← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 146

Sashe 136

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** *Watanni biyu* Ana cikin haka kwatsam gwamnatin tarayya ta rage lakcarori cikin ikon Ubangiji har da Yaya Jabir aka sallama. Gabadaya mun ji ba dad'i mussaman da yake ya tara iyali. Tunda amaryarsa ma yaranta biyu, Maijidda na da biyar domin haihuwa take akai akai tamkar da gayya. Zaman Kaduna ya gagara tunda dama a quayers yake. Kan dole ya tattaro ya dawo Toro. Na tausaya, na ji babu dad'i dole a aka hak'ura tare da fatan Allah ya kawo wata damar. Baban Tsakiya ya dinga fad'in sa hannu ne. Kuma a cikin wadanda yake zargi har da Baban Kasuwa. Domin ya ce ai tunda Jabir ya kara aure yake ta tsiyace wa. Tabbas hannu aka saka masa. Yayin da Baban Kasuwa da ahalinsa suke murnanr hakan da ya samu Yaya J. Tunda sun tafi a cewar Jabir yana fifita amaryarsa akan Maijidda da take yar'uwasa kuma uwar y'aya'nsa. To yanzu sai ya yi rashin mutuncin su ga ni. Daga Baban Tsakiya har Baban Kasuwa kowa so yake a ce Baban Marina a bayansa yake. Har yau din nan sun fishi kudi. Amma ya fisu gata da rufin asiri . Domin a yanzu yana fita wajen sana'arsa saboda sabo da kuma mike kafa. Amma duk watan duniya sai mun ajiye abincin da za'a ci a kofarsa da kudin cefane. Hatta sabulun wanki da na wanka da zai bawa iyalinsa mun dauke shi. Hadawa muke yi gwagwadon k'arfin mutum. Ni ce sha kundum. Hakan da suke gani kuma sai kowa a cikinsu yake son ya shige masa, ya soki d'an-uwansa a gabansa. Shi kuwa baya biye wani a cikinsu suyi hirar wani. Amma ya karbe su da fuskar afuwa da sassauci yake mauaamala da su. Tunda ba abin da Ubangiji bai masa ba. Jahilci ne ka ce zaka rama sharri da sharri. Bakar Taada ce ka ce zaka maimaitawa wani irin kuskuren da aka yi maka. Mussaman akan zumunci, matukar ana son gyara, matukar ana son cigaba. To a bar BAK'AR TA'ADAR riko da kullaci. Afuwa da yafiya yana kawo soyayya da masalaha a tsakanin jini guda. Tashin tashina kuwa yana dawo da gaba da k'iyayyar juna. Allah ya yafe mu gabadaya. Zaune nake kusa da Babah yayin da Anas yake kan kujera su Hanif suna ta dabdala a jikinsa. Babah ta kalle shi ta ce "Kai bana son iskanci ka ji. Da wasa kake ko kuwa da gaske kake wannan maganar?" Da murmushi ya ce "Wallahi ta makance Babah! Ga mamakinmu sai Babah ta fashe da kuka tana fad'in"Allah mun tuba. Allah ka yafe mana. Ni dai ka shaida na yafe mata. Anas ina rokon arzikin ka, ka yafe mata. Addu'ar da ka yi mata cikin fishi ne Ubangiji ya karba. Ka yi hak'uri. Yau na sake gasgata A guji addu'ar wanda aka zalunta, mussaman idan ya yi ta cikin fishi da neman agajin Allah". Nan da nan ya ce "Na yafe mata. Ko yanzu idonta ya bude zan yi murna, idan bai bude ba kuwa Allah yasa ya zame mata kaffara. Amma ai ko yanzu ta ga karshen sharri. Tsofe tsofe da ita ta yi mini bakin sharri irin wannn. Haba wannan duniyar cike take da rudani. Ace wai jinin ka bai k'i ka tozarta ka yi bak'in ciki ba?" Ta share hawaye tana fad'in "Babu wanda zai mori zumunci sai wanda ya yi hak'uri ya hadiye komai, ya yi sassauci ya kuma yi afuwa. Zumunci da kansa ya roki Zati ya ce "Ubangiji ka jefa wanda ya yanke ni cikin wuta. Ubangiji ka tsananta wa wanda ya tsananta mini. Allah kuma take ya karbi addu'ar zumuncin. Shi yasa Annabi ya yi ta jan kunnenmu akan zumunci. Hatta makoci da aminin iyaye sai da Annabi ya yi ta jan kunnenmu a kansu bare kuma wadda nasabarku guda. Akwai bukatar mu ninka hak'uri da kawaici, hadi da yafiya idan kuwa ba hakan ba, gaisuwa ma sai ta gagara a tsakanin jini guda." Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Da dukkan zuciyata na yafe mata. Na yafe wa kowa. Allah ya cigaba da dafa mana." Ta ce "Ameen na gode Anas. Na gode da ka yarda da maganata Ubangiji ya yi maka albarka". *Ya ce "Ameem Hajiya Babah tamu". ** Jumaa da yamma muka yi Toro. Muka tarar da baba Maryo a zaune a dakinta jikinta ras. Ido kuma gwaragwara amma bata ga ni. Fadi take yi "Na rantse bakin Anas ne ya kama ni. A yiwa ma'aiki a kira mini shi. Wallahi ya fini gaskiya. Hauwa ki yafe mini. Ki roka mini afuwa a wajen Yabi da Tijjani." Ta kece da kuka. Na matsa kusa da ita na ce "Baba ki yi hakuri. Ban kullace ki ba. Na kuma yafe miki. Na Ari bakin Tijjani shi ma ya yafe miki. Allah ha baki lafiya." Babah ma tana kuka ta rik'e hannunta ta ce "Sannu da ibada Maryo! Tuni na yafe miki babu komai a zuciyata game da sha'anin ki. Sai alheri. Allah ya yafe mu gabadaya ya kuma gajarta miki wahala. Sannan Anas ya yafe miki tuni, zan kuma k'ira miki shi ki ji da kunnen ki. A take Babah ta kira Yaya Aliyu ta ce ya bar komai gobe ya zo ya dauke su zuwa asibiti a duba ta da kyau. A Toro Babah ta barmu suka nufi asibitin Jos tare da Yaya Aliyu da kuma Yaya Ammar. Dama Nasiba a can take aure dan haka babu matsalar abinci. Kamar jira jikina yake na zo Toro ai sai kawai na hau wani irin zazzafan zazzabi. Hak'ora na har kad'uwa suke yi. Ga azabar ciwon k'asusuwa. Sai na ji tamkar ana kwankwatsa mini jikina. Kullum jiki sai dada rikice wa yake yi. Amai ya tisa ni a gaba. Ba dama a d'ora tukunya yanzu zan fara amaye amaye. Hankali iyayena ya tashi. Da yake yanzu mamam ta hakurkurtar da zuciyarta ta daina tsiyataku, aka rasa me za'a ce mini. Tunda alamu k'arara na mai shigar ciki sun bayyana mini. Gwaggo ta rasa me zata ce mini. Sai da dare ya yi dare. Ta yi gyaran murya bayan ta gama danna mini jiki ta ce "Yabi alamun shigar ciki nake ga ni a tare da ke" Sanin a cikin zullimi take ya sanya ban tsaya noke noke ba na ce "Ni ma ina kyauta zaton shine Gwaggo". Ta hau salati ta ce "Cikin haihuwa Yabi?" Na ce "Shi fa Gwaggo". Ta dauki sabon salati ta ce "Ta ina kika samu ciki Yabi? Nasan dai da ikon Ubangiji ba zaki yi ashararanci ba, ina kyautata miki zato." Na saki ajiyar zuciya. Ga shi ina jin jiki. Ina nishi na ce "Na gode da kyakkwar shaida Gwaggo". Daga haka na kulle bakina a dalilin yadda nake jin tsananin kwankwatsa a duka jikina. Kan dole ta tashi doro alwallah ta tada sallah. Ganin bata samu nutsuwa ainun ba. Ya sanya bayan ta yi sallama na ce "Gwaggo Zaton da kike kyautata mini tabbas hakane. Kuma hakkun ciki ne. Idan Babah ta zo ki tuntube ta ki ji me zata ce akan hakan". Ta zuba mini ido ta ce "Yabi a gidan kurkun kuka yi cikin ko a ina?" Na fara nishi ina fad'in "Ki bari ta zo, ni ba iya bayanin nan zan yi ba. Dan Allah ki zo ki cigaba da matsa mini kafafuwana". Ta sake daukan salati tare da tafa hannu. Sai nanata iko sai lillahi take yi. Sai ta yi shiru sai ta sake zabura ta d'auki salati tana ce wa "K'warzaba da jarabar yaran yau ta kai kure wa. Ni Asma'u ina kallon zamani". A kan dole ta cigaba da yi mini tausa. Tana yi, tana hirji domin ta shiga mamaki mai yawa. Da safe da Baban Marina ya shigo duba ni. A sanyaye ta ce "cikine da Yabi Alhaji". Babu dar ya ce "Ma sha Allah! Ai rabo ba k'aramin al'amari ba ne. Allah ya raba lafiya". Ta yi galala ta ce "Alhaji na ga baka ka'du ba! Ya murmusa ya ce "kad'uwar me zan yi bayan na gasgata Yabi tamkar yadda na gasgata yunwar cikina. Ita tasan yadda ta had'u da mijinta. Tana da miji kuma dan na ganta da ciki sai na bi ba'asi, akan me?" Ta ce "To ai kowa yasan baya nan, sai kuma a ganta da ciki, kana jin yadda ake daura mata magana haka siddan. Ina kuma a ganta da ciki". Ya ja tsaki ya ce "Idan har kika daka bak'ak'en taadodin jama'a babu abin da zaki yi. Ya mik'e yana ce wa "Sannu Allah ya raba ku lafiya." Ya saka kai ya fice. Satin su baba biyu sannan suka dawo, cikin sa'a ido daya ya budu. Daya ya mutu. Aka yi murna da yi mata barka da arzikin da ta auna. Babah tana zaune a dakin Gwaggo. Yayin da nake kwance akan k'aramin gadon. Na samu sauki, amma jikin babu k'warai. Gwaggo ta ce "ikon Allah Yabi dai ciki ne da ita." Ta dauke kai ta ce "Ho ke kam yanzu kina neman baci da magana. Ina dalilin wannan tuyar da kike yi ne. Nasan da shi tun kafin mu zo." Gwaggo ta sake ce wa "ikon Allah sai kallo. Abin ne yake dafa ni. Wato kinsan komai ke, shi yasa ta ce idan kin zo, na ji a bakin ki". Babah ta mik'e ta ce "Sai ki yi ke kad'ai ina dalilin bin wannan diddigine haka? Mace da mijinta". Da mamaki Gwaggo ta sake ce wa "To wai a kurkun, a ina suke haduwa ni Ma'u! Babah ta fice ta ce "A a nima ban sani ba. Sai ki tambayi mijin nata tunda ita kin saka duk ta sururuce da kunya. Domin ke sai akan girman ki zaki baci da magana, sai ki je ki gano shi, ki tambaye shi yadda aka haihu a ragaya ". Ta fice da sauri. A haka muka sake shafe sati biyu. Yaya Aliyu ya zo ya kwashi yara ya ce tunda ba tafiya zamu yi ba, to ba zasu yi asarar karatunsu ba. Na kuma gane Babah tana son ta zauna da Dada a dalilin ta damu da lalurar da ta sami autarta. Sannu a hankali na fara warware wa. Matan gidanmu sai nan ake yi da ni. Mama da kanta sai ta tambayi
Chapter 136 · 0% Book details