← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 146

Sashe 14

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bashi da hayaniya ko ka'dan. Da sauri na janye idon nawa, murmushi yana subuce mini wanda ban shirya yinsa ba, na tsananin shauki ne. Na wuce ba tare da na yi gaisuwar ba. Cikin raha ya ce "Nasiba ki koya wa Asiyan Toro gaisuwa tunda ta zama bak'auya". Da dariya ta ce "Yaya Jabir kaine da fa'din Asiyan Toro yau? Babu ruwana a shirginka da Yabi". Ya k'yal-k'yale da dariya ya ce "Tsoron ta kike ji ne Nasiba? Kin fita tirinya fa, to kuma ya za'a yi ne tunda ku biyu zan ha'da na aure rana guda?". Ta yi maza ta ce "Lallai kuwa ka shiryawa darun Yabi domin har ka tafi ba zata saurare ka ba, ni kuma ba zan taya ka rarrashi ba". Ta wuce ni da sauri ta shige shashin Dada. Ni kuma na wuce shashinmu a dalilin yau Nazira ba ta samu damar zuwa ba, saboda tana fama da ciwon mara. Zuciyata har wani tukiki take yi na tsananin bacin ran kalaman Yaya J. Wai zai ha'da ni da Nasiba ya aura. Na yi tsuka na ce "Sai dai ya aureta ita ka'dai. Dama na san dunbula dunbulan kirjinta na iya tafiya da shi, ba'kin ciki ya sake turnike ni a dalilin ni ba mai cikar k'irji ba ce. Har yanzu bana saka breziya sai dai half best, domin a manne suke a kirjina yan kananu da kadan suka fi tsakuwa. Amma Nazira da Nasiba kam kirjinsu a cike yake sosai. Wataran har rayawa nake yi ko dai na fara shan ruwan baru ne ko zan yi sa'a su fito su cika mini kirji ni ma. Amma sai na kasa, mussaman da sai na ro'ko ruwan kuma sai nake ganin kamar za'a gane dalilin shan da zan yi. Da daddare ya dinga aiken na zo amma na yi mirsisi na ki fita. Washagari a zauren Dada na tarar da shi. Na sani sammakon tashi ya yi dan ya hadu da ni. Domin shi ba ma'abocin tashi sassafe bane, da zarar ya dawo daga sallar asubahi idan ya kwanta sai tara yake tashi. Nazira ta gaishe shi ta shige, yayin da na dauke kai fuska murtuk zan wuce shi. Ya yi maza ya sha gabana yana fa'din "Haba Yabin J baki san wasa ba ne? Na yi bakam tamkar dai ban fahimci da ni yake magana ba. Na yi kasa da kaina. Ya sassauta murya ya ce "Yanzu Ashe zaki iya mini irin wannan fishin Yabi?" Na dago na kalla shi na ce "Oh wai ka yi zaton ba zan iya ba? To kuwa ka dauka zan yi maka fiye da hakan domin zan iya shafe babinka gaba'daya." Ya jima yana kallona cikin ki'dima. Ya yi k'arfin halin cewa "Me ya yi zafi haka, daga wasa?" Na sake d'aure fuska na ce "Bansan wasa ba, ban iya shi ba, ban kuma ta'ba daukan al'amarinka a matsayin wasa ba, bare har na yi maka tsokanar da zaka ji ka tozarta". "Hakane, na kuma gasgata ki, yanzu ki yi ha'kuri ba zan sake miki irin hakan ba kin ji". Na jijjiga kaina tare da yin wata irin shakiyar dariya na ce "Ha'kurin ma ban iya shi ba. Ba kuma zan koyo shi a dalilin cin fuskar da aka yi mini ba. Na riga na barwa Nasiba kai, dan haka ka manta da wata Yabin Marina". Ya yi tsam cikin kaduwa wata'kila yana mamakin yadda kishi yake kutsowa tunda ga kasan zuciyata ne, kallon yarinya k'arama yake yi mini, sai dai bai san yar shekaru goma ma zata yi kishin abin da take so ba, bare ni da nake da shekaru sha sha biyar, na ke harun sha shida. Ya lankwashe murya cikin rarrashi ya ce "Ai na yi zaton ina da wata alfarma ta daban a wajen ki, ban ta'ba zaton zan yi miki laifin da zaki shafe ni a zuciyar ki ba. Yau dai daya tak da na sab'a miki, ki daure ki mini uzziri, ni kuma na yi al'kawarin ba zaki sake kama ni da laifi irin wannan ba". Na dauke kai na ce "To idan na yi ha'kuri na ce maka komai ya wuce, ya zan yi da tafasar da zuciyata take yi idan na ga Nasiba? Ya zan yi na goge amincin da zuciyata ta yi akan ita kake so bani ba, tunda ita din ta fini zama y'anmata?" Tsananin mamakin da na ba shi ya sanya ya kasa magana na tsawon lokaci. Sai da ya jima kafin ya numfasa ya ce "Ni fa ba wacce take burgeni nan duniya idan ba Yabin Marina ba. Kinsan dai ina tsokanar Nasiba tun fil'azal tunda abokiyar wasanmu ce, yar mace da dan namiji muke. A kaikaice na ce "Oh oh, ashe dama ana wasa har irin haka? To kuma wai ya matsayin wannan *Bak'ar Ta'adar* a shari'a tunda ba'a wasa da maganar aure?" Ya dan tunzura ka'dan ya ce "Ke Yabi". Nima na ce "Ke Yabi ko kuma ke gaskiyar magana?" Ya girgiza kai ya ce "Shi kenan na gode, na gode sosai da yadda kika ajiye ni". Ya fice ya bar ni, kafin na shiga wajen Dada Bulkachuwa ya fito daga dakinsa. Ya yi fitoh irin na tantiran yan-iska ya kalle ni ya ce "Asiya Toro rikakkiyar budurwa". Ya kwashe da dariyar iyashege ko me ya tuna kuma sai ya gintse dariyar tasa. A fili ya ce "Ban da ma shan koko d'aukar rai ne, ta yaya kamar Jabir da yake ganin Bigger babes zai tsaya wajen kwailaye irin Asiya Toro? Ya wuce yana sake fa'din " Soyayya da kananun yara menene a cikinsa ban da raini da ba'kinciki, yar yarinyar da bata gama iya wanka ba ma sai ta caccaba maka magana son ranta, abin ba'kinciki kuma dole ka rarrasheta ko ka hadu da gallazawar zuciya."
Chapter 14 · 0% Book details