← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 146

Sashe 141

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Allah ya yi albarka, yasa kai ma ayi maka tagwaye." Ya ce "Ai tuni ya bani Dada. Wadannan da suke gittawa ta gabanki ba nawa ba ne? Ko kuwa dan a gidan Marina kowa d'an da ya haifa ne nasa shiyasa kike ganin sai na haifi wasu tagwayen?" Da yake babu wata shak'uwa a tsakaninsu, asalima tsoro tsoronsa take ji. A sanyaye ta ce "A a kuskure ne, da mantuwa Ali. Yanzu dai ba zamu yi fad'a ba, bayan ka zo mana da babban albishirin da babu irinsa. Allah ya saka da alheri, ya yi muku albarka gabad'aya". Ya ce "Ameen". Babah itama ta yi masa godiya da fatan alheri da bunk'asar arziki. Yabi tana bude baki ta ce "Na dad'e ina son na tura Baban Marina Umrah. Na dad'e ina fatan na yi masa ba zata. Ta ce zan tattara abin da nake da shi a yi tafiyar nan da shi". Idon ta ya ciko da k'walla tana ayyana yadda Baban 2 yake fatan ya kai ta Makkah. Ashe abin na ransa, ashe itace zata riga shi zuwa Sau'udiyya? Hawaye ya tsinke mata. Babah ma ta shiga taya ta. Aliyu ya ce "Maimakon ku yi masa addu'a sai kuma ku yi masa tukuicin kuka?". Cikin kuka sosai Dada ta ce "Kai ku yi kukanku da kyau kun ji ai! Ali ai dole mu yi kuka. Yau sama da shekara Shehu na garkame a haka aka samu rabon Asma'u. Kai rabon haihuwa zazzafa ne". Aliyu ya ce "Kai Dada da fitina kike. Me ya kawo wannan maganar a yanzu kuma? Sannan kuma Yaya Tijjani ne ya koma shehun ko kuwa?" Ta ce "Eh shi fa. Tunda ga y'aya'nsa na girma ai gara na tsayar masa da suna d'aya. To na zabi Alhaji Shehu kawai domin sha Allahu wataran zai zama Alhaji da ikon Ubangiji kuwa". Ya gintse dariyasa ya ce "Ni na tafi, tunda Yabi ta had'a ni da aikin dauko Baban Marina gobe". Sai lokacin na ce "Tare zamu je, zan duba yaron Adda Nazira da ya yi targade." Ya ce "Tom in sha Allah". Babah ta ce "To kuma ya zaka yi da wannan kilifar ne tunda bata isa yaye ba. Watanta uku kacal" Ya ce da ita zaku tafi mana". Dada ta ce "Allahu akabar! Yabi ta haifo Yabi." Ya kwashe da dariya ya ce "A a Dada. Ai Yabi wadda aka haifa a hanyar sau'udiyya dan aikin Hajj ne ko aka je da cikinta. Ita kuwa wannan ai an riga an haife ta, sannan Umrah zaku je ba tawwali ba". Ta ce Hakane, sai ace mata Ummara Husna. Domin na tabbatar sai ta yi jidalin Asiya idan ba'a ce mata Ummarah ba. Oh ashe dai da rabon burin Yabi na zama Hajiya a kusa zai tabbata. Nasan Shehu ya biya mini ne dan na kula da ita, na jagorance ta a wajen sa'ayi da safa da Marwa". Ta bawa Aliyu dariya ainun ya ce "A Ina zaki jagorance ta din? Ai ko ke yanzu kika je d'aya zaku zama, ko wanda ya je bara idan ya koma bana sai ya ga abubuwan da bai san da su ba. Saboda yadda gwamnatin Sau'udiyya ta mayar da hankalinta akan Makkah da Madina gabad'aya. Bare ke mai shekaru ashirin da biyar da zuwa, ina ce da kika je ma ba'a haifi Anas ba?" Ta rausayar da kai ta ce"Ko Yabi yayarsa ma ba'a haife ta ba. Kasan ana daf da aihuwata ta Alhaji ya hadu da sharrin masu zamba cikin aminci, aihuwarta ta zo cikin wani irin yanayi mai tsananin gaske ". Na hauro na ce "Dada kina son fad'an wannan labarin. Nasan idan tafiya ta mika zaki k'arasa abin da kuke fad'a cewar ni na kore masa arzikinsa". Ta kama baki da azama ta ce "Yabi ki yiwa darajar Alhaji da Asma'u kada ki birkice mini. Ko mahaukaci ya ji labarin ki da irin bajintar da kike yiwa uwa da uba ai yasan ke din arzika ce ba wai Yabi ba. Yo duk gidan Marina akwai wanda bai ci arzikinki ba ne? Babu shi Wallahi. Allahu ya huci zuciyar ki. Bazan sake ba. Kai Ali tashi ka yi tafiyar ka, nima alwallah zan yi na yi munajiti da Ubangiji. Kai ma ka yawaita zikirrn ambaton Ubangiji ko na istigifari, ko da kuwa tukin mota kake yi ". Ya yi dariya ya ce "Wato da Yaya Tijjani da Nasiba da Yabi sune maganin Dada." Na dauke kai na ce "Kada ka sani Yaya Aliyu! Baban 2 da Nasiba dai. Tun fil-azal sune zasu yi sa insa da ita ta yi mukus. Amma ni kam menene bata yi mini ba?" Ta yi shiru ya kasa ce wa komai. Sai Babah ce ta fanshe ta da ce wa "To marasa kunya ta yi din. Suma wadancan din waye su da zasu yi maganin uwarmu? Ai tunda aka yi sa'a tana tsananta ibada komai zai daidaita mata." Da haka aka bar maganar domin jikin Dada ya yi sanyi.
Chapter 141 · 0% Book details