← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 146

Sashe 47

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

mussaman akan lamarin ki". A hanzarce na ce "Ai kuwa dai ba zaka ga ranar ba". Ya girgiza kai tare da ce wa "Babu damuwa time will tell". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ina son na tambaye ki, zaki iya zama a wanccan daya bangaren na Dada?" Maimakon na yi masa magana da baki, ai sai kawai na d'ora hannu aka na fashe da wani irin kuka na tashin hankali. Murya na rawa na ce "wato dai a cikin masifar gidan nan zan tabbata? Idan kuwa har a cikin gidan nan ake nufin na zauna da sunan zaman aure Allah ya dauki raina kafin hakan ya tabbata. Na shiga uku ni Yabi". Ya rikice ya hau fa'din yi shirun ki dama na fa'da mata wajen ya miki local da yawa, sannan baki samu sauyin muhalli ba. Yau din nan duk inda gida yake zan nemo kafin dare. Da ku'di a hannuna. Yi hakuri ki daina irin wannan kukan. Kin ga yadda kika koma kuwa Asiya?" Da k'yar ya lallaba ni, na yi shiru. Ya zura hannunsa a aljihu ya ciro cakulet manya masu da'di da tsada k'waya biyu ya mik'o mini. Bansan ya aka yi ba na fashe da dariya ga kuma hawayen ba'kin ciki na ziraro mini. Da yake d'an duniya ne sai kawai shima ya fashe da dariyar yana cewa "Ni nasan Ubangiji zai cusa miki soyayyata dan yasan yadda ya gina ki a tawa zuciyar. " Da k'yar na samu dariyar ta tsaya. Da hawaye a idona na ce "me zan yi da wannan abar?" Ya zuba mini ido yana wani lumshe su ya ce "Wai fa dan kada na zo hannu na dukan cinya ya sanya na taho miki da su" Na rasa me zance masa tsabar takaicinsa da ya d'ada makure ni. Na ce "To ajiye idan ka ga Yarinya k'arama ka bata amma ba ni ba". Ya waske ya ce "Asiya Toro maraina ka'dan fa barawo ne. Kowa ba iya karfinsa zai yi kyauta ba? Kin san wahalar da na sha kafin na samo miki wannan cakulet din a garin nan? Saboda nasan kina son ta ne. Amma ban burge ki ba? Idan kin yi hakuri wataran katon zan siyo na ajiye miki." Da sauri na ce "da dai ace ba hannun jinjirai ne da kai ba tsabar rowa." Ya nuna kansa da yatsansa ya ce "Ni ne mai hannun jarirai? Lallai kuwa zan baki mamaki Asiya Toro local government. Bauchi state of Nigeria". Ko kula shi ban yi ba na wuce shi na tafi na bar shi a tsaye. Tsabar takaicinsa da ya sake kular da ni. Ya d'aga murya ya ce "Sai gobe zan dawo, ko da anjima ma na dawo?" Da kansa ya bawa kansa amsa da ce wa "To zan dawo da daddaren ran ki ya da'de." Har na isa k'ofarmu mamakin Bulkachuwa kawai nake yi. Ban da dai ya riga ya same ni a araha ya rasa me zai kawo mini sai cakulet k'waya biyu. Shi ko kunya bai ji ba? Amma da na tuna halin rowarsa sai kawai na janye mamakinsa. Na shiga tambayar kaina wanne irin zama zamu yi ne da shi? Na tabbatar sassaucin da ya yi dan baya son na yarfa shi ne. Amma da tuni ya baje mini kalolin rashin mutuncinsa. Na zauna na fara kokarin cigaba da k'ullin sigan. Zuciyata ta shiga hakaito mini kayan jikinsa. Shadda ce a jikin sa kalar ganye wato kore sosai. Ya d'ora hular sanyi mai tambarin kungiyar Manchester United. Na sani kuma d'an ya boye wa Baba curarriyar sumarsa ne tunda zafi ake yi ba sanyi ba. Daga ni tun farar safiya ya sanya kayan a hakan kuma shi ya k'ure malejin kwalliya ne. Na ja tsaki tare da ce wa "Idona ya saba ganin samari ma'abota wanka da gayu. Irinsu Yaya J da Nuru Tanim. Ta ya ya Bulkachuwa zai burge ni?." Gwaggo ta shigo ta ce "me ya faru da kika je?" Na yi kasa da kai na ce "Ba Dada ba ce ashe". Ta ce "To waye?" Na bata rai duk da kan nawa yana kasa na ce "Tijjani ne". Daga hakan bata kara ce wa komai ba ta dauki abin da zata dauka ta fice tsakar gida. Washa gari da azahar ina kwance a tsakar daki sai ga Nazira ta zo. Karon farko da ta zo gida tunda aka yi mata aure. Duk rud'anin da nake ciki sai da na tashi da azama na rungume ta. Muka haye k'aramin gadon Gwaggo da muke kwana a kansa ni da ita tun fil'azal. Da murmushi a fukskata na ce "Yau Adda Nazira ce a gidanmu?" Ta d'aka mini duka tare da cewa"oh har kin cire ni a cikinsa, to kema kwana nawa ya rage miki mu yi kunnen doki?" Na bata fuska sosai. Ta ce "daga wajen Dada nake suna can, suna artabu da Yaya Bulkachuwa akan inda zaku zauna. Wai akan me zai je ya kama haya tamkar ba shi da kowa a Toro? Shi kuma ya kafe ba zai zauna a cikin gidan nan ba.". Na bata rai na ce "Ai Wallahi na fa'da masa indai ya yarda da tsarinsu to kuwa sai dai a tsine mini dan bazan zauna a gidan nan ba'kin ciki ya karasa ni tun ajalina bai zo ba" Adda Nazira ta ce "Haba ashe tirjiya ya samu daga gare ki, kin ga yadda ya fitittike akan ba zai zauna a wajen ba? Dada har da kukanta wai sai da ya bari su Baban Tsakiya sun gama gyara masa wajen sannan ya ce zai fita ya kama haya tamkar wanda bashi da galihu a Toro? Shi kuma kinsan shi ya ce "Salisu da yake hayar rashin galihu ne ke nan? Ashe ashe Gimbiya Yabi ce ta saka ya rikice ya turje. Ya kama miki gida mai kyau a bayan sakatariya. Ba ki ga gidan ba. Yanzu muka dawo a mashin dinsa ya goye ni muka je ya nuna mini gidan. Ni Wlh har na ji na daina k'insa. Kin ga rawar jikin da yake yi. Sai fa'di yake ya kika ga wajen Nazira? Nasan idan ya burge ki to zai burge kanwar ta ki ma. Gaskiya Yabi ke d'in mai sa'a ce. Gaba'daya kin rikita namiji irin Yaya Bulkachuwa. Murna nake yi, da dukkan zuciyata nake jin addu'armu ta karbu. Da ikon Ubangiji sai kowa ya yi mamakin alherin da zai biyo bayan wannan auren." Na tab'e baki na ce "Hmm ai ni dai an cuce ni kawai. D'azu muna maganar k'awayen amarya. Na ce masa ba ni da k'awaye, ke ce to kuma kin yi aure. Yana bu'de baki da yake shi d'in bunsuru ne sai ce wa ya yi wai ina k'awata fara mai dan jiki. Kin san wa yake nufi?" Kafin ta ce komai na zarce da ce wa "Shafa'atu yake nufi fa. Har ya k'yalla ya ga halittu a tare da ita shine zai silala me za'a yi da Tijjani ne. Na fa'da cikin kunan rai. Ga mamakina sai ganin Nazira na yi ta k'yal-k'yale da dariya sosai. Sannan ta ce da wuri haka Yabi?" Na bata rai na ce 'ban gane ba?" Ai kuwa cikin ido ta ce" tun yanzu kin fara kishin Yaya Bulkachuwa ina kuma idan kin shiga hannunsa?" Hawaye ya b'alle mini ina ce wa "Allah ya sauwake, ashe ba ki fahimce ni ba Adda Nazira?"
Chapter 47 · 0% Book details