Sashe 23
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take na tuno Nazira bata fuskantar tsanani irin nawa a wajen Baffannin namu. Amma kuma ko ka'dan bata samun sakin fuska da alherin da suke yiwa ya'yansu. Na sake tafiya dogon tunanin yadda Baban Marina yake mua'amalantar nasu yaran. Mua'amala ce ta sassauci da ja a jika. Domin duk talaucinsa, yana k'ok'arin siyan albasa ko su mangwaro ya ce mu mika kofofinsu. Hakanan indai zai yi aski sai ya ha'da da ya'yansu an musu ya biya. Bayan nan duk wani rikicin da ya'yansu zasu rakito shine zai yi ta zarya yana bada ha'kuri har sai komai ya daidaita. Amma su ba ruwansu damu, wani ikon Allah Yaya Musa da yake a lalace sun fi sonsa, sun fi yinsa, sun fi tattalin farin-cikinsa. Na jijjiga kai a fili kuma sai na ce "Allah haska kofar Baban Marina, Allah ka jibanci al'amarinsa da na ya'yansa. Na shige cikin gida ban doshi k'ofar Dada ba. Yanayin da na tarar da Babanmu da ahalinsa ya sake sanyaya mini jiki. Na shiga bakina da sallama na isa kan tabarmar da suke zaune na tsugunna ina gaishe shi cikin girmama wa. Ba walwala Baba ya ce "Asiya me kika zo yi? Ba na ce sai na neme ki ba?" Da rawar murya na ce "A mini afuwa Baba! Na kasa jure ji daga gareku ne." A sanyaye ya ce "Na miki afuwa Yabi zo ki zauna. Da rarrafe na karisa kusa da shi a dalilin rawar da jikina yake yi ya sake ta'azzara. "Na yi godiya Baba Allah ya k'ara maka lafiya, ya shirya maka zuri'a, Allah ya mayar da ahalinka wasu masu fa'da aji". Ya yi murmushin da babu nisha'di. A sanyaye ya ce "Ameen Yabi! Duk yadda zan yi ba zan iya cire miki wannan BAK'AR TA'ADAR k'ullaci da ta shiga ranki ba. Amma abin da zan fa'da muku duk taku, duk wanda bai mutunta y'anuwana ba, to nima kar ya mutunta ni". Jikina ya yi sanyi, na yi kasa da kaina, na kasa cewa komai. "Yabi". Ya k'ira ni murya babu amo. Na amsa a hanzarce "Na'am Babanmu". Ya yi gyaran murya ya ce "Nan da kwanaki goma sha biyu auren y'anuwan ki. A duk wanda kuka taso ke da Nasiba ne kawai babu ku a cikinsu. Da gobe zan je na sanar da ke maganar a nutse cikin kwanciyar hankali. Na tura wa iyayen Abdulrashid su turo ayi magana to bansan inda aka haihu a ragaya ba, sai suka aiko mini da sun yi wa d'ansu mata tuntuni, ba da yawunsu yake neman auren y'ata ba." Jikina ya sake daukar bari a dalilin idan na fahimci maganar Babanmu kenan zan rasa Yaya J da kuma Abdul tashi guda, wannan shine biyu babu, kamun gafiyar b'aidu. Na tattaro dukkan jarumta na yafa a dukkan sassan jikina da fuskata. Na ce "Babu damuwa! Allah ya sanya alheri. Amma Baba har da Adda Nazi kenan?" Na fa'da cike da karsashi irin na tsananin karfin hali. Ya ce "Da ita Yabi, sai dai bana jin za'a yi tariya da ita, domin ban mallaki komai na aurenta ba, tunda titsiye aka yi mini." Na kalli dukkan yaran gidanmu masu hankalin suna wajen hatta Yaya Musa kuwa. Hawaye ya b'alle mini na ce "A a Babanmu da ikon Ubangiji a ranar zata tare. Na kalli Yaya Salamatu na ce "Yaya" Sai kuma na fashe kuka sosai. Dukkansu matan sai suka taya ni kukan in ban da Yaya Ummi da take Jin zafin yadda nake damuwa da lamarinsu alhalin ita ma ba sonta suke yi ba in aka dauke Naziran. Da rauni Yaya Salamatu ta ce "su uku sun kawo dubu sha biyar biyar, yan dakinsu kenan. Sai ummi ta kawo dubu biyar, Ni kuma na bayar da ashirin maigidana kuma ya bada buhun masara da na shinkafa ayi hidimar biki da su". Su Salisu kuwa sun ha'da hamsin a tsakaninsu dan haka dari da ashirin ne a k'asa kacal". Nan da nan na zaro magana tamkar babbar mace na ce "Ai kuwa sun isa Yaya, kuje ku siyo mata katifa da labule da ledar tsakar daki. Na kunce hannun zanina na kunce na fito da kudi kimanin dubu sha bakwai da dari takwas. Na ce ga nawa a siya mata bargo da zanin gado. Su Mama ku fito da kwanuka da tukunya. A kai ta a hakan da ikon Ubangiji watarana sai ta yiwa wani kayan daki na alfarma, ai duniya ce mai rawar y'an mata na gaba ya koma baya". Hatta Mama a wannan ranar na ga kallon sassauci da adalci take yi mini, domin da ta ga na sake dauko bankina na mik'a wa Nazira na ce "Ki fasa ki yi dinkin fitar biki nasan zasu ishe ki tunda kinsan mu din masu k'aramin karfi ne, masu nema a wajen Àllah." A fili take fa'din "Yabi da Nazira sai Allah". Baba kuwa zuba mini ido ya yi, tsawon lokaci kafin hawaye ya goce masa. Duk muka ha'du aka yi ta kuka tamkar an ce ya mutu ne. Domin ita kanta Mama da take ha'da kai da matan su Baban Tsakiya suna sake tsananta mana, ta sha mamaki da ta ga suna yiwa ya'yansu hidimar aure basu yi kara sun saka da Nazira ba. Wata'kila a haukanta zasu yi ko saboda da ita. Da rawar murya Baba ya ke fa'din "Allah ka sake jefa soyayya da tausayi a tsakanin ya'yana, Ubangiji na gode maka". Yaya Indo ta kira Malam Yunus ta fa'da masa ku'din lefe ya bayar yadda zai iya ba sai ya yi ba , domin kuwa muma abin da zamu iya za'a yi. Da yake ba yaro bane ainun, sai ya gamsu ya ce zai yi mata lefen yadda ya sauwaka, sannan zai bawa Yaya Salisu ku'din da ya sauwaka shi mutunci ya gani dan haka komai zai yi. Ba wanda ya san me ake ciki domin kowa ya zuba ido yana jira aje ganin dakunan amare Yayin da ta bangarena nake ta danne damuwar auren da Yaya J zai yi da Maijidda. Ita ka'dai ce amaryar da bata da kuzari a dalilin babu ha'din kai ko zumudin ango, komai sai dai mahaifinta ko na angon su yi mata. Gefe guda kuma Nasiba ta susuce domin ba karamin son Bulkachuwa take yi ba, wanda aka ce ya fito kuma a dangin Babanta sun ce bai shirya ba sai bad'i. Bulkachuwa kuwa yarinyar da suke takaddama ta haihu an yi gwajin halittar dan Adam bashi da alaka da jaririn. Sai dai an yi masa hukuncin bulala tamanin tunda ya amsa da bakinsa ya ta'ba takarta. Wannan lamarin, da bulalar ya yi matu'kar sururuta shi. Ya zama abin tausayi, duk wani iyashegensa ya zubar da rabi. Kowa ya ganshi sai ya tausaya masa. Hatta ni da bama ga maciji sai da na yi masa jaje. cike da alhini, ya dinga fa'din na gode "Asiya Toro, ki yafe mini, a duk sadda na tuna addu'ar da kika yi mini cikin fishi da kika ce sai na hadu da sharrin mace, sai na ce ashe dai Asiya bayan samun tallafin dan aljani yayin fa'da, har baki idan kika yiwa banu adam sai sun taimake ki, ya zama wajabat. Shiyasa na k'udire zan roke ki, ki mini addu'a na zama yadda mutane na gari suke". Na girgiza kai na wuce shi "Ina cewa "Allah ya shirye ka Tijjani". Ya d'aga murya ya ce "Da biyu kika yi wannan addu'a domin da zuciyarki fes take da ni Yaya Tijjani zaki ce". Ban tsaya ba, bare na tanka shi, a zuciyata kuwa ina fa'din mashiririci, ba sauya wa zaka yi ba, borin kunya ne kawai, ka zubar da mutuncinka a idon kannenka da iyayenka, Allah ya shirye ka kawai. Shikenan sai na dawo gida, muna ta shirin bikin Nazira. Auren da ya zo tamkar dirar mikiya, ya yi matu'kar rage mini tashin hankalin da nake ciki. Kitso da lalle nake yi babu hutu, tun safe idan na zauna sai magariba, sallah kawai take tayar da ni. Haka nake mika ku'din ga Baba ina fa'din "A dinga siyan kayan cefanen biki Baba" Da farin-ciki yake fa'din "Madallah da Yabi Asiya". Kallo daya za'a mini a gane ina cikin tasku kawai boye wa nake yi, sannan son Babanmu ya fita kunya da tozarta da ake son ya yi, ya danne wanccan damuwar. Domin yadda nake kishin Babanmu da yan k'ofarmu bana jin anan kusa za'a samu mai yin hakan. Shiyasa na cire son jiki, da lalaci nake sana'a, Ubangiji kuma ya haska, ya saka mini hannu, domin a rana ina hada dubu shida zuwa bakwai, mussamna idan kwanakin da ake yin biki ne. Da ce a birnin Kano nake yarfa kunshin nan ai da ku'di masu nauyi zan dinga ha'da wa, amma hakan ma na gode sosai, tunda mafi yawa manyan mata idan sun zo basa bayar da iya ku'din sai sun mini k'ari. Bana kuma jin k'yashin na bayar da komai dan mu yi hidimar mu cikin rufin asiri. Duk yadda Yaya J yake son mu ha'du na rufe kofofin da zasu sa mu kebe. Ranar litinin dukkanmu muna wajen Dada. Ana ta hira, na yi lakwas a dalilin bani da kuzari, ba k'aramin cizona auren J da Maijidda yake yi ba, har addu'a nake yi kada a wayi gari aga zuciyata ta buga a dalilin ba'kin ciki. Kwana nake yi ina kuka, ina kalubalantar wannan hukuncin da aka zartar mini tare da tsanar Baban Tsakiya da Baban Kasuwa. Tabbas a idona su din ba kowa bane face mutane masu son kai kuma y'an jari hujja. Dada sai farin-ciki take zata aurar da jikokinta kusan goma. Ta kalle ni ta ce ",Ke da Nasiba ne aurenku ya yi gardama, ga shi kune fitanannu." Ban kula ta ba domin abin da yake zuciyata fadinsa da ciwonsa sai ni da mahaliccina. Balle Nasiba da ta bari halin da take ciki ya bayyana a komai na ta. Ni mamakin da take bani wai akan Bulkachuwa take wannan ba'kin cikin, sannan abin kaicon shi bai ce yana sonta ba, kawai ya lura da yadda take mararinsa sai yake amfani da hakan yana sata tana yi masa bauta. Misali komin dare zai kawo indomie ya ce ta dafa masa, ko kuma ya ce ta dafa masa ruwan wanka,