← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 146

Sashe 56

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dinta". Na share shi, na shiga falo na dauko naman da ban ci ba a fridge. Na duba na ga ya cire albasar ciki. Na nufi kicin din. Na zuba mai a tukunya. Na zuba albasa. Na jere komai na bu'kata a gabana. Na kalli gas din da yake tsaye sabo dal da shi. Na fara tunanin yadda zan kunna tunda zancen gaskiya ban ta'ba kunnawa ba. Bamu taba amfani da shi a gidanmu ba. Na yi shahadar murda wa sannan na fara kokarin kyasta ashana. Sau biyu ashanar tana karyewa saboda rashin k'warinta. A karo na uku ta k'yastu, na nufi bakin gas din da ita. Ai kuwa gas ya yi wani irin but da karfin gaske! Na furgita, na tsora ainun, na mike na dinga karo da fatali da kayan da na jere a gabana na yi waje a guje cikin ki'dima mai yawa. Ya fito a band'aki ke nan, ya gan ni a guje na yi dakina. Ya biyo ni da sauri. Fa'di yake "mene ne, mene ne?" Ya zuba mini ido yana kallon yadda jikina yake kyarma irin na tsoro sosai. Da sigar salama ya ce "Asiya! Nutsu ki fa'da mini. Mene ne ya ki'dima ki haka?" Ganin na kasa magana ya tashi ya nufi kicin din. Ya tsaya a bakin k'ofar yaga yadda ruwa ya jiqa kasan kicin din. Komai a wancakale tabbacin ta kansu ta bi. Ga gas kuma yana ta yi fahh. Ya rage karfinsa. Sannan ya dora sanwar. Domin ya saba girki tun yana makaranta. Ya gyra wajen. Bai bar kicin din ba sai da ya tsaida ruwan girkin tunda ya ga taliya ta yi niyyar dafawa. Ya koma ya zauna kusa da ita a bakin gadon. Zuwa lokacin ta dan shiga nutsuwar ta. Ya sassauta ya ce"Asiya wai mene ne? Kadangare kika ga ni ko tsaka?" Na zum'bura baki na ce "Wutar abin nan ne ta yo kaina gaba'daya". Ya kwashe da dariya sosai. Hakan kuma ba karamin kular da ni ya yi ba. Cikin bacin rai na ce "Yi dariyar ka son ran ka Tijjani, ai ko k'onewa na yi baka da asara tunda ba sanin darajata ka yi ba". Na fara hawaye. Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Nan da nan ya gintse dariyar da yake yi. Ya ce "Very sorry Asiya Toro. Abin ne ya bani dariya yadda kike yar gayu kuma wayayyiya amma gas ya yi miki wula'kanci irin haka?". Sai kawai ya sake tintsire wa da dariyar da ta fi ta farko k'arfi. Ba'kin ciki har mak'oshina nake jinsa. Na rasa me zan yi na sanya takaici akan zuciya da fuskarsa. Kafin na yi magana ya yunkura ya tashi a dalilin kamshin da ya fara cika hancinmu wanda alamu ne na ya tafaso. Bai dawo dakin ba, sai da girkin ya kammala. Ya dawo da plate biyu a hannunsa. Ya dire a k'asa, ya sake fita. Kaamshin girkin ya cika d'akin, hakan ya sake sabunta mini yunwar da nake ji. Ya dawo dauke da pure water da lemo akan tire. Hannunsa kuma da fork guda biyu. Ya zauna ya ja plate daya gabansa ya bu'de murya ya ce "Bismillah Amarya". Na bata rai na ce " Asiya Toro dai. Ina na kai darajar amarya bayan ni din yarinya ce kwaila kuma kankanuwa". Ya murmusa ya ce "Oh wai maganar ciwo ta yi miki ne? Tsakani da Allah ba gaskiya na fa'da ba? " Na girgiza kai ba tare da na kula shi ba. Na sauko na ja abincin da yake jirana. Na kai bakina duk kushena ban isa na ce ga inda girkin yake da tasgado ba. Na dinga zura loma. Sai da ya ga na kusa cinyewa ya kaikaice ya ce "Asiya Toro iyashegen ki yawa gare shi. Jibi yadda kike zabga loma kina zare ido. Me ya janye tunanin zan zuba miki wani abu a ciki Kuma? Kunya ta kamani ka'dan. Amma na daure na yi kamar ban ji komai ba. Na share shi. Sai da na gama na yi gyatsa, na kalle shi na ce "Na tabbatar da Yaya J ne ya dafa abincin nan, zubowa zai yi a waje daya. Sannan ya manta cikinsa har sai ya tabbatar nawa cikin ya cika." Na saci kallonsa na ga har wata zufa ce ta karyo masa. Zuciyata ta fara harbawa da tunanin hukuncin da zai yi a dalilin yadda yanayinsa ya nuna maganar ta buge shi. Ga mamakina sai kawai ya yi yak'e ya ce "Ba ki yi karya ba Asiya! Domin jiya mun je gidansa ni da Salisu a dalilin an sace mashin dinsa. A gabanmu ni da Salisu yake tarairayar Maijidda akan ta daure ta ci ayaba. Kinsan cikinta ya tsufa ba komai take iya ci ba. Ai Jabir kam yana mutuntunta maganar tsohonsa akan Maijidda. Sosai yake sonta yake tattalinta. Har mamaki na dinga yi tare da shakkun idan har ya taba son wata mace kafin ita. Ita ma bata jin kunyar mu din yayunta ba ne sai tabara take yi masa son ranta. Take na gano mata irinsu ba zasu ta'ba barin mijinsu ya yi tunanin wata macen ba. Wanda duk ya samu irinsu ya gama morewa, ga cikar halitta ga shagaba ga kuma biyayyar iyaye da aure. Wanda bai samu irinsu ba ai zai dauwama cikin cizon yatsa ne. Sannan tagomashin biyayyar da suka yiwa iyayensu ya sanya gidansu ya zama gidan farin ciki." Maimakon na b'ata masa rai, sai ya zamana nawa ran ne yafi b'aci. Bayan kod'a Maijidda da ya dinga yi, tare da kwarzanta ta, sai na fahimci yarfe yake yi mini akan ban yiwa nawa tsohon biyayya na mutuntata aurena ba. Na yi shiru na kasa cewa uffan. Ya gaji da jiran kalamina, ya tokara ya tashi. Bai dauke kwanon da ya ci ba, bare ya ha'da da nawa. Ya bar gidan ba tare da ya yi mini sallama kamar yadda ya saba ba. Tun da ya fita bai dawo ba, sai bayan sallar isha. Ga mamakina sai na ji haushin hakan. Rashin dawowar tasa ta mintsinin zuciyata sai dai ban bari ta bayyana akan fuskata ba. Ya leko ni, ina zaune a daki. Bai shigo sosai ba. Ya ajiye mini leda ya juya bayan ya ce "Sai da safe". Bansan ya aka yi ba kuka ya k'wace mini. Ni da kaina ban san dalilin kukan ba. Amma so na yi ya shigo yana lallaba ni, da ro'kon na ci abin da ya siyo, ina botsare masa. Ko duba ledar ban yi ba, na yi kwanciyata bayan na rufe k'ofar dakin. Cikin dare na tashi da wata azababbiyar yunwa. A gigice na janyo ledar na hau cin awara irin manyan nan ga kabeji. Da k'yar na iya janyo leda a lungun gado. Maman kawata Shafa'atu ce ta je Kano ta siyo yajin Annur food mai dan karen dad'i. Shine ta ba ni roba d'aya. *Annur food Delicious* *Ba iya yaji ba har da garin danwake da man Shani, da yajin daddawa* *Tuntube su a wannan lambar dan k'arin bayani 08039183880*. Na sani sadda ya kawo da zafinta. Sai da na cinye tas, sannan jikina ya daina rawar yunwa. Take na tuno ashe jiya iya taliyar nan kawai na sanya a bakina. Na jima barci bai dauke ni ba. Sai kawai na yanke shawarar na doro alwallah na yi nafilah. Na mike ina da tabbacin Gwaggo na kan sallayarta a irin wannan lokacin da bayi suke barci. A hankali na zare sakatar na fita. Abin mamaki sai na ga Tijjani akan barandar yana sallah. Yana sujjada. Na dakata ya idar tunda ba zai yiwu na wuce ta gabansa ba. Na jingina da kyauren kofar dakin nawa. Ina kallon yadda ya kyautata sujjadar. Tsawon lokaci bai dago ba. Wani abu ya sake tsirga mini a kansa. Na tuna a duk sadda Gwaggo ta tashe ni cikin dare dan mu yi nafila. Cewa take yi daure ki tashi ki nemi yardar Ubangiji Yabi. Irin wanna lokacin sai zababbun bayi ne suke rabauta da yin ibada. Duk kuma abin da mai yin ibadar dare yasa a gaba sai ya ga sau'kinsa. Allah da kansa yake saukowa sararin subhana yana shelar ina mai bu'kata na biya masa?" Zuciyata ta sake harbawa domin ni kaina da bana son Tijjani. Kallonsa yana sujjadar nan sai da na ji wani irin abu, to ina kuma Ubangijin da ya kyautata sujjadar saboda shi. Har lokacin kuma bai dago ba. Na sake tuna jawabin Gwaggo da take fadin kada ki ce sai kina cikin damuwa ko bu'kata zaki yi sallar dare. Domin idan ta zame miki dabi'a, to lah shakka duk wata bak'ar k'addara da zata zo miki, sai ta zo da sau'ki, sannan komai kika roka zaki ga biyan bu'kata duk nisan jinkiri. Ban da ma dai dan adam mai shagala ne, ai ya kamata ace yana yawan yin godiya ga Ubangiji bisa dinbin niimomin da ya masa. An yika musulmi, an baka lafiya, an kuma hore maka abin da zaka ci komin kankantar sa. Ashe kuwa ba sai da damuwa za'a yi ibada ba. Na nisa ina jin na fara gajiya da dakonsa. Har zan koma daki sai kuma ya d'ago. Na dinka fatan ace sujjadar karshe ce ba zai koma wata ba. Ai kuwa sai na ga ya zauna, alamun attahiyatu yake yi. Ina ganin ya sallame na yi maza na wuce a dalilin fitsari ya kama ni ba ka'dan ba. Yana zaune har na fito na shige shi. Sai dai Ina wuce wa ya sake mikewa tabbacin dama ya jinkirta mini ne na wuce. Raka'a biyu na yi mai dauke da gajerun surori. Na yi yan adduoina. Ban san me yasa na kasa addu'ar da nake nacin yi ba. Na Ubangiji ya tarwatsa aurenmu. Na tsinci bakina da fa'din Àllah ka mini zabin da zai fi mini alheri. Karon farko da na yi addu'ar da dukkan zuciyata. Na yi addu'oi, na yiwa mahaifana addu'a, na ha'da da al'ummar ma'aiki. Na koma na kwanta ina fa'din "da wanda yayi doguwar sujjada, da wacce ta yi gajeriya, Allah dai ake yiwa, to Ubangiji ka karba mana gaba'daya".
Chapter 56 · 0% Book details