← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 146

Sashe 61

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATTUN SAIWOWI NA MUSSAMAN KUMA GANGANRIYA DAGA CHADI*
*IDAN KINA DA KANWA KI DIYAR DA ZAKI AURAR TO KI ZO KI JARRABA WADANNAN KAYAN DA BABU ASARA KO ALGUS A CIKINSU*.
*SANNAN KE MA DA KIKA KWANA BIYU A DAKI AKWAI BUKATAR KI SABUNTA KANKI*
*AKWIA SAIWOWIN SANYI*
AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR KAZA*
*AKWAI SAIWOWIN DAHUWAR TATTABATU*
*AKWIA SAIWOWIN TSUMI*
*AKWAI PACKAGE DIN MAGANIN SANYI SADIDAN*
*AKWIA PACKAGE DIN AMARYA*
*AKWAI PACKAGE DIN MAIJEGO*
*AKWAI KAYAYYAKIN MASU INGANCI A FARASHI MAI RAHUSA*.
*AKWAI GORAN TULA SYRUP*
*AKWAI GORAN TULA FRUIT*
*INA AIKAWA KO WANNE GARI A FAD'IN TARAYYAR NIGERIA*
*, SO SU MINI MAGANA TA WANNAN LAMBAR 08032773332*
*DAN ALLAH SERIOUS BUYER'S*.

Yadda ya yi maganr ya yi matu'kar dukanmu. Ko ni da ba sonsa nake yi ba. Ya bani tausayi kwarai da gaske. Bare Dada da kowa yasan bata jure ganinsa cikin damuwa.
Ta rasa inda zata tsoma ran ta. Ta kasa cewa komai.
Can ta ce "Tashi ki kawo masa abinci".
Na zum'bura baki ainun na ce "Ba fa ya ci Dada. Akan me zaki ce sai na ba shi, salon ki sa zuciyata tafi hakan b'aci tunda barinsa zai yi".
Da sauri ya ce "Wallahi bazan bar shi ba Asiya. Ci zan yi, yunwa nake ji rabona da abinci tun daren jiya. Na gaji da abincin siyarwa, ban saba ba, tun fil'azal."
Jikina ya mutu murus.
Cikin murya marar amo ta ce "Kin ji ya rantse zai ci".
Na sake d'aure fuska ban tanka ba.
Ta kalle shi ta ce "Kai me yasa idan ta dafa kake k'in ci?"
A hankali ya ce "Zubin wula'kanci ta yi mini. A bu'de kuma a farantin roba".
Dada ta fara ce wa "Eh dole ranka ya b'aci, duk namiji sarki ne a gidansa komin kashinsa kuwa. Lalle Yabi wula'kanci da tozarcin ki kabiran ne".
Nan da nan ya ce "A a Dada ya kuma zaki sake ankara ta. Ai ban ce ki tayar mata da hankali ba. Ke dai kawai ki rarrashe ta, ai dazu ma kin ce yarinya ce zata daina ne".
Ta yi sukuri tana kallonsa cikin tu'ajjibi mai yawa.
Jin ya fa'di hakan, na k'ara kukana na ce "Bar ta ta yi son kan da ta saba yi a tsakaninmu.
Kuma kai ma dan me baka fa'da mata ka kira budurwarka har falona kun yi hira ba. Me yasa baka fa'da mata bayan hakan da ka yi, bai ishe ka ba. Har umarnin ta yi maka girki a kicin d'ina ka bata?"
Na fada cikin kuka sosai.
Dada ta dauki salati tana ce wa "A cikin gidan auren ki, ya yi irin wannan ba'kin zunubin? Eh lallai ba laifin ki ba ne, nasa ne. Wato ni a lokacin da nake kamar ki yaushe za'a mini hakan na bar al'amarin salin alin ba tare da na fitarwa da ja'irar jini ba. Na goge hawaye na ce "Ban yi komai ba na kai k'ara wajen Ubangiji. Sannan kuma har abada bazan sake ba shi abincina ba. Ba kuma zan huce ba, daga nan har na tsufa".
Dada ta yi maza ta ce "Eh to ba dan ina jin tsoron kada kwanaki arba'in din ta cika auren ya samu karaya ba. Dana goyi bayan wannan tutsun na ki. Amma yanzu ki yi ha'kuri, ki yafe, ki huce! Ubangiji yana son masu afuwa da sassauci. Idan ya kuma ni da kaina ne zan sanar da iyayenku. Ai bazan yarda ki yi irin wannan zaman na kuttu ba".
Na girgiza kai na ce "Ai Dada babu maganar huce wa. Babu ni babu sake shiga shirginsa tunda juninsa wula'kanci da nema mini raini ne".
Kafin Dada ta yi magana ya yi fit ya ce "Ban san zaki ji haushi ba Asiya. Na rantse ban yi da gayya ba. Amma tunda ban kyauta ba. Allah ya baki hakuri. Ba zan sake ba."
Na dauke kai ina harara tamkar idona zasu fa'do k'asa.
Ya ce "Dada ki ce ta yi hakuri mana."
Ta nisa ta ce "ki yi ha'kuri kin ji. Ta shi ki ba shi abincin ba dan halinsa ba. Dubi Allah, ki duba Manzonsa."
Ban sake ce wa komai ba. Na mik'e din.
Ban san ya aka yi ba, da na isa kicin din na samu kaina da d'auko plastic plates masu fadi guda biyu.
Na zuba masa na rufe na dora cokali a kai. Na dauka na nufi falon. Ina jin Dada na fa'din "kada ka sake kuskuren saka wata ta yi maka girki. Ban da sakarci ma ina kai ina doguwar magana da ita, bare har kasa a yi maka girki akan idon matar ka. Ai gwara da ta murd'e maka. Kasan halin fa'dan ta ai, bare kuma an tsokano ta".
Murya ba amo ya ce "ki bar maganar nan, sai na zo dakin ki. Yanzu dai lallaba mini ita Dada kawai".
Na shiga na ajiye a gabansa. Ya saki murmushi ya ce "
"Madallah da Asiya". Na cuna baki na dauko ruwa na ajiye masa a gabansa na koma gefe na zauna.
Ya dauki abincin ya dinga ci tamkar bai ta'ba cin abinci irin hakan ba. Cikin kankanin lokaci ya tashi da uban abincin da na danne farantin da shi.
Fanka na kad'awa amma zufa sai yanko masa take yi.
Ya ta'ba ruwan ya ji sanyi sosai.
A hankali cikin kwantar da murya ya ce "Asiya idan kina da ruwan Lipton taimake ni da shi mana please" .
Na dauke kai, kamar bazan amsa ba, sai kuma na tashi na fita ba tare da na ce komai ba.
Dada ta bini da ido tana fa'din "Kasaitacciyar mace. K'aramar halitta mai babban al'amari".
Sai da na isa kicin na yarda na yi dariya.
Na dauko kofi da cokali. Sannan na dauki filas din ruwan zafin.
Na sake ajiye wa a gabansa ba tare da na ce komai ba.
Na zauna na dauki waya ta ina danne danne.
Dada ta ce "Ba ki kawo masa sigari ba."
Kafin na yi magana ya ce "Idan zata dafa take zubawa, dan rage masa tasiri."
Ta murmusa ta ce "Yabi mutanan turai".
Shi ma ya taya ta murmushin. Ni kuwa ban ce komai ba.
Ya kammala, ya yi gyatsa tare da hamdala.
Ya ce "Har na ji ni a duniya. Na gode sosai Asiya. Allah ya yi miki albarka."
Ban amsa ba. Dada ta amsa da sauri tare da fa'din "Barka da arziki Yabi! Kin rabauta tunda kika samu farar addu'a daga mijin ki".
Na yi shiru ban tanka ba. Yayin da shi kuma ya mik'e yana cewa "Bari na canja riga na zo na mayar da ke."
Yana fita Dada ta ce "Yabi maganar nan ta wuce. Ku zauna lafiya. Ko makaho ya zo gidan nan sai ya gane mijin ki na son ki".
Cikin fishi na ce "Baya sona Dada. "
Ta murmusa ta ce "Yana son ki. Ke ma da gangan kike inkarin hakan. Yanzu bazan fa'dawa kowa ce wa ba k'alau kuke zaune ba.
Amma fa idan na dawo gidan nan, na fahimci baku shirya kanku ba. Ku tabbatar sai na ha'da muku iyayenku da Malamai. Dan bazan yarda da zaman kafirci ba."
Na dinga k'unk'unin babu ruwanta da shiga al'amarin da bai shafe ta ba.
Ta gyada kai ta ce "komai zaki ce Yabi ki fa'da. Amma ki sani, ni bazan ha'inci shari'ar musulunci ba. Tilas ne ku bi ka'idojin shari'a a kan aurenku."
Ya lek'o daga bakin k'ofa ya ce "kin gama Dada, ko na je na dawo bayan maghariba sai na kai ki?"
Ta yun'kura tana fa'din "Na gama, yinin ya isa, ba sai na kai almuru a waje ba."
Nima na bi bayan ta muka fito. Na kalle shi ya sanya jallabiya. Ko mai bai shafa ba, bare tuarare. Àllah ya sani ina son na dinga jin k'amshin na tashi a jikin mutum.
Na shiga daki, na d'auko ledar kayan da ya siyo. Na dauki dubu guda a cikin ku'din da na tara na lalle. Na saka mata a ciki. Na k'ulle. Na sake k'ara wata ledar.
Na tarar har sun kusa fita.
Na bu'de baki na ce "Dada mun yi sallama ne?"
Suka dakata na isa garesu. Na mika mata tare da ce wa "Ga shi Dadarmu na gode da ziyarar ki. Amma Wallahi bakin ki k'anin kafar ki akan sha'aninmu Dada. Idan kuwa kika fa'di wani abu, sai dai a neme ni a rasa."
Ta sassauta ta ce "Ayyah Asiya me na ga ni ma ban da alheri? Ai ko da na ce zan fa'di baku zauna lafiya ba. Dan ban fahimta ba ne. Yanzu da na fahimci shine da laifi, ai na fa'di gaskiya. Kawai da ke da shi ku yi kokarin d'abbaka sunna, kada auren naku ya b'aci ba'a ankara ba.
Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na rasa yadda zan yi, sai kawai na juya da sauri na yi ciki na barsu.
Shi kuma ganin hakan ya sanya ya ce "Allah yasa dai ba sai yanzu kika yi mata wannan bitar ba Dada?
Domin a zaune zaki yi mata ba a kurarerren lokaci irin haka ba. Idan kuma zaki fasa tafiyar sai bayan Isha da na fi haka gode wa Dada".
Ta nuna shi da yatsa ta ce "Tabataccen marar ta ido. Oh ni Binta ina kallon shak'iyanci. Ai gara ma da Asiyan ce matar ka, ita ce maganin ka. Haba kana da fitina Wallahi".
Ya yi gum. Ta d'aga murya ta ce "Na tafi Yabi, na gode Allah ya yi albarka.
A ci gaba da hakuri."
Ina zaune ina kallonsu ta windo har suka fice.
Suna tafe a hankali yake jan mashin d'in gudun kada ta subuto tunda ba iya hawa ta yi ba.
A hankali take fa'din "Ashe haka zaka yi mana? Akan me zaka kawo wata har gidan auren ka?"
Ya ce ba ni na kawo ta ba. Wajenta take zuwa fa.
Kuma kunshi take yi, wai ni rage mata aiki nasa aka yi"
Ta hassala ta ce kaniyarka da rage mata aikin. To bata so. Kada ka kuma wannan d'anyen aikin."
Ya ce "To bazan sake ba, da gaske."
Suna isa ana kiran magariba. Dan haka da ya kafe mashin din a zaure bai shiga gidan ba, ya nufi masallaci.
Da nutsuwa ya isa kofar Baban Marina ya gaisa da su Gwaggo cikin kunya da girmama wa.
Kansa a k'asa ya ce "Gwaggo idan uniform din Asiya na nan wai a bata zata fara koyon dinki"
Da sauri ta shiga daki tana ce wa "Sabon yana nan. Tsohon dai Ikilima tana amfani da shi."
Jimawa ka'dan ta kawo masa a bak'ar leda.
Hannu biyu ya sanya yayin karba.
Ya yi godiya, ya yi musu sallama ya tafi.
A gurguje ya yiwa Dada sallama ya wuce gidansa. Yana Jin zumudi da d'okin zama kusa da Yabi.
Yana son yi mata ba zata. Yana son ya shawo kanta, ya d'ora mata girma ko zata rage tsiwa da zafin kai.
Chapter 61 · 0% Book details