← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 146

Sashe 142

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*INA MUKU ALBISHIR AKWAI DUKKAN TSOFAFFIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA SALIHA ABUBAKAR ZARIA*
*ZAKU SAME SU SOFT COPIES A HANNUNA*

*HAKA NAN AKWAI WASU DAGA CIKIN LITTAFAN MARUBUCIYA HAJIYA HAFSAT C SODANGI, SUMA SOFT COPIES*

*HAJIYA HANNE ADO ABDULLAHI?*
*MARUBUCIYAR WANKA DA GARI DA KUMA WACECE UWA?*
*TO ITA MA TAKANAS NA SAMO MUKU LITTAFANTA DOMIN KUN SANI TA YI RUBUTUN MASU MA'ANA*.
*LITTAFAN DA YAWA, AMMA AKWAI DISCOUNT DOMIN SO NAKE KU YI TA SIYAWA Y'AYA'NKU DA KANNENKU LITTAFAI MASU DARASI DA MA'ANA*.

*BA DA JIMAWA BA ZAN ZO MUKU DA SU*.

*0803277333*.

Da kaina na je Toro na sanar da Baban Marina cewar Tijjani ya biya mana Umrah ni da Dada Aliyu kuwa ya biyawa Babah. Ni kuma na biya masa.
Ya yi k'asa kansa tsawon lokaci bai yi ko da motsi ba bare ya yi magana. Ya jima kafin ya d'ago. Na ga hawaye jagejage a fuskar sa.
Nima nawa hawayen ya kwace mini amma ni kam na farincikin yadda Ubangiji ya yiwa fafutukar sana'ata albarka nake yi. Domin bani da burin da ya wuce na sanya Baban Marina farinciki tun ina mitsitsiya ta. Gorin da ake mini, haihuwa ta ce ta tsiyata shi. Da kuma bak'in cikin yadda ya zama koma baya a cikin gidanmu na matuka mintsinin zuciyata.
Da k'yar ya yi jarumtar ce wa "Na sha fad'a miki ke kad'ai gayya ce Asiya. Na fad'a miki zaki yi albarka. Na dad'e ina fad'a miki akwai lokacin da zai zo da kowa sai ya so ki har makiyan na ki. Ga shi na fara ganin sakamakon alherin da Ubangiji zai yiwa hak'uri da juriyar da kika yi a rayuwar ki. Allah ya yi miki albarka. Daga nan har kasa ta rufe mini ido na yafe miki, kina cikin farar addu'a ta. Allah yasa y'aya'n ki su yi fiye da ke. Allah ya miki tukuici da alheri. Kin yi hak'urin aure, kin yi juriya. Da ikon Allah ba zaki sake fuskantar tsanani a gaba ba."
Ina kuka na ce "Allah ya amsa Babanmu! Na gode Allah ya k'ara lafiya.
Ya ce "Ku tafi da gyatumar ki Yabi. Kin ga dukkanku mata ne. Da ikon Allah zaki kai ni."
Na girgiza kai na ce "Zata je Baba! Amma wannan kudin na tara kaso uku cikin hudu da sana'ar da na rayu ina yin ta. Kai nake son ka je, dan ka ji dad'i ka kuma godewa Ubangiji da ya jarrabe ka da fitinar yan'uwa. Sai kuma ya baka y'aya'n da zasu sadaukar da komai dan ka yi murmushi. Ka je ka yi mana addu'a. Ka kuma tayamu addu'ar Ubangiji ya kubuto mana da Tijjani ".
Sai kuka na sosai ya k'wace mini. Abin mamaki sai shima ya taya ni kukan muka dinga yinsa a hankali.
Da yake a dakin Gwaggo yake. Ta shigo da Husna a hannunta da ta fara kukan neman nono. Ta tsaya cak bata miko mini ita ba. Ta sassauta murya ta ce "Ayyah Yabi baki ga kullum girma sake kama shi yake ba? Me yasa kike kasa hak'uri a idan kina gabansa? Kin san yadda kukan ki yake rikita shi kuwa? Kalli irin kukan da yake yi mana. Me yasa kike rasa dukkan jarumtar ki a gabansa?"
Na kasa magana. Sai shine ya ce "Ni ne nake rasa dukkan jarumtata akan lamarin Yabi. Tana matukar bani tausayi, kuma dama ita ce raunina a cikin dukkan y'aya'na. Shiyasa Ubangiji yake ta jarabtata akan sha'anin ta. Tafi kowa shiga garari da kalubalen rayuwa. Asma'u ki ji tausayin ta?. Ki sake ninka addu'ar da kike yi mata. Zauna a zaune ki ji al'amarin da ta zo da shi."
Yana hawaye ya fad'a mata zuwn nawa albishir na yi masa zai tafi gabas. Yana rufe baki itama ta fara hawaye tana fad'in Allah mun gode. Ina taya Yabi godiyar yadda ka cika mata burin ta, na mayar da Alhaji dakin ka. Allah ka k'ara yaukaka mata arziki, ka shirya mata zuria. Ka mata tsari da dukkan abin da zai cutar da ita ko iyalinta".
Ya k'ira Mama da Inna ya fad'a musu alherin da ya same su ya rufe da ce wa kada su fad'awa kowa sai abu ya kankama. Domin tafiya gabar kiran Allah ne.
A gurgurje na je gidan Nazira na dubo yaronmu.
Da yamma muka juyo da Yaya Aliyu akan gobe Baban zai zo BAUCHI don ayi masa passport.
Ba a fito da maganar tafiyarmu ba sai da komai ya kammala ya rage saura kwanaki hudu.
Baban Marina da kansa ya fad'awa y'an uwansa cewar zasu tafi Saudiya. Da Yabi da diyarta da Dada Tijjani ya biya musu. Aliyu ya biyawa Hauwa. Shi kuwa Yabi ce ta biya masa. Suka ka'du k'warai. Amma da yake dangantarsu ta yi tsami ainun kowa ya hadiye a ransa tunda yanzu so suke ace kowa yafi kusa da Baban Marina a tsakaninsu. Sannan basu gamsu Yabi ce ta biya ba. Duk da dai sun yi matukar sikewa da lamarinta tun auren Iklima. Zuwan tawagar matar gwamna Toro gidan Marina ba k'aramin cece kuce da girmama lamarin Yabi ya janyo ba.
Ranar talata da asuba muka nufi Kano tunda an ce shabiyun rana zamu tashi.
Karfe tara a airport din ta yi mana. Aliyu bai tafi ba sai da ya ga tashinmu. Sannan ya juya da twins da Ikilima da suka yo mana rakiya. Hamim sai kukan sharbe yake yi. Hanif sai hak'uri yake ba shi yana ce wa "Mun girma fa Hamim. Ammi ba dadewa zasu yi ba. Ba ta ce addu'a zasu je su yiwa Baban 2 ba? Husna zata raina ka fa". Suka bawa Aliyu tausayi. Haka kawai yaran suke ba shi tausayi ainun.
Bai bar Kano ba sai da ya siya musu kayayyakin wasa da na ciye ciye dan su warware gabadaya.
Kai tsaye a Madina muka sauka. Mun gaji likis. Dole muka kwanta. Dada sai addu'a take yi tana fad'in "Allah k'amshi ya cika hancina, haske ya cika idona, k'arfi ya yiwa gangar jikina k'awanya, farinciki da imani sun cika zuciyata. Allah ka karawa Annabi daraja. Allah ka karbi addu'ar da zamu yi, ka bamu k'arfin da zamu yi ibada ta gaskiya."
Sai ta zauna. Sai ta zabura ta je jikin windo tana leken asumayar masallaci ma'aiki. Tana kuka tana fad'in "Rabbani yadda ka sake yi mini gatan ganin koriyar gubba ta d'an Amina mai wuyar ga ni. Allah kasa zan gan shi da idona. Allah ka bani ikon rokon gafararka idan na shiga rauda. Allah ka shirya mini zuria, ka jefa soyayyya a tsakanin ahalina. Allah na yi tuba. Allah mai babban suna aiko ni ya yi takanas, Ubangiji a karba a sassauta a kubuto da shi albarkacin masoyinka Baban Nana".
Duk juyin da zan yi zan ga idonta biyu. Babah kuwa barci ta yi sosai domin bata runtsa ba a jirgi, ita take ta fama da Husna.
Daf da asuba muka tashi, muka yi alwallah muka nufi masallaci. A harabar hotel din muka had'u da Baban Marina shima ya fito zai tafi. Na kalle shi cikin sabuwar jallabiyar da na siya masa guda uku a Kano. Ya yi fes da shi. Garin Madina rahama ne.
Gabadaya zukatanmu cike suke da shauki da rauni. Duk juyin da muka yi da Dada ta saka silifas din ta. Ce wa ta yi "Wane mutum ta taka k'asar Madina da takalmi? Mu dai da muka ga zamu taka ba zata ce komai ba. Allah ya yafe mu kawai"
Kan dole muka k'yale ta. Domin har muka yi kwanaki biyar a a Madina bata yarda ta saka ba. Duk ranar da aka yi ranar juma'a ma haka ta tako. Sai da muka shiga motar tafiya Makkah sannan ta saka takalmi, tana hawaye tana fad'in "Allah ina son na sake dawowa. Idna ban samu damar ba, na yi godiya. Allah karbi addu'ar da muka yi."
A Makkah kuwa har tausayi suke bani tunda muka je dukkanmu a masallaci muke kwana. Mu yi sallah, mu yi dawafi. Duk shekarun Dada bata zama. Ko dan yar firit ce irina? Ban sake gasgata komai na Dada na kwaso a halitta ba. Sai a tafiyar nan da muka yi. Kamar da muke yi ta baci. Na tsinci kaina da addu'ar kada Allah yasa na yi halinta idan shekarun girma suka cimma ni. Tunda ta sha fad'ar hatta fad'an da na yi ina karama itama haka ta yi a lokacin kuruciyarta.
Baban Marina kullum sai ya ce "Dada yau ki kwanta ki huta, Hauwa ke ma ki huta, Ubangiji ya ji addu'ar mu da ikon Allah Tijjani zai fito. Idan kuwa har muka ga bai fito ba, to tabbas zamansa a can yafi alheri. Ku duba shekarun da Annabin Allah Yusuf. Da'n Annabin Allah Yakub, d'an Annabin Allah Ishaq, d'an Annabin Allah Ibrahim A.s. ya yi a kurkuku. An tambayi Annabin Rahma wanne mutum ne yafi kololuwar daraja da nasaba, sai ya ce D'an uwana Yusuf A.s. Amma ya yi shekaru masu nauyi a sijin. Hakan bai zame masa tawaya ba, sai ma k'ara masa kusanci da Ubangiji ya yi. Bayan ya fito kuma Ubangiji ya karrama shi daga bawa ya koma shugaban kasa, kuma babban d'an majalisar sarki."
Dada tana kuka ta ce "Hakane Alhaji amma tunda zan iya bari kawai na yi ibada tuk'uru. Na nemi gafarar Allah, na nemi soyayya da tausayi da afuwa ta wanzu a gidan Marina. Bar ni na yiwa Shehu addu'ar ya fito ya cigaba da walwala cikin iyalinsa. Yabi kad'ai idan na kalla sai na ji kuka, bare y'aya'nsa. Ni dai na yafe maka Alhaji. Kaima ka yafe mini". Sai ta kece da kuka. Ya rik'e ta a jikinsa ya ce "Sha'anin uwa ai mai girma ne Dada. Hakkin haihuwa kad'ai ya isa ayi mata biyayya, a girmama sha'anin ta. A kuma dauwama ana rokar mata alherin duniya da na kiyama. Ban kullaci kowa ba bare ke da aljannata take damafare da sawunki."
Cikin kuka ta ce "Albarkar d'aki ka rabauta duniya da lahira Alhaji".
**
Kwanakinmu goma a Saudiya. Saura kwanaki biyar mu koma gida. Addu'a kam mun yi ta sai fatan alheri ya biyo baya.
Imani ya sake cika mini zuciyata. Na ji sassauci mai yawa akan kullatar da na yiwa mutanan da suke gwada mana rashin kirki. Sai na fahimci afuwa da yafiya suna warkar da zuciya, suna sake girmama mutum a wajen jama'a da wajen Ubangiji.
Kwatsam na kunna wayata sai ganin status din danginmu nake babu kakkautawa dauke da hotunan Baban 2 babu kakkautawa
Jikina ya sab'e da rawa na kasa gane me suke rubutawa domin gabad'aya na rikice!
Chapter 142 · 0% Book details