Sashe 52
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *OK NA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* *** Bai dawo ba, sai da ya sallaci Isha. A falo ya tarar da ni, na yi wanka na zira doguwar riga cotton mai zuwa da mayafi babba. Na shafa turaren oudi(concentrate). Ya kalle ni ya ce "Ranki ya da'de Asiyata". Na galla masa harara na ce "Ba taka ba ce". Ya murmusa ya ce "Ta Ummi ce shikenan?" Na yi shiru domin so nake na fa'da masa abin da zai bak'anta masa rai. Amma tunda ya saki maganar bari na k'yale shi sai idan ya sake katobarar cewa ni tasa ce zan tabbatar masa ba tasa ba ce, ba kuma zan zama tasan ba. Ya ajiye ledar hannunsa ya fita. Sai gashi ya dawo da kananun bowls da kuma fork biyu. Ya zauna kusa da ni. Ya bude ledar kamshin hadadden balangu ta buge ni. Ya juyo mini dauri guda ya turo mini gabana. Tare da robar yogurt madaidaiciya mai sanyi, da kuma robar ruwa shima mai sanyi. Sannan ya juyo nasa daurin. A hankali ya ce "Bismillah Amarya". Ban kula shi ba. Na gama yaukina na dauka na fara ci. Sosai naman ya yi mini da'di, sannan kuma mai laushi ne. Na cinye tas na bu'de yogurt na fara sha. Rabona da abinci tun karyawar safe. Duk da an kawo mini daga gida amma ban iya ci ba. Ganin na cinye yasa ya turo mini nasa ya ce "Kara Asiya". Na yi kamar ban ji ba. A sanyaye ya ce "Ba kyau a yi magana mutum ya yi kamar bai ji ba". Nan ma tamkar ba na wajen. Ya yi k'wafa alamun ya k'ulu. Ganin hakan ya sanya na tashi na bar shi na yi dakina ko kwanon da na ci ban kawar ba, bare na kawar da nasa. Ina shiga kuma na sanyawa dakin sakata. Na cire mayafin rigar na haye gado na yi kwanciya ta. Tunda na kwanta ban farka ba, sai da asuba shima kwakwasa mini kofa ya yi. Kafin na fito tuni ya bu'de gida ya wuce masallaci. Yau kam har na gama barcina na tashi k'arfe goma. Da na bu'de kofa na fito a zaune na same shi akan barandar. Babu alamun gaggawa a tare da shi. Yana ganina ya mike da sauri yana fa'din "Bari na janyo miki, na roba da sanyi, na rijiyar kuwa dumi ne da shi. Ya bu'de bandaki ya dauko botiki ta nufi rijiyar. Na bishi da kallo. Mamaki nake yi dama Tijjani zai iya yin laushi haka? Duk wula'kancin da nake yi ba ya fasa yi mini hidima. Na sake bin kayan jikinsa da kallo. Alamu sun nuna ya yi wanka. Sabon yadi ne a jikinsa amma ba alamun karin guga. Na tabbatar yadda tela ya ba shi hakan ya saka su. Na ja tsaki sosai. Dai-dai lokacin kuma ya zo daf da ni. Ya ce "Asiya Toro wata rana za'a wayi gari a ga kin zama tsaka fa". Ban kula shi ba, bare na tanka ya samu sanadin da zai jani da surutu. Ya wuce ya kai mini bayin. Na shiga na yi wankana na fito. Yauma atamfa na dauko koriya Shar. Doguwar riga ce da ta manne a jikina. Na gyara sosai. Na gyara d'akin, na zauna. Ya yi sallamah na amsa a dole. Ya ce "Na shigo?" Na ja tsaki, na kame bakina na tsuke. Jim ka'dan ya shigo. Na daga kai na kalle shi. Fuska a daure na ce "Na baka izinin shigowa ne?" Da walwala ya ce "Tunda baki zabura kin ce kada ka shigo mini ba, ai nasan kin kammala adana yan kananun abubuwan da kike yi mini k'yashin ganinsu". Ba'kin ciki ya turnike ni. Na murguda baki na ce "A a kiyasai ne k'arewar kankantar". Ya zauna bakin gado ya ce "Ban da samun guri irin na ki Asiya. Ta ya ya zaki dinga rufe mini kofa, kina hayewa gadon da ba'a siya miki ba sai saboda ni, ni kuma ki bar ni da kwanan kasa. Kwana nake yi ina artabu da sauro. Amma ke babu ruwan ki, ba kya gudun maleriya ta yi mini illah?". Na ki kula shi, bansan me yasa yake bani haushi ba, baya burge ni ko ka'dan. Ya sake yin k'asa da murya ya ce "Ki yi kokarin kyautata lahirarki Asiya. Babu ruwan alkalami da cewar ba kya sona. Matu'kar ina kwana da ba'kin ciki ki sani kina cikin fishin Ubangiji". Na rasa me zance masa domin dai ya sako wanda ban isa na fa'di bak'ar magana a kansa ba. Kan tilas na share ban ce komai ba. Ya tashi tsaye ya ce ki taso ki karya ga abin kari can a falo. Bauchi zan je. In sha Allah ba zan wuce la'asar ba. Za'a kawo miki abinci da rana. Ki shirya gobe zaki fara yin girki". Sai lokacin na fashe takaicinsa da cewa "Ba zan yi ba. Har abada ba zan dora tukunya saboda kai ba". Babu damuwa a tare da shi ya ce "Babu laifi. Lokaci zai fayyace komai ai". Ya juya ya tafi bai sake cewa komai ba. Har shad'aya ina daki ban fita falon ba. Sai da cikina ya tsananta yi mini kartan yunwa. A dole na fita. Na tarar da waina a karamin flask. Sai kunu a jug. Daga dukkan alamu siyowa ya yi. Kan dole na zauna na karya. Ina zaune har aka fara kiran sallar azahar. Na idar kenan sai ga almajiri yana kwankwaso kofar shigowa wajena. Da yake ni ce a farko su kuma su Mama na can ciki. Bamu ha'da komai ba, sai kofar shigowa gidan. Da sauri na fita na bu'de masa. Ya mik'o mini flask din abinci babba mai kyau. Wai wani ne ya bashi ya kawo wannan kofar. Na kar'ba ba tare da na ce komai ba. Na sani abincin da ya ce za'a kawo mini ne. Sai da na zauna a falo na bude na ga alalan gwangwani ya ji manja. Da alamun kifi a ciki. Na ji wani iri a dalilin yunwa nake ji ba ka'dan ba. Ni kuma bana iya cin alala na koshi. Tabbas an gyara shi ne dan a burge ni. Na rufe, ina sake jin yunwa na taso mini gadan gadan. Na yi shiru ina nazari. Sai na ji wayata na k'ara. Ina dubawa na ga Tijjani ne domin ina da lambarsa tun lokacin kwamshina da muka fara dan gaisawa. Na ki amsawa har ta katse. Ya sake kira ban dauka ba. Bai fasa ba, sai a karo na hudu na dauka a fusace na kan ga a kunnena, bayan na danna alamar amsa wa. "Yaro ya kawo miki abinci?" "Eh". Na fa'da a gajarce. Ya ce "kin ci na safen kuwa?" "Wai ni kam jinjira ce ne da zaka dinga mini tambaya tamkar kankanuwar yarinya? Idan ma ban ci ba ai cikina ne ko? Tunda baka shawarce ni akan abinda zan ci ba, ka ajiye mini wanda ya yi maka". Ya nisa ya ce "Asiya Toro kenan! Cikin kuka na ce "Komai zaka ce Allah na ganinka ai". A sanyaye ya ce "Kukan na menene Asiya?" Na sake tsananta kukan na ce "Akan me za'a kawo mini alala? Ni bana ci". Ya tausasa murya ya ce"Alalan gwangwani ne, saboda ke har kwai da kifi aka saka a ciki. Daga gidan abokina Abdul aka kawo miki fa, kema kuma kinsan matarsa mai tsabta ce". Da kukan na ce "To ni ina ruwana, ni dai ba zan ci ba, kuma yunwa nake ji tunda kunun ma ban iya sha ba, ya riga ya yi sanyi k'arara." Ya diririce ya ce "Ki yi ha'kuri bari na sa a kai wa Ummi macaroni da kayan miya sai ta daho miki yanzu. Hakan ya yi miki?" Na yi shiru. Ina harara tamkar yana wajen. Ya sassauta ya ce "Please mana Asiya ki ce to". A shak'e na ce "Yanzu d'aya da rabi. Idan ya wuce uku da rabi bazan ci ba, gara yunwar ta kashe ni". Ya dinga fa'din"Na gode sosai, bari na saka a kai mata yanzu. In sha Allah ba zai wuce hakan ba." Ya katse wayar. Na ri'ke wayar, haka kawai sai na tsinci kaina da mamakin yadda Tijjani yake rawar jiki a kaina. Gashi tunda na zo ban ta'ba yi masa wani alheri ko da ta magana mai da'di ba ce. Yadda ya lank'awasa harshe yana rarrashi tabbas yana yi ne tunda ga kasan zuciyarsa. Na fara gasgata sona yake yi ba sha'awa ba. Mintina biyar a tsakani ya sake kira. Na dauka bayan ta kusa tsinkewa. Da sauri ya ce "An tafi kai mata. Na ja mata kunne, na ce ta bar komai ta girka miki, tunda Nina sanya ta. Biyu da rabi zan aika a karbo mini. Dan haka zuwa uku za'a kawo miki in Allah ya yarda". Na yi shiru. Ya numfasa ya ce "Asiya ba ki ce komai ba". "A hankali na ce "Ina ji ai" Ya yi kasa da murya ya ce "Me zan taho miki da shi?" "Bana bu'katar komai na ka". A sanyaye ya ce "Shikenan, amma na siyo miki abin da nasan zaki yi murna". Na kyabe baki tare da fa'din "Hmm to ya yi". "Baki ce na dawo lafiya". A gajiye na ce "Tijjani ni na aike ka ne? Ka dame ni, in ta nine ma kada ka dawo". Kada na dawo Asiya? Saboda ke na yi tafiyar fa! Amma idan na dawo zaki ga ni". Ban bashi amsa ba na kashe wayata. Na ajiye ina jin wani irin abu da bansan menene ba yana mamayata. Uku saura na ji ana buga k'ofar. Na zari hijabi na nufi k'ofar. Yaro ne ri'ke da madaidaicin flash. "Gashi in ji wani a waje". Ya fa'da a hanzarce da alamu