← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 146

Sashe 132

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*** Yini na yi ina yiwa wata hamshakiyar Hajiya kunshi ita da mukarrabanta. Da zata tafi ta ajiye mini kudi a envelope. Ga mamakina da na bude dubu hamsin na gani a ciki. Duk da sunzo da yawa sosai. Amma tabbas kudina bai kai haka ba. Rub'anya mini ta yi. Ban sani ba ko dan na yi jarumtar yi musu jollof din taliya mai dad'i ne. Na kuma baibaye su da pure water mai sayi tunda Ina siyarwa. Na lura ta ji dad'in yadda na yi musu, sannan ta yaba da kunshin da na yarfawa kakkaurar k'afarta fara tas. Cikin hira nake fad'a mata na iya kwalliya ma sai dai nafi bada k'arfi a lalle da kitso. Kwanaki biyu da tafiyar ta sai ga waya ta k'ira ni akan wani satin zan je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi zata je bikin d'iyar gwamnan Jigawa. Jikina ya sab'e da rawa. Ni Yabi zan je government house a sanadin sana'a ta? A fili na ce "Alhamdulillah! Ubangiji ka bani damar da zan yi amafani da ita na fito da Baban 2. Allah ka yi alkawarin taimakon wanda aka zalunce shi. Ubangiji ka shiga lamarin Tijjani." Na zauna kusa da Babah ina fad'a mata. Ta yi farinciki sosai. Na ce "Idan mun je ganinsa zan fad'a masa, idan bai amince ba zan hak'ura, tunda nasan baya son na dinga zuwa gidajen mutane". Ta zuba mini ido ta ce "Allah ya yi miki albarka, Ubangiji ya kawo mana karshen ibtilain nan. Allah ya dawo da mijin ki, zaman zai yi miki yawa babu miji a tare da ke." Sai kawai ta fashe da kuka sosai. Da rawar murya nake bata hak'uri. Ina ce wa "Zan iya Babah! Zan jira shi, da ikon Allah zai dawo a kusa ma". ** Muna ta shirin tafiya dubo Baban 2 a dalilin a irin wannan ranar ta asabar din k'arshen ko wanne wata muke zuwa duba shi, tare da kai masa kayan shopping tamkar na dan makarantar kwana. Ni nake had'a masa wannan kayan. Kudin lallena da kitso suna tafiya ne a hidimarsa da ta gidanmu domin Yaya Aliyu ne yake rik'e da mu. Daidai da pencir ban san na siyawa su Hanif ba. A yadda na taso a irin gidanmu da babu tausayi da tallafawa na k'asa ban yi zaton Aliyu zai yiwa Bulkachuwa irin wannan zumuncin ba. Na sani hidimar kayan abincinmu da baya mantawa akwai alfarmar mahaifiyarsu a tare da mu. Amma yadda baya mance wa da y'aya'n Tijjani na gamsu ko Babah bata tare da mu zai yi iyakacin kokarinsa. Da na fahimci basu mayar da hankali wajen kai wa Tijjani kayan ciye ciye ba. Ni kuwa sai na mayar da hankali, domin shopping nake yi masa mai sunan shopping. Hatta kifin gwangwani ina siya masa fiye da dozin guda duk wata. Kayan shayi da su conflakes kam ba'a maganarsu. Babah har fad'i take wai kayan suna yin yawa. Biskit irin masu dadin nan kullum na yi lalle sai na siya, kafin lokacin da zamu je, sai na yara masu yawan gaske. Sannan bana raba shi da cincin da cake. Kullum fes muke ganinsa. Illa duhu da ya yi. Amma da dukkan zuciyarsa ya karbi kaddarar da ta fad'o masa. Da wuri muke tafiya, da k'atuwar tabarmarmu. Tunda Yaya Ammar yana cikin manyan gandorurobobin kurkun bamu da matsalar komai. Domin yini muke sai yamma lis muke dawowa. Muna zaune mun gama cin abinci. Ya kalle ni ya ce "Baba lafiya bata zo ba yau?" Na yi murmushi na ce "Ta ce wai takuramu take yi, ba zata zo ba sai wani zuwan". Murya babu amo ya ce "Da ta zo abin ta." "Ni ma hakan na ce mata Wallahi". Ya kalli yaran suna can nesa damu suna kallon bishiyar mangwaro da y'aya'n suka sauko kasa kasa ana iya mika hannu a tsinko. Ya kankance murya ya ce "Little kina kewata ko?" Na yi k'asa da kai, idona ya cicciko domin babu yadda za'a yi mu zo bai mini wannan tambayar ba. Na fahimci ita ce tafi damunsa. Na kalle shi na ce "Ina kewar ka sosai Baban 2. Kullum dare idan na kalli inda kake kwanciya sai na jika filo da hawaye! Amma ina karfafa kaina guiwar cewa tunda muna shakar numfashi daya a wannan duniyar akwai lokacin da zai zo da zaka dawo cikinmu mu cigaba da rayuwa. Ina kuma da tabbacin rayuwar da zamu yi zata Fi wacce muka yi a baya nutsuwa da kwanciyar hankali. Yaya Aliyu yana matukar kokari akan gidanka. Su Yaya Salisu da su Ammar suna taimaka, bamu da matsalar komai sai rashin ka." Ya ce "Ke Baki fad'o naki k'ok'arin ba little ". Na ce "Ka sha fad'a mini, ni kake da tabbacin ba zan gaji da hidimar y'aya'nka ba. So nake ka gane ba y'aya'nka ba kawai kai kanka da mahaifiyarka ba zan gaji da hidimar ku ba, muddin ina numfashi." Ya kasa magana. Sai can ya nisa ya ce "Ina son ki sosai little. Ina rok'on Ubangiji ya taya ni son ki, ya k'ara miki hak'uri da jarumta". Cikin rauni na ce "Ameen" domin ya yi matukar ba ni tausayi. Ya saki ajiyar zuciya ya ce "jiya shekara ta d'aya a nan. Tunanin ki kad'ai yasa nake ganin na dade. Amma ban da hakan ba k'aramin gata aka yi mini ba. Domin tunda nake ban tab'a samun damar da nake yin ibada nake ambaton Ubangiji irin a wannan lokacin ba. Na gamsu akwia hikimar Ubangiji ta sakaye ni a nan. Ba ni kaina ba, ko ke addu'ar da nake yi miki little ta ishe ki, bare kuma y'aya'n ki. Shi yasa ban damu sosai ba, da aka kasa fitar da ni". Na ce "Allah ya karba. Ina kuma ganin tasirin addu'ar ka garemu domin bamu tozarta ba Baban 2." Ya ce "Ki tsananta addu'ar nan ta*RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Kullum ina fad'a miki tasirinta mai yawa ne". Na zuba masa ido, shi ma ya zuba mini tsawon lokaci muna kallon juna, idanuwanmu cike da k'walla. Ya yi k'arfin halin danne nasa hawayen ya hadiye. Ya ce "So nake na gan ki da ciki Little" Nasan yadda kike son haihuwa. Na kuma tabbatar renon ciki da hidimar bebi zaisa ba zaki ga nisan zaman da zan yi ba". Na ce "Ta ya ya hakan zata kasance Baban 2?" Domin ni kaina idan har zan samu cikin zan yi matukar farinciki mai yawa. Ya ce "Kina so?" Na daga kaina da sauri amma ban yarda na d'ago kaina ba. Domin haka kawai na ji kunya ta rufe ni. Ya ce "Shike nan zan roki arzikin Ammar ko zai mini alfarma". Na ce "Me zaka ce masa?" Ya ce "Zaki ji daga baya." Na d'ago na ce "Amma Baban 2 idan na samu ya bare kada ka ce na zubar maka fa, nasan halin ka". Ya dan murmusa ya ce "Ai ina fad'a miki ne dan na rama rikici da tashin hankalin da kika dinga yi mini kafin ki samu cikin twins". Na rufe idanuwana ina dariya sosai". Na ce "wanccan satin dai aka daura auren Nasiba". Ya ja tsaki ya ce "Ammar ya fad'a mini. Ya isa haka kuma". Na yi maza na sauya maganar da ce wa "Ka saurare ni da kyau Baban 2 ". Ya ce "Ina jin ki". Na ce "Jiya wata baiwar Allah ta mini waya akan gobe suna son na je gidan gwamnati na yiwa mai dakin gwamna kunshi. Na ce su saurare ni kad'an. So nake mu tattauna me zaka ce game da hakan. Na fi son na yi komai da yardar ka". Ya yi shiru. Sai kuma ya ce "Kuna da matsalar Wani ma abinci ko ma bukata ne?" Da azama na ce "Wallahi bamu da ita. Kuma Ubangiji yana kawo mini mutane har gida babu yanke wa." Ya ce "To bana son zuwan ki gidan mutane Asiya" Na zuba masa ido na ce "Bajq zuwa, ba Kuma zan je ba. Amma sai nake ganin da ka yi hak'uri na je wannan din. Domin ina son a shiga jikin matar gwamna. Watak'ila ta sanadin ta sai Ubangiji ya fito mini da kai, tunda ka hana ni dauko maka lauyoyi, ka hana ni neman taimakon manyan mutane. Ka bani dama yanzu,tunda ita mace ce kuma komai sai da sabab" Ya yi shiru. Kafin ya nisa ya ce "Tsoro nake ji Asiya. Ina jin tsoro kada ki samu dama mai yawa ki fi k'arfina ki k'asa yi mini hak'uri da kike yi yanzu" Ya fada hankalinsa a tashe ainun. Na ce "Haba mana Baban 2! Me yasa kake wasiwasi a kaina? Har duniya ta nade ni taka ce. Ina fad'a maka idan shekaru hamsin aka daure ka Wallahi zan jure na jira ka. Da bakinka ka fad'a mini akwai iyaye mata da suke sadaukar da kuruciyarsu saboda y'aya'nsu. Ashe ni baka gamsu zan yi irin wannan sadaukarwar idan kasa ta rufe maka ido ba. Tunda ga shi da ranka ma kana kallon ba zan iya sadaukar da komai saboda na reni yayanka ba." Ya girgiza kai ya ce "Ba hakan ba ne Asiya. Na sani zaki yi mini komai. Sannan ke yaranki basi yawa". Na ce "Ba yanzu ka gama mini albishir din zaka samo hanyar da zamu bi mu samo wasu yaran ba? Har na fara tunanin zan ga likita dan a d'ora ni a maganganun da zan zasu taimake ni wajen samun ciki da wuri. Ashe da wasa kake yi, ni kuma have nasa rai". Ya ce "Ba wasa nake yi ba. Na ce "To ka ba ni wannan damar. Bana son na yi abu ba tare da ka sani ba, bana son na bata maka rai Baban 2 ". Ya saki ajiyar zuciya ya ce"Shike nan. Amma tare da yara da Babah za'a dauke ku". Da sauri na ce "Dama tare da su zamu je. Na gode, Allah yasa hakan ya zame mana sanadin alheri". Ya ce "Ameen. Daga haka na shiga ba shi labarin Aliyu da Iklima. Ya murmusa farincikin zuciyarsa ya bayyana akan fuskar sa. Haka muka dinga hira. Har lokacin tafiyarmu ya yi. Hanif ya ce "Baban 2 sai mun sake dawowa. Hamim kuwa ya ce "To bude ka
Chapter 132 · 0% Book details