Sashe 49
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki* *Maganin sanyi* *Saiwowin Tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza* *Saiwowin dahuwar tattabaru* *Gumba* *Tsumin kwakwa* *Y'aya'n gadali* *Hadadden daka*. *Tsugunno mai sa a matse* *Goran tula* *Goran tula syrup* *Garin goran tula*. *Maganin gyaran nono*. *Zuma ta mussaman*. *Tsumi*. *Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*. Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*. *Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntubi marubuciyar Halin yau dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa*. *08032773332* Hatta mamah da matan Baban Tsakiya da suka rakoni tare da ita sai da suka tsokane ta suna cewa "To ko dai ba zaki bar ta a dakinta bane kamar yadda aka yiwa kowa?" Duk da hakan kuma bai sa ta bar ni ba. Har sai da Aliyu ya dauko mata Bulkachuwa cikin abokansa da suke dakon a gama watsewa su rako shi. Yadda mahaifina ya damka mata ni a hannunta, bata saki hannuna ba duk tsawon lokacin nan. Ta kamo hannunsa ta ha'da da nawa ta damk'e cikin nata. Ta ce "gata nan ubanta ya bani amanarta na kawo maka ita da kaina saboda ya nuna mini ita ce tawa ba kai ba. Na karbi amanarta, ni kuma na baka amanarta. Ka dinga tuna dalilin ha'da wannan auren. Ka zama cikin mutane masu halarci da kuma sakanta alheri da alheri. Ban ta'ba farin ciki irin na yau ba. Ka sani na ha'diyi takaici da wahalolinka daban daban. Zan mance komai na yi alfahari da kai har ma na daga maka sawuna ka shiga aljannah idan Yabi ta kubuta daga tozarcinka da gangan. Ko bana raye idan ka kyautata mata tamkar ni ka yiwa. Albarka da farin-ciki zasu kewaye ka. Ka kula da tarbiyarta, kada ka bari ta bijire wa ka'idojin shari'a. Amma ka zama mai sasauci da kawaici domin dai yarinya ce y'ar k'arama. Ina fatan auren nan ya bud'a maka k'ofofin arziki da kuma fahimtar rayuwa daidai. Àllah ya shirye ka ya shirya maka iyali. Allah ya albarkaceku gaba'daya". Ta mik'e ta bar shi a durk'ushe yayin da nake kan gado, hannunmu kuma suna sark'e. Sai da na tabbatar ta yi nisa na fincike hannuna, na ja tsaki na koma gefe. Murya a dushe ya ce "Na yafe miki Asiyata! A gabanki Babah ta ce amanarki ta bani, na tausaya miki, na kuma yi miki sassauci." Na sake jan tsaki fiye da na farko. Ya mike ya fita bayan yan tsirarrun kawayena sun fara hayaniyar ba'a sayi baki ba dare na yi. D'aya ce ma k'awata a ciki ragowar hudun duk wanda suka zo daga Kangire ne wato cousin dina na dangin Gwaggo. Sai kuwa Ihisan k'anwarsa. Ita kuma a takure take a dalilin yayanta ne angon. Ba jima wa suka zo. Suka taba barkwancinsu, sannan aka yi nasiha da addu'a. Suka gwangwaje k'awaye da ku'din sallama mai auki. Sannan suka tafi da su. Ina ganin sun fita, shi kuma ya bisu da niyyar rakiya. Na tashi na rufe kofar dakina. Da ya dawo ba yadda bai yi dan na bu'de kofar ba na ki. Ta windo ya leko ya ce "Ga leda nan ki dauka ki ci nasan da yunwa a tare da ke". Washagari ina jin ya fita sallah na yi maza na fita na doro alwallah a bandaki, takaicina daya bandaki a tsakar gida yake ba a cikin daki kamar yadda na ci buri ba. A gurguje na kammala uzziri na koma na rufe dakina. Ina idar da sallah na yi kwanciya ta. Sai tara da kadan na bu'de k'ofar dakin, domin barci na yi mai nauyi. Ina bu'de wa kuwa ya shigo da sauri. Ya ce "Kin tashi? Sannu ya kwanan bakunta?" Uffan ban ce ba. Amma wani irin bakin ciki ne ya turnike ni. A dalilin rashin bandaki a cikin daki. Na hakaito kusan duk wadanda muka taso tare ko wacce band'akinta a dakinta ne. Na tuna gidan J da na Nura, hatta Nasiba band'akinta a dakinta ne sai ni ce na samu dakuna tamkar na Islamiya tunda na ga falon ma daban ne ba'a hade suke ba". Sai kawai na fashe da kuka mai sauti sosai. Ya diririce ya ce "Daga tashi sai kuka Asiya? Tun dazu fa nake zaman jiran ki tashi ki karya. Ina son na fita muyi sallama da abokaina zasu koma garuruwansu". Ban ce masa komai ba. Illah kukan da nake yi mai tsananin cin rai da nuna k'ololuwar ba'kin cikin da mai yinsa yake ciki. Ya dinga rarrashi yana Fa'din "Ki yi ha'kuri Asiya komai zai dai-daita, daure ki tashi ki yi wanka anjima ka'dan zaki fara yin baki, duk wadanda zasu tafi yau sai sun biyo sun gan ki. Ina ganin kafin Babah ta wuce Bulkachuwa ma sai ta zo, idan ta ganki a hakan kinsan ba zata ji da'di ba." Gaba'daya ya rikice ya ce wannan ya saki, ya ce wancan. Da kuka na ce "Ni ban ta'ba hasko zan shiga gida mai bandaki a waje ba. Gaskiya an cuce ni, an gama da ni. Na saka fashewa da kukan da yafi na farko tsanani. Hankalinsa ya tashi domin a ki'dime ya tattaro ni. Na zabura na k'wace ina sake jin taikacinsa tamkar na rufe shi da duka. Jikina har bari ya dauka domin lokacin ne karon na farko da jikin namiji ya rab'i jikina irin haka. Da muryar kuka na ce "kada ka kuma ta'ba ni. Bana son ka, bana ko son ganin ka". Ya rasa yadda zai yi da ni. Ya zauna a gefena cikin rashin abin yi. Tsawon lokaci ina shesshekar kuka. A hankali ya ce "Ko na samo miki katon baho sai ki yi wankan anan idan kin gama sai na dauke na gyara wajen". Yadda ya yi maganar sai na ji wani irin abu mai kama da tausayinsa yana neman kama ni. Na sassauta kukan nawa. Amma ban kula shi ba, bare na tanka masa. Ya sake lank'awasa harshe ya ce "Ki yi ha'kuri Asiya! A yanzu bani da halin irin gidan da kike mafarkin samu. Ban ta'ba jin takaicin ta'adin dukiyata da na dinga yi ba irin yau. Amma ina ro'kon arziki ki yi mini ha'kuri . Da ikon Allah zan yi aiki tukuru dan na cika miki burin ki. Na miki al'kawarin matu'kar rayuwata da taki ta kai lokacin da zan yi miki ginin da zai dace da ke, to ke zan bawa zabin yadda za'a fasalta ginin". Na ja tsaki na ce "Duk kana nufin ina nan tare da kai, ina kuma dakon ganin wasikar jaki irin taka?" Idonsa ya kad'a ya ce "Ni na sani Allah zai taimake ni, dan haka ba wasikar jaki nake yi ba". Na ja bakina na tsuke. Ya dinga magiya tamkar zai fashe da kuka akan na je na yi wanka. Da k'yar na yarda na tashi sai dai ban yarda na tube kayana akan idonsa ba. Sai da ya fita. Sannan na cire. Na dauko sabon zanina gyauto guda. Na daura na saka hijabi. Na bu'de akwatin da na shirya kayana a ciki. Na ciro soson wanka da sabulu da burush, hadi da makilin. Na ajiye tawul akan gadon. Na fito na tarar da shi zaune akan baranda duk jikinsa ya saki babu kuzari a tare da shi tamkar ba Bulkachuwa wanda baya barin ta kwana ba. Yana ganin na fito ya mik'e ya dauki botikin da yake gabansa cike da ruwa. Ya nufi band'akin. Na dakata ya fito, ya kalle ni ya ce "yanzu na janyo miki a rijiya da dumi tunda garin da zafi." Ta tafasa ban ce ba. Na shiga na turo kofar na sanya sakata. Ina wanka ina ayyana, ina ma a cikin daki bayin yake? Dan karami amma ko ina tayals ne. Na fahimci sabon gini ne mune muka fara zama a ciki. Sosai na yi wanka. Sai da na alwala da kuma brush sannan na fito. Na shiga daki na tarar da tsintsiya a hannunsa tabbacin shara ya yi mini. Ga gadon ya gyara tamkar gyaran mace. Daga kasa kuma kwanukan abinci ne. Ko kallonsa ban yi ba, bare na yaba masa ta hanyar cewa sannu ko na gode. Ya kalle ni ya ce "Bari na baki wuri ki shirya". Ya juya ya fice. A hankali nake shafa mai tamkar mai ciwo sannan na goga powder. Na shirya cikin sabuwar atamfa ta Buyers Batik. Doguwar riga ce amma dinkin ya yi kyau domin a Jos aka dinko mini. Gata shudiya ce sosai aka yi mata yarfen ja. Tsaya fa'din yadda farar fata ta haska atamfar bata lokaci ne. Na goga rol on din Nivea a raina sai tsaki nake yi ina fa'din da an bar ni da kwamishina ko Yaya Jabir da tuni roll on din oriflame zan dinga tu'amalli da shi dama sauran product dinsu gaba'daya. Tunda su zance a zubo mini a lefena. Na fesa turaren Far-away, na shafawa lebena jan baki mai jan duhu. Gefe na ajiye jan mayafi Wanda ya dace da atamafar. Da yake yanzu a hutar da mata bata lokaci wajen daura dankwali ana ta yin huluna. Nima hular aka yi mini. Ai kuwa na kafata a kaina na isa gaban madubi ina daidita zamanta. Ni da kaina na dinga fa'din "Fatabarakallahu ahsanul khalik'in. Sosai na yiwa kaina kyau. Maimakon na zauna sai na tsinci kaina da son yin walaha tunda na yi alwallah kafin na fito a band'akin. Na idar na tsaya ina kallon dakin. Madaidaici ne sannan kayan gadona suma matsakaita ne masu sau'kin ku'di. Amma sun yi kyau babu laifi. Labulayen sun fi komai dqukar hankalina, ledar tsakar dakin ma mai kyaun aka saka mini wacce za'a kwana biyu bata fatattake ba. Na bude akwatin na dauko wayata na kunna. Na koma bakin gadon na kishingida ina dakon ta gama daidaita. Ina cikin dube dube ya shigo shima tamkar alamara ya sanya shudiyar shadda irin shud'in atamfar jikina. Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Domin komin k'in da nake yi masa tun fil'azal nasan yana cikin yan ka'dan da Ubangiji ya yi masa kyaun fuska da kuma ciakken zati. Da walwala ya ce "Amarya kin sha kyau. Nan gaba fa idan zuciyoyinmu suka zama aminai ba karamin gidan farin ciki zamu gina ba. Tun yanzu zabin zuciyoyinmu