Sashe 117
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
yi hira, sai dai ya yi da wayarsa, na sani kuma da y'anmata yake yin hirar ni ya bar ni gaho. A Kano kuwa da kunnena na ji yana zancen zai tura gidansu". Ta ce "Akan me ba zai yi aure ba? Akan ki zata zauna, me ce a cikin kishiya ne da kika tsananta wa kanki k'in ta. Allah ya ce su yi mataye sama da d'aya idan zasu iya adalci. An janye ayar ne, ko kuwa rushe ta zaki yi, ki kafirta?" Tana rufe baki na rushe da kuka ina fad'in "Kin bi bayansa ya yi mini kishiya ko Babah?" Ta janyo mafici ta shiga kwada mini tana fad'in "Na bi bayan nasa sakarya. To hakan da kike yi masa ne zai hana shi k'ara auren. Tun yanzu kin tattara kin bar shi, idan ta zo ba sai ta karbe shi gabad'aya ba." Cikin kuka sosai na ce "Babah na rantse da Nasiba yake soyayya. Ya auro kowa amma ban da ita. Ni Wallahi bazan yi kishi da ita ba. Mutuwa zan yi, idan kuwa ban mutu ba, daga ranar da ya aure ta. Billahi a ranar na haramta gare shi!" Na fada cikin matsanancin kuka. Ta saki maficin hannunta ta ruko hannuna ta ce "Ni ma matukar bai nisance ta ba Wallahi sai dai ya nemi wata uwar. Na yafe shi. Share hawayen ki har abada ba zaki yi kishi da ita ba. Na miki wannan alk:awarin". Ya shigo a sanyaye ya durkusa a gabanta ya ce "Ki tsananta yi mini addu'a. Ban san me yasa nake jin ina zakuwa akan lamarinta ba. Idan na je wajenta kwata kwata bana jin sukuni dan tsananin takurar da nake shiga. Ko ganin ta bana son yi. Amma da zarar na taho kuma sai na ji zuciyata tana azalzalar na koma Toro dan na ganta. Ku mini addu'a, ku mini uzziri dan girman Allah. Wallahi addu'ar da nake yi ne ma take saisaita mini al-amurana, amma abubuwan da suka sha kaina masu tsanani ne. Ku taimake ni, kune mafi kusa da ni a yanzu." "Tirkashi" Babah ta furta a fili domin ta fahimci ba haka aka bar shi ba tabbas. Ta nisa ta ce "Allah mun tuba, Allah kada kasa shaid'an ya yi galabar tsinka siriryar igiyar zumucin gidan marina da ta yi saura." Kukana ya tsaya cak a dalilin yadda na ga Babah ta tsorata da furucinsa ainun. Yayin da zuciyata ta shiga zullimi sosai. Ke nan Tijjani da gaske yana burin auren Nasiba. Wani irin k'ullutu mai ciwo ya tokare ni. A matukar sanyaye take fad'in "Zan dage da addu'a, kai ma ka dage da addu'ar da kuma danne yadda kake ji akan lamarinta. Sannan ka saka a ranka ba matar ka ba ce, domin matukar ina raye ba zaka had'a su ba, kai gabadaya ne ma ba zaka aure ta ba. Dalilin da ya hana a baka ita a farko, shine dalilin da yasa ba zaka zama mijinta ba a yanzu" Ta juyo gare ni ta tausasa harshe ta ce "ki yi hakuri kin ji Yabi. Yana cikin canka cakare. Ki tallafe shi har ya tsallake wannan siradin. Mutanan yau da yawansu mugaye ne, zuciyarsu cike take da gilli mai yawa." Na kasa ce wa komai domin na kidime, idan har Tijjani da yake kawaici a gaban Babah zai bude baki ya ce yana zakuwa akan lamarinta a gabanta to lah shakka abin da yake ji babba ne. Hawaye ya dinga tsere a fuskata. Tabbas ina cikin tashin hankali. Bana jin tsoron karawa kishi da ko wacce mace, domin na yi imani namiji baya zama da wacce baya so. Idan kishiya ta kere ka a wani fanni to kai ma da ikon Ubangiji sai ka samu fannin da zaka kere ta. Abu biyu ya dame ni. Nasiba suntumemiyar halitta ce irin matan da suke birge Bulkachuwa. Sannan mahaifiyarta kowa yasan bata barin mazanta haka, a hannunta suke, ko marigayi mijin Nasiba kullum a yunkurin mallake mata shi ta ke. Na tabbatar Tijjani ma za'a yi komai dan ta sha gabana, tunda a yanzu ma da bai aure ta ba idan ta gan ni kamar ta doke ni haka take ji. Da k'yar Babah ta shawo kaina na samu nutsuwa, na daina kuka. Sai yamma muka baro Bulkachuwa. Dan haka sai dare muka iso. Na daure na yi k'arfin zuciya ban cigaba da share shi ba. Na rungume shi da hannu biyu muka cigaba da zama lafiya. Duk dare kuma sai ya fita waje ya yi waya. Idan kuma yana gida baya amsa waya matukar bata shafi kasuwancinsa ba. Asalima kamar ya dakatar da a a kira shi idan yana gida ne. Da kaina na fahimci da gaske ya canja, wulakancin yin waya idan yana gida yanzu ya daina, asalima kaffa kaffa yake kada na tuntsire masa.