← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 146

Sashe 7

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

falala ne da shi Yabi". Na girgiza kai na ce "To ka dinga yi mini addu'a na shiga sahun masu ha'kurin domin kuwa ni duk wanda ya ta'ba ni idan ban rama ba sai nake ganin na zama sullutu". Ya murmusa sosai domin ba mai dabi'ar k'yal-k'yala dariya ba ne. Ya zuba mini ido ya ce "Wai Goggo ce ta haife ki, al'amarin Ubangiji da girma yake. Waton idan kika rama baki zama sullutu ba?". Da hanzari na ce "Ras Yaya J domin dai kai din shaida ne na yadda ake kaffa kaffa da ni, da duk kayana". Ya zuba mini ido ya ce "Allah ka sanyawa Yabi ha'kuri da juriya, a mayar mini ita ta zama mai shanye dukkan kalubale da ha'kuri da kuma kawaici". Na ce "Gaskiya Yaya J kada mu yi haka da kai, roka mini na zama yar gwagwarmaya mana, sai kawai ka roka mini na zama mai ha'kuri komai aka yi mini sai dai na yi kuka, ko ya yi ta cina a zuciyata, watarana sai dai kawai a budi ido aga Yabi ta ha'du da jinya ko ta mace ma gaba'daya. To ni ba zan zama hakan ba". Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kinsan darajar ha'kuri kuwa Asiya?" Na kalle shi domin bai cika fa'din zahirin sunana ba, tunda ya fahimci ina son inkiyata ta Yabi shi kenan ya wajabta ma kansa fa'da mini duk da dai yafi son Asiya. Domin an sha dakuwa da ni akan ce mini Asiya, ina ganin duk wanda ba zai ce mini Yabi ba, to hassada yake yi mini, tunda an yi dawafi da ni a ciki, an yi tsayuwar arfa da ni, an yi jifan shaidan da ni, an yi sa'ayi da ni to mene ne na tauye mini Hajjin?" Ban bashi amsa ba ya ce "W anda Ubangiji ya masa baiwar ha'kuri to ina tabbatar miki an ba shi arzikin duniya da lahira, ba kuma abin da ba zai cimma ba a rayuwarsa, daure ki zama jaruma amma ba jarumtar rashin ha'kuri ba". Na girgiza kai ina murmushi domin dai ban gamsu ba. Har yau da na fara mallakar hankalina ban ga ribar ha'kurin da mahaifiyata take yi ba. Ban ga ribar kawaici da ha'kurin da mahaifinmu yake yiwa zumunci ba. Ban ga ribar ha'kurin da Yaya Ummi take da mijinta da uwargidanta ba. Tunda har yau ita ce a wahale, kuskure ka'dan zata yi ya mata tijara a tsakar gida a gaban kowa tamkar ba ita ce mai k'uruciya ba. Dan haka na k'udire a raina ba wanda zai nemi ta'ba ni, na k'yale shi, zan yi komai dan na tabbatar ban bari na zama gajeriyar katanga mai da'din k'etara ba. Yanayina ya tabbatar masa ban yarda zan iya yin hakan ba. Ya girgiza kai ya ce "Ai shikenan sai dai zan cigaba da yi miki addu'ar dace wa da babban arzikin duniya wato Ha'kuri". Na yi dariya na ce "Dama addu'ar na zama hamshakiyar y'ar kasuwa kake yi mini, ta yadda kasuwacina zai d'auke mini hankali daga dukkan wani rashin ha'kurina da kake ga ni". Da sauri ya ce "Ina yi miki Yabina! Da ikon Ubangiji komai kika kasa sai kin sayar, kullum sai na roka miki Ubangiji ya baki dauwamammiyar sana'a da zaki tsufa kina cin gajiyarta". Da'di ya kama ni, domin Yaya J ne kawai ya fahimci irin yadda nake son na zama shahararrriyar y'ar kasuwa. Ya miko mini tsarabar Jos leda biyu da ya ajiye a bayan k'yauren shiga shashinmu. Na karb'a ina godiya sosai. Na tabbatar Atile ce da kuma turare, tunda sune abu mafi soyuwa a mini kyautarsu. Fahimtar hakan da ya yi, sai ya dimanci yi mini tsarabarsu. Shine ya fara koya mini amfani da turaren Far-away. Daga haka muka yi sallamah. Kai tsaye dakin uwata na nufa ban koma wajen Dada ba.
Chapter 7 · 0% Book details