Sashe 95
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta shiga ba shi ha'kuri, shi kuma ya dinga yi mata sababi. Yana fa'din "Da kam nan da kwana biyu na yanke zata koma zan ha'da ta Mamarsu ta je ta zauna da ita ko na sati ne kafin jikinta ya yi k'wari. Amma yanzu na fasa ba zata koma ba. Ki fa'da masa na ri'ke ta, sai ta haihu tunda ba shi da kunya, ya banbanta, ya nuna uwarsa ce ka'dai zata yi wa iyalinsa hidima. Ai kuwa Babah ta dinga ba shi hakuri, ta lallaba ta zame kanta ta bar Tijjani tsundum cikin maganar. Ta shigo d'aki ta duba ni. Ta bani leda mai d'auke da soyayyun kaji. Da kuma soyayyar awara da ta sha yaji mai da'di fal leda (K'ara'i). Na fahimci duk yadda Babah bata shiga al'amarin Bulkachuwa Amma bata dauki abin da ya shafe ni da sau'ki ba. Samuwar cikin jikina kuwa sai na fahimci k'arfin soyayyar da take yi masa. Domin farin cikin da take ciki duk wanda ya rab'e ta sai ya gane hakan. Kusan kullum sai na amsa k'iran abokan arzik'inta. Suna mini sannu da jiki. Daga samuwar cikin zuwa yanzu na manta adadin da ta zo duba ni. A dakin Gwaggo ta shigo ta same ta suka hau cakar juna, tunda k'anwar miji ce. Gwaggo ta ce "Oh ni Asma'u ina ganin kananci a wajen Hauwa. Kina zazzame wa akan sha'anin yara. Amma tunda kika ji zaki yi jika sai b'are b'are kike yi da sintiri a hanya tamkar a kanki za'a fara yin jika". Ta ce "kya yi kya gama. Y'ay'ana nawa ne suka haihu? Yanzu ina ce duk sa'anin aurenta sun haihu dama wandanda suka riga ta auren. Duk ba jikokina ba ne?" Gwaggo ta ce "wace ni na ce ba jikokin ki ba ne. Gani na yi Ummi yar hutun ki ma baki ta'ba zuwa dubiya idan tana laulayi ba, sai idan haihuwa ta yi. Amma Yabi kin zo ganin ta, sau ba adadi sabo..". Ai bata jira saboda me Gwaggo zata ce ba. Ta sunkuci jakarta ta fice tana wani irin murmushin farin-ciki. Tare da ce wa "sai ki yi da wata ai. Ke da ake ganin shirunki da hak'urinki, nan kuwa ba'kinki fal zan ce da bita da k'ulli ne". Washagari ta shiga mota ta juya ba tare da ta ce wa Tijjani komai ba. Ai kuwa kwanaki biyu ya dinga wata irin zarya a cikin gidanmu ta ban mamaki. Baban Marina ya share shi. Rannan da daddare ya murje kunyar sa ya ce "Baba gobe zan zo na d'auki Asiya." Baban ya gyara zama ya ce "Ai haba?" Ya yi wani irin tare da sunkuyar da kansa k'asa ya kasa amsawa. Baba ya numfasa ya ce "Ai k'ure rashin kunyar ka zan yi Tijjani. Wai kai magidanci kada a ga gazawar ka. Shine ka turo mini uwarka dan ka nuna mini ita ce zata maka hidima kai tsaye ko?" Ya yi k'asa da kansa tare da ce wa "Ba haka ba ne Baba". Ya ce "Ya ya ne? Fada mini ina jin ka". Tsawon lokaci bai tanka ba. Baban ya ga ji da shirun sa ya ce "To uwar taka ma da soyayyarka ta rude ta, ta zo zata mini rashin kunya na fatattake ta, bare kuma kai karamin alhaki. Ai tunda ka nuna mini da wajena da wajen Hauwa da banbanci, ni kuma zan nuna maka da kai da Salisu d'aya ne a waje na. Bazan baka Asiya ba sai ta haihu ta yi arba'in". Ya kalli Baban ya ce "Idan na baka hakuri fa Baba, zaka ha'kura ka bani ita?" Kai-tsaye ya ce "Bazan hakura ba." Tijjani ya ce "To ka yi ha'kurin kuskuren da na yi". Ya ce "To na ha'kura Allah ya yafe mana. Ku daina banbanta iyaye. Dukkanmu d'aya ne." Ya ce "To Baba zan kiyaye." Suka yi shiru. Can Tijjani ya ce "Baba ko zaka yi hakuri ka janye zancen sai ta haihu, nan gaba a k'ara wata biyar fa, kafin ma ta haihun". Ya ce "To na ha'kura Tijjani. Allah ya yi muku albarka. Allah ya k'ara ha'da zuciyoyinku. Ya kuma hore maka ikon kula da iyalinka". Ya amw.sa da "Ameen Baba". Washagari da yamma ya zo muka tafi, ni kuma sai fishi nake yi. Muna isa gida ya rungume ni sosai yana ta sakin ajiyar zuciya. Ni kuma na sha mur, na kawar da fuskata gefe guda. Ya ce "Tunda mun dawo ai sai ki huce. Yau kwana uku ko hudu kina mini fishi. Gidan fa gaba'daya zafi ya yi mini da ba kya nan." Nan ma ban kula shi ba. Sai da ya dinga rarrashi da ban baki sannan na bu'de baki na ce "Ai dan ka ga na damu da kai ne shi ne kake musguna mini ta hanyar ce wa dan baka da abin duniya ne nake yi maka wani abu. Tunda haka zaka dinga yi mini kawai ka k'yale ni, kowa ya yi harkarsa". Ya dinga fa'din "ki yi ha'kuri na daina, dan Allah ki huce haka nan". Ya shafa cikina da ya fara tasa wa. Ya ce "Ya bebinmu?" Kawai sai kunya ta kama ni na ture hannunsa na rufe fuskata da hannuwana. Ya sani a jikinsa ya ce "Asiya ina son ki, ina son kasance wa tare da ke muddin rai. Jikina ya yi sanyi na kasa ce wa komai. Amma kalaman sun yi matu'kar tasiri a zuciya da gangar jikina gaba'daya. Ban samu kaina ba sai da cikin ya shiga wata biyar. A lokacin kuma ya fito sosai tamkar ba cikin fari ba. A kan dole nake yin k'unshin, amma sai muka tak'aita iya mutum uku kawai nake yiwa a rana. Amma ina yiwa masu son bak'i da tunda shi babu durk'ushe sosai. Sannan ina yin kitso. Ana kuma siyan lalle. Dai-dai lokacin kuma Tijjani ya fara zuwa Bauchi cikin kasuwar Muda lawal. Ya samu Alhaji Auta aminin mahaifinsa tare ma suke kasuwancin. Kawai dai da tafiyar ta yi nisa sai bai cigaba da bibiyar iyalin marigayin ba. Amma hatta katon fiilin da ya fito a gadon Tijjani a jere suka siye su. A yanzu hakan ma shima nasan filin yana nan. Wajen ya rayu, ya yi daraja ainun. Cikin cire girman kai Tijjani ya yi masa bayanin yana son ya zama cikin yaran shagon ko da ciccire ribabbun kayan miya ne. Domin ya fahimci idan Yabi ta haihu ba k'aramin nauyi ne zai sake hawa kansa ba. Ga shi kuma, kullum rayuwar k'ara tsananta take yi ga talaka. Da sakin fuska ya karb'e shi ya kuma babshi wani bangaren da zai dinga kula da shi. Dan haka sai Tijjani ya zama sai bayan kwana uku yake zuwa Toro. Duk sadda zai je kuma zai je da kayan miya, da kayan abinci. Sannu a hankali yake bin kasuwar yana kuma yin biyayya. Amma ba'a dauki lokaci mai yawa ba sai ya fahimci yadda *BAK'AR TA'ADAR* hassada ta yi katutu a zuciyar jama'a. Mafi yawa yaran shagon sun ha'de masa a dalilin suna ganin maigidan nasu ya daukake shi. Sannan ba ya yarda a yi aikin ha'inci da shi. Domin mafi yawa suna satar kayan su siyar ba tare da sum saka ku'din a shagon ba. Zuwansa sai k'udaden shiga suka karu dan haka Alhaji yake bud'a masa yake yi masa Ihisani. A yanzu da ya wadata su da abinci sai ya koma siyan kayan haihuwa. Duk sadda zai tafi sai ya sayi riguna unisex guda biyu, baya damuwa ko da iri daya ne matu'kar dai kala ta banbanta su. Da ya tara riguna da yawa sai ya koma sayan ragowan kaya. Yau ma Sai da ya biya ya siyi setin robar wanka mai sau'kin ku'di. Ya kalli rukunin masu tsada mother care. Ya ji sun ba shi sha'awa. A fili ya ce "Allah ka hore mini wata haihuwar na siya wa Asiya irin wadannan". Ya kara da setin mai na Nycil. Ya tafi ya hau mota. Bayan ya siya mata tarkacen su fruits dangin mangwaro da su abarba. Sannu a hankali muke rayuwa, har cikina ya shiga watan haihuwa, zuwa lokacin kuma ya canja mini gidan, amma shima na rabin shekara ya kama tunda ya fara tunanin mu koma Bauchi da zama, amma ya ce sai na haihu tukun. Kowa ya kalle ni sai ya yi maganr girman cikina. Har rinjaya ta yake yi. Idan ya tafi Bauchi sai Iklima ta dawo gidana. Sai ya dawo sannan ta tafi. Cikin sa'a haihuwa ta kama ni yana gari, kuma da daddare. Dan haka ya samo abin hawa, muka tafi, sai da aka karb'e ni, aka bani gado. Sannan ya tafi gida ya fa'da. Take Baban Marina ya ha'do shi da Mama akan ta zauna da ni. Har asuba ban haihu ba ina shan azabar duniya. Na yiwa Gwaggo addu'a yafi cikin carbi. Sai da na gama galabaita sannan aka fahimci bazan iya haihuwa da kaina ba. Nan da nan aka shirya ni zuwa d'akin tiyata. Amma muna shiga ciwo ya sake tasowa fiye da ko wanne. Na dinga kururuwa ina salati, tare da fa'din a ce wa "Gwaggo ta yafe mini." Likitocin da zasu yi mini aikin suka rufu a kaina. Ai kuwa sai ga haihuwa gadan gadan. Suka taimaka wajen zaro jinjiri. Yana fito wa ya xika dakin da kuka mai tsananin gaske tamkar gyare. Na fara maida numfashin wahala da gajiya. Ai sai wani sabon ciwon ya taso, gaba'daya na rasa karfina. Take kuma likitocin suka tabbatar ba mabiya ce kawai a cikin ba, akwai sauran halitta. Na fara kuka domin na tabbatar bazan iya sake haihuwa a yanzu ba. Ina kuka ina fa'din "Summa sabila yassara". Daga haka ciwo ya tsananta, na birkice, ga shi na kasa nishi mai tsanani. Da taimakon Allah da na likitocin na biyun ya iso duniya bayan sun k'ara ni. Wahala kan wahala na yi kafin na rabu da cikin da na kwashe watanni tara ina tiriri da shi cikin kalubale kashi kashi. Ban gama wartsake waccar azabar ba, aka shiga yi mini dinki tamkar k'warya. Duk yadda aka yi mini allura kashe rad'ad'i sai da na dinga jin ciwon har cikin kaina. Sai da suka gyaramu sannan aka karbo kayan Bebi a wajen Mama sannan aka fito da mu. Sai hamdala nake