwa Tijjani karanci, ina da lokaci na mussaman a wajensa. Da zarar ya shigo gidan zai kashe wayoyinsa ya tisa ni a gaba da y'aya'nsa. Soyayyar nan da nake so bai fasa shayar da ni ba. Haka nan a shimfi'da sai ya tsiyayar mini da ruwan kai tas. Da kaina nasan an yiwa Baban 2 baiwar lafiya da kuzari.
**
Zaune muke a babban falona ni da dukkan yan'uwana da muka taso tare domin a yanzu kowa so yake ace yana kusa da ni. Hatta Maijidda da Nasiba kuwa. A dalilin na haihu sati hudu baya, sai yau na shirya walima tunda c.s aka yi mini. Na Kalli Nazira na ce Adda Nazira dan Allah ki sam mini kiba. Kin ga yadda kika tara teba kuwa?"
Ta ce baki ga Maijidda da Nasiba ba sai ni? Ni maganin rabge tumbi ma nake nema. Na ce "zansa a kawo miki daga Kano."
*Bada jimawa ba zan zo muku da littafan Hanne Ado Abdullahi*
*Marubuciyar Wanka da gari da Kuma wacece uwa?*.