← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 146

Sashe 50

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ya zo d:aya. Mun sanya kaya iri daya ba tare da mun shawarci juna ba". Na zabura na cire hular na bu'de akwati ina laluben wasu kayan. Da sauri ya karaso kusa da ni. Ya ce "Dan Allah! Ba dan ni ba. Dan alfarmar Annabi ki bar kayan ki, sun miki kyau ainun. Ina ta fa'da miki baki zaki ta yi yau. Ni fita ma zan yi". Magiyar da ya yi ta sace mini guiwa na fasa canjawar. Ya bu'de flask din abinci ya ce "Wannan doya ce da kwai Salisu ne ya aiko mana. Ya bu'de d'ayan kuma masa ce itin tamu ta mutanan Bauchi da kuli kuli. Ya ce wannan kuma daga gida aka kawo ga kuma kunu". Yana nuna mini jug din. Ya sake cewa "Na tafasa miki shayi na dauko miki?" Ina kallonsa amma ko motsi ban yi ba bare na tanka shi. Bai yi fishi ba, ya mike ya dauko flask din shayi wanda nawa ne a cikin kaya ya dauko. Ya koma ya dauko kofina da kayan hada shayin a leda wanda alamu suka nuna siyowa ya yi. Ya zauna ya ce "Sauko to mu karya". Na sake sharewa. A hankali ya ce "Da ace kin ji nasihar da aka yi ta yi Miki, iya ta jiya kacal da kin raga mini, domin dai ko ya ya nake ni din Ubangiji ya za'ba miki ya zame miki miji. Shi kuwa miji komin kashinsa ai daraja ne da shi." Na yi kamar ban ji ba, na cigaba da danne danne wayata. Ya karya, ya kwashe kwanukan da ya yi amfani da su. Ya dawo ya ce "Zan fita Asiya. Zamu je yiwa iyayenmu ban gajiya. Nasan ba zaki yini da kewa ba yau". Ya sake cewa sai "Na dawo". Daga hakan ya juya ko uffan bai sake cewa ba. Sai tashin mashin dinsa na jiyo. Yana fita na sauko na karya. Na kai ragowar kicin. Na tsinci kaina da son karewa gidan kallo. D'akuna biyu ne a jere akan baranda. Sai kuwa guda daya daga can gefe kusa da bandaki. Sai kicin a dayan gefen. Gini ne ba laifi gashi ya sha fenti. Kan barandar ma tayals ne. Haka kicin dinma. A fili na ce "ko me ya hana a saka tayal a dakin? Na kalli yadda aka k'awata mini kicin din da kayayyaki. Na sani kuma mafi yawa dangin mahaifiyata ne suka zo da kayan. Da sauri na nufi d'akin da yake mak'wabtaka da dakina wanda na tabbatar shine falon. Ina shiga na ji sau'kin takaicin da nake ciki. Domin dai falon ya yi kyau daidai na masu karamin buri. Kujera ce irin mai L din nan. An saka ta a bango guda, da yake falon ma an saka tayals sai aka saka madaidaicim kafet a tsakiyar falon. Ga kuma TV an mak'ala a bango, sai fridges daga can gefe. Shikenan sai labulaye kalar kujeru da kafet din wanda suka kasance royal blue ne. Ga katon agogo mai kyau shima an kafa shi. Na zauna ina jin da'din yadda na ga wajen. Na sani da ace Yaya J ne mijin tabbas da na kasance cikin farin-ciki mai yawa. Na kunna fanka ganin da akwai wuta. Na fita na nufi daya dakin da ya fi kusa da band'aki. Na leka na ga bashi da girman wanda aka saka mini gado a ciki. Ba komai sai labule. Gefe kuma akwatin kayansa ne da tarkacensa sai takalmansa. Na janyo kofar kamar yadda na ganta a sakaye na fito. Na koma falo ina jin dau'kin tv na kama ni. Duk kokarina na kasa ha'da ta. Dole na hakura na kashe na jona wayata a caji. Na zauna iska.lr fanka tana kad'a ni. Ina haka sallamar babbar mace ta saka na zabura ina amsa wa. Na marabce ta da sakin fuska duk da dai ban gane fuskarta ba. Sannan a kallon farko na fahimci ba bahaushiya ba ce, tunda ga siffarta har tsagun da suka cika faffadar fuskarta Na gaishe ta da girmama wa tunda na ga zata haife wacce ta fini ma. Ta ce "Ni ce a waccar kofar. Suna na Gadatu. Ana kirana Maman Safiyanu. Mijina bara ya rasu, ina da yara maza da mata. Allah ya sanya alheri. Allah kuma ya zaunar da mu lafiya. Na yi k'asa da kaina. Na tashi na kawo mata cin cin da dubulan. Bata ci ba. Na juye mata a leda ta tafi da shi. Bata Jima da tafiya ba sai ga y'arta da alamu suka nuna zata girme mini. Gata da garin jiki. Doguwa ce sannan a koshe take ainun. Ta ce "wai Mamansu ta ce na bada kasko a kawo mini garwashi ko zan yi turare. Na dauko na bata, fuskata a sake. Ta kawo mini kuwa. Na tambayi sunanta ta amsa mini da cewa "Rafi'a" Na ce "To na gode miki". Na zuba turare nan da nan gida ya kaure, ya zama na amaryar sosai. Ba jima wa kuwa jama'ar Kangire suka zo motarsu guda, suka dinga addu'a da jan kunnena akan bawa marar d'a kunya na zauna lafiya da mijin da Allah ya za'ba mini. Daga haka suka tafi wanda kai tsaye Kangiren suka wuce. Haka kuwa aka dinga shigi da fice. Hatta Babah ma ta zo kafin ta tafi Bulkachuwa ta dinga yaba yadda ta gan ni. Tare da su Nasiru da Ihisan ta zo. Da kulawa mai yawa ta ce "Duk abin da zai miki kada ki biye shi waya kawai zaki dauka ki sanar da ni, ni kuwa zan miki maganin matsalar. Ki yi hakuri, ki yi biyayya, ki yawaita addu'a. Sannan ban da rashin kunya. Allah ya yi miki albarka." Kuka kawai nake yi. Kukan da bansan dalili ba, ban saniba ko dan na ga ita ma hawaye take yi. Bansan kukan da take ta faman yi ba, na farin-ciki ne ko na tausayina ko kuwa na yadda aka juya al'amarin ne oho. Ashe tare suke da shi ya coge a tsakar gida. Sai da suka fito sannan ya bi bayansu ya rakasu.
Chapter 50 · 0% Book details