← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 146

Sashe 27

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

fa'da na ha'duwar farko, ya take kaya wa?" Ta galla mini harara ta nuna kanta ta ce "Ni kika yi wa wannan tambayar?" Na k'yal-k'yale da dariya ina fa'din "Adda Nazi manya. Yo wa nake da ita da zan tambaya, kawai fa'da mini Malama". Ta leka ta ga ko Iki na jinmu, sai ta ga game take yi a wayarta a falo, mu kuma muna uwar daki. Ta ce "Kawo kunnenki ki ji". Da rawar jiki na mika mata, ai kuwa ta gantsara mini cizo. Na saki kara a ki'dime. Ita kuma ta ci magani tana fa'din "Maganin mai son jin almarin da bai shafe shi ba, maganin mai son jin abin da Allah ya sakaye shi, maganin mai son ya ji sirrin da Annabi ya tsine wa mai bayyana shi". Ai kuwa na fara hawaye ina shesshe ka. Nan da nan ta hau shafa kafa'data tana fa'din "Yi ha'kuri mana Yabina a hankali fa na yi miki, menene zaki zubar da hawayenki?" Na zum'bura baki ina fa'din "Mun bata gaskiya! Kuma dan kin zama babba ce ai dai kinsan fa'da na." Ta yi murmushi ta ce "Ni ban girma ba." Muka yi dariya gaba'daya. Sai lokacin wacce na bari a gida da k'unshi, ta biyo ni, akan na yi mata kitso. Muka fara, yayin da Ikilima ta hau wanke wanke ita kuma Nazira ta hau gyara wajen da muka yi dabdala. Da zan taho ta hado ni da kayan kwalliya masu yawa har Ina fa'din ta kwashe mini kayan ai. Da sabuwar doguwar riga da ko sata bata yi ba, da sabon takalmi. Na kalleta na ce "Ki rage kayan sun yi yawa Adda Nazi". Ta ce "Idan ina da fiye da hakan baki zan yi Yabi". Na jijjiga kai na kasa cewa komai na yi gaba na bar Iki tana dauko mini. Muna tafe ni da Iklima muna hirarmu na ce "Idan kin gaji dai, ki bani na karbi kayan." Ta ce "zan iya Adda Yabi". Muna tafe wani Alhaji sai binmu yake a hankali a cikin dankareriyar motarsa. Duk hon dinsa ban yarda mun tsaya ba. Har muka je gida, bai fasa ba. Muka shige gida, ya yi parking. Dai-dai lokacin Bulkachuwa ya danno kai. Na shige na bar Iki tana lekensa. Ba wani jima wa ta shigo da sauri tana fa'din "Adda Yabi wai ke ya biyo. Yaya Bulkachuwa ya fa'da masa babu maganar wani a kanki, ya bashi ku'di, ya kuma aiko shi wajen ki". Tana rufe baki sai ko ya shigo, daga tsaye ya gaida Gwaggo da Inna yana fa'din "Asiya Toro zo mana". Na yi kamar bazan kula shi ba, sai da Gwaggo ta ce "Yabi wai Yayanki ba magana yake yi miki ba ne? Ni fa bana son wannan wula'kancin na ki". Na mike ina fa'din "Shi ai Tijjani kayan haushinsa yawa ne da shi." Ya yi dariya ya ce "Ashe duk yadda na yi ba'kin jini a wajen Jabir akan ki ban wanke laifina na baya ba?" Muka dan fita wajen k'ofa. Ya sassauta ya ce "Kin ga Àllah ya dubi takaicin da aka cusa miki Asiya Toro! Kin zargo babban kifi. Wannan mutumin son ki yake yi da aure, kwamshinan harkokin addini ne na jahar nan, sannan babban dan kasuwa ne. Mutumin kirki ne, kin ga abin da ya ba ni". Ya nuna mini rafar dubu guda. Na zaro ido na ce "Billahillazi dan yankan kai ne Tijjani! Ban da hakan daga haduwa ya baka dubu dari?" Ya yi dariya ya ce "Kin san istigifari nawa na yi yau kuwa? Na yi yafi dubu goma, Ubangiji kuwa ya yi al'kawarin warware mana komai matu'kar muka dimanci istigifari har da bude kofofin arziki. Bana haufi Ubangiji ne ya turo mini arziki ta hannunsa. Ki yiwa kanki fa'da Asiya kin ga dai ba shiri muke yi da ke ba, amma na fi jin ciwon abin da aka yi miki sama da wanda aka yi mini. Ki saurare shi, ki yi addu'ar zabin Allah. Idan kin samu nutsuwa ki ba shi dama azo a yi auren ki ko kya samu sau'kin masifar gidan nan. Nima kin ga wannan ku'din ajiye wa zan yi wani satin zan bayar akai mini ku'din aure, ko wannan yar'uwar ta ki zata shafa mini lafiya". Na sauya fuska na ce "Nasiba fa bata da laifi Tijjani". Ya kwabe fuska ya ce "To ai ni kuma ko ita ce ka'dai ta rage a duniyar nan na haramta wa kaina ita. Bulkachuwa bai yi wannan arahar ba, ba za'a ci mutuncinsa, a tozarta shi kuma ya lik'e ba". Ya mik'o mini dalleliyar waya a kwalinta ya ce "Da caji da kuma layi a ciki ki kunna zai kira ki." Ya hade hannu alamun rarrashi ya ce pls ki saurare shi ko za'a dace". Na ce "Baba fa ya hana ni rike waya, yanzu haka akwai sabbin wayoyina a ajiye, da wacce Yaya J ya siyo mini, da ta wajen Abdulrashid har biyu. Wai sai na kammala makaranta, ko idan na yi aure na ri'ke". Ya ce "Wannan dai kin ga Babban mutum ne Yabi, ga shi kowa ya yi masa shaidar nagarta. Ki boye ta ba sai an ga ni ba, bana son ya kubuce miki. Bauchi zai kai ki, ba zai ajiye ki anan ba, ko ma Abuja. Babbar waya ce ki yiwa Allah kada ki bari ta salwanta". Ya juya na bi shi da ido ina raya ina ma yadda ake zuba masa kyakkawar sura kuma cikakkiya haka yake da kyakkawar dabi'a da nagarta. Inda a ce shine yake da dabiun Yaya J da ya zama komai an hada masa. Mafi yawan lokacin ina yawan ayyana da Yaya J ne yake ingarma kaman Bulkachuwa da an yi namiji tsayayye mai kyakkawar manufa. Amma halayyar Bulkachuwa shine nak'asunsa, mussaman na yadda yake iya keta alfarmar shari'a yana aikata kaba'ira, ga rashin ta ido, ga shigar iyashege, yau har barima na ga ni makale a kunnensa, gashin kai ya sha tiri (dying) gashinsa mai kyau ne irin na fulanin Bulkachuwa amma ya mayar da shi cibiri cibiri tsabar fitina da son yaudare y'anmatan da ba susan ciwon kansu ba, ga kafiya akan ra'ayinsa, ko k'uda ya shafa masa lafiya wajen naci.
Chapter 27 · 0% Book details