← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 146

Sashe 140

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai washagari aka hak'ura da juyayyin rashin Bulkachuwa. Dada tun asuba ta yi wankan tafiya gano shi. Tana yi tana fad'in "Allah a saukakawa wannan yaro. A jibanci lamarinsa. Ya ci arzikin ma'aiki. Ya ci albarkacim Shehu mai karama". Da wuri ya kawo Iklima. Ya ce "Dada zan dawo idan an yi azahr zan kai ki gano mai sunan manya." Ta ce "Ina ce yanzu zamu tafi Ali?" Ya ce "Ai yanzu baza su bari ma a gan shi ba." Ta kyabe baki ta ce "Ina ce Ammar yana wajen? Ni da nake da kafa har a mini iyaka?" Ya ce "Yi hak'uri, ki bari na dawo, tiyatar haihuwa zan yiwa wata mata karfe tara zan shiga." Ta rausayar da kai ta ce "Shike nan sai ka dawo, ya zan yi?" Da ga dawo kuwa gabadaya suka rankaya ganin Tijjani. Ni da Babah kawai aka bari a gida. Da ga can zasu biya gidan Iklima su bar ta a can. Dada ta kalle shi ta ce "Mai sunan manya kana wuridin *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN kuwa?" Ya ce "Ina yi sosai, ina kuma ganin tasirin ta Dada. Komai ya saukaka mini, na samu k'arfin zuciya da tawakkali, iyalina kuma suna cikin rufin asiri mai yawa ". Ta ce "Hakane, Hakane! Cikin tausayawa. Sun jima sosai suna shirin tafiya ta cewa su Yaya Ummi su yi gaba tana zuwa. Yaya Ummi ta kalle shi da idonta da suka yi ja. Da rawar murya ta ce "Yaya Bulkachuwa sai mun sake zuwa". Ya yi mata murmushi ya ce "Ummilolona kullum sai kin yi kuka? Kamata ya yi ki gode Allah ina rayuwa. Ban rasa komai ba sai y'ancina. Wanda duk ya zo kurku bisa zalunci sai ya samu daukaka, so ku tsananta yi mini addu'a ba kuka ba". Ta share hawaye ta ce "Allah ya nuna mini ranar da zaka fito Yaya Bulkachuwa sai na yi azumi uku da ikon Allah". Haka kawai ya ji ta bashi tausayi. Tun tana k'arama ta damu da shi ainun. Shima kuwa idan aka dauke Ihisan da su Aliyu ba shi da wata yar'uwar da ta wuce ta. Ya tabbatar ko bai auri Yabi ba, amincinsa da ita mai yawa ne. Sai aurensa da Yabi ya sake girmama amincin nasu domin ya sani, tana son Yabi fiye da komai. Shiyasa ta sake kaunarsa, ta kuma bada gudunmawar shawo masa kan Yabi matuka gaya. Suka tafi, su mama duk jiki ya mutu, tausayi ya ratsa jikin kowa. Sai da suka yi nisa Dada ta sassauta murya ta ce "Mai sunan manya wai anan din akwai d'akin sirri ne, ko kuwa a ina kuke haduwa da Yabi?" Kunya ta kama shi. Ya kasa ce mata komai. Ta ce "A a ba kunya zaka ji ba. Kawai ka fad'a mini domin idan cikin jejin can kuke shiga a samowa jinjirar taimako domin idan aka samu ciki da ranar Allah, kuma a fili irin haka aka yi tarayyar da ciki ya shiga to fa wannan yaron ko yarinyar rashin kunyar da zasu yi sai ya gigita kowa". Dariya ta k'wace masa. Ya yi kad'an ya gintse tare da ce wa "Ki yiwa Allah ki bar maganar nan haka. Ki nemo mata taimakon ki kuma tsananta yi mata addu'oi kawai". Ta saki ajiyar zuciya ta ce"Mai sunan manya abin ne yake ta bani mamaki to ta ina kuke kebe wa ne? Ga yarinya nan ta kwaso Aliyu amma cikin ikon Ubangiji doguwa ce sambal. Dazu ana mata wanka da na zuba mata ido gabobinta irin naka ne sak, haka gashin kanta. Oh ni Binta. Kullum ina kuka da zullimin rashin ka ashe kai baka fasa komai ba?" Ya murmusa ya ce "Kina sauke mini dala'ilalul khairati kuwa?" Da hanzari ta ce "Duk satin duniya kuwa. Ko wacce juma'a nake sauke wa. Kuma hadiyya ce a kanka. Mai sunan manya na ga gurbinka! Dakina a bushe, babu kayan shayi irin naka. Babu sabulai da turaruka irin naka. Ta hau kuka sosai. Jikinsa ya yi sanyi. Ya ce su Baban Kasuwa basa siya miki ne?" Ta ce "suna siya amma har sai sun k'are, kai kuwa kafin su k'are ka kawo wasu. Sabulai da turare masu kyau ba masu s'aukin kudi ba. Amma yanzu fa?" Ya ce "Ammar da Jabir basa yi miki ne Dada?" Ta kyabe baki ta ce "Jabiru kam ai yanzu fama yake yi da kansa. Har ya gama samun damarsa kuwa ban wani more shi ba. Kasan sun k'ullace ni akan ku. Wai nafi sonku. Iyayensa kawai yake yiwa. To yanzu an yi mutuwar kasko, kowa ma ya rasa. Shi kuwa Ammar yana yi mini bazan masa k'aharu ba". Amma sai ta waiwaya ta sassauta murya ta ce "Da uwarsa muke raba daidai. Idan ba'a hannuna ya bani kudi ba kuwa, basa zuwa mini". Ya yi shiru, tausayinta ya kama shi ainun. Abin da ya fahimta Baban Marina da mahaifiyarsa sun fi dukkan y'aya'nta yi mata biyayya da kyautatawa a gareta. Sune kuma wadanda ta rayu tana nuna musu rashin soyayya. Komai sune a baya. Amma kuma shi da kansa ya tabbatar Dada tafi sonsa akan kowa cikin jikokinta. Domin Ammar bai samu sukunin yi mata raddi da fito na fito da ita ba. Da ace shine yake da nutsuwarsa da bai san yadda zata ririta shi ba. Ya tuna sadda zai sadada ya kwashe mata yan kobbonta da kayan amafaninta ya siyar. Bata yi masa fada a gaban jama'a. Bari take sai dare ya raba kowa ya kwanta sannan ta shiga dakinsa su yi sababi, tana yi kuma tana ce wa murya kasa k'asa mai sunan manya kada a gane halin da muke ciki. Shi kuwa sai ya bude muryarsa ya ce "Aji mana tunda sharri zaki k'ala mini saboda kin washe ni. Duk yawan jama'ar gidan nan m, babu mai yi miki sata sai Tijjani! Nan da nan zata bar maganar ta ce "Alfarmar shehu zaka bari. Darajar sunan da ka ambata na yafe maka, Allah ya shirya mini kai, ya tsare ka daga hau da sharrin zamani". Ya nisa ya sake murmusawa ya ce "Ki yi hakuri zan fad'awa Aliyu ya dinga yi miki. Ki kuma cigaba da yi mini addu'a Dada. Sannan ki yafe mini ta'adin da na yi miki a shekarun baya. Da azama ta ce "Wallahi na manta komai. Kuma menene baka yi mini ba da ka samu dama? Aliyu kuwa ai shima a k'ullace yake da ni. Ya sha fad'a mini ina nunawa uwarku butanci. Wanda sharri ne kawai, to wa zai haifi d'a ya ce baya sonsa saboda Allah? Jiya kuwa a gidanka ya ce "Yasan nafi sonka a kansa. Sannan kasan matarsa d'iyar Alhaji ce, su kuwa gabadayansu sun kwashe kayansu a gaban ma'aiki akan sha'anina. Yabi ce kawai take mini sassauci, itama dan tasan ni da kai ba dai mutum ba. Duk tsiyatakunta, duk yadda ka jarabtu a kanta, ba zaka k'i jin kaina ba, ba zaka k'i ni ba! Ta fad'a cikin sigar tausayi. Ya saki gauron numfashi ya ce "Ki yi hakuri Dada. Za'a gyara. Yanzu ki daina damuwa. Sannan kada ki koma Toro. Ki zauna anan BAUCHI ki dan huta. Idan jama'a sun tafi zansa a kawo miki kaji Babah ta gyara miki, ki dinga cin abin ki. Idan sun kusa karewa za'a sake soya miki wasu. Sannan yanzu a hanya za'a siya miki kayan shayin ki, ki ajiye a wajen ki. Naki ne ke kad'ai kada Yabi ta yi miki k'auron nata". Ta yi maza ta ce "A a itama tana yi mini alheri, sannan tunda aka sakaye ka soyayya ta sake kulluwa a tsakaninmu, kullum muka hadu sai mun yi kuka. Kasan yanzu ta yi hankali. Gara na fad'i gaskiya ko ba haka ba". Ya yi dariya ya ce "Ho Dada ta Yabi. Tsoron ta kike ji ne yanzu?" Ta rausayar da kai ta ce "Uum kaidin mata mai yawa ne. Yanzun nan idan ta murde kai ma sai ka juya mini baya a kanta. Barta dai tunda ta nutsu, kuma tana mini ya kamata. A lallaba a tafi a haka, domin na riga na yi imani da kiararin da na ji ubanta yana yi mata. Na ce wa ita kad'ai gayya ce a gidan Marina. Ko kasan kaf zuri'ata babu mai ruwan kudi a hannunsa irin Yabi? Yadda na gasgata karamar Shehu haka na gasgata kudinta na halali ne. Ka ga yadda ta mayar da dakin uwarta ne? To ragowar matan uban ma duk ta yiwa dakunansu kwaskwarima lokacin auren Ubaida. Idan ka ga bajintar da ta yi a auren kuwa sai ka rik'e baki. Matar gwamna har tawaga ta turo su wakilce ta a bikin. Kofarsu tafi ko ina haske da kyawu yanzu, kuma duk ita ce. Ko kai ma irin yadda kake yiwa ubanta ai saboda ita ne. Yabi, Yabi duniya ce? K'aramar halitta sai babban al'amari". Ya kwashe da dariya ainun. Ta ce "Allah kuwa. Mata ai yanzu sun ri'ka. Idan basa yin ka to mijinsu ma ba zai maka kallon rahama ba". Ya sake yin dariya ya ce "Duk zan fad'a mata ne". Ta kyabe baki tare da ce wa "To hudawa cikinka wuka da kanka. Ta jima kafin ta dingisa ta tarar da su a mota suka tafi. ** *Watanni uku a gaba* Zuwa lokacin Husna ta yi gubibi da ita. Shayarwa na matukar ciko da Yabi . Saboda kirjinta suna cika, ita kam tana cikin mata kad'an da goyo yake karbarsu. Bata da matsalar komai sai ta rashin miji. Har zuwa lokacin Dada na tare da su. Ba zato ba tsammani Aliyu ya zo ya kwashe su aka yi musu passport. Sai da passport ya fito yake fad'a musu kudin hayar filling Tijjani ne. Shine kuma ya ce Yabi da Dada su tafi su yi Umrah su yi masa addu'a." Ai kafin ya rufe baki Dada ta zabge da kuka tare da ce wa "Ashe zan koma gabar ni Binta? Hauwa kin iya haihuwa! Shehu ya haifu. Allah ka yiwa Shehu abin da mai zato bai yi zatonsa ba ". Sai kuma ta rushe da kuka wurjajan. Aliyu ya ce "Ganin hakan ya sanya na biyawa tawa uwar sai ku tafi tare" Nan ma Dada ce ta yi fit ta ce "Wayyo Ali
Chapter 140 · 0% Book details