Sashe 33
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A fili na furta "dutse a tsakanina da Bulkachuwa ya Rabb". Ina wankin ina jaddada wa kaina matu'kar Yaya J bai yi yun'kuri mai k'arfi ba, to nan da lokaci kankani zan bawa kwamishina dama ya fito tun zuciyar Baba bata ayyana masa wani al'amarin da zai iya kassara ni, ya dauwamar da ni a cikin ba'kin ciki mai tsananin gaske ba. Na kammala wankina. Mama ta fito ta ce "Yabi anjima zan aike ki gidan Nazira". A ladafce cikin murna na ce "To" Domin kuwa ha'din baki muka yi da Naziran, saboda na yi ta tambayar Baba zani gidanta yana hana wa, basan me yasa yake hana ni zuwa ba, amma bai ta'ba yin k'orafin zuwa koyon sana'ar da nake fita ba kullum. Duk kuwa da ce wa ake yi shargalle nake yi da sunan koyon sana'a. Shiyasa Nazira ta ce wa Mama ta bani kwanuka na kai mata kar aba wa marar wayo ya yi b'arinsu su yi lamba. Tunda idan ita ce ta aike ni Baban ba zai hana ba, ba kuma zai tambayi aiken menene ba. Dan haka a gurguje na shirya na tafi. Muna zaune ina bata labarin yadda muka yi da J. Ta galla mini harara ta ce "um um uhum. Ashe dai Yabin bata san ciwon kanta ba. Har wane ne Jabir kuma? Idonta ya ciko ta ce "Allah ka sanya sai bayan raina zaki zama matarsa!. Jikina ya sabe da rawa na ce " Addda Nazi! Cikin gigita domin ban ta'ba ganin fishi mai yawa a tare da ita irin hakan ba, ita din mai ha'kuri ce, mai kuma sanyin hali ce tamkar dai ba daga tsatson Mama ta duro ba. Murya na rawa na ce "mene ne na wannan mugun fatan Nazira?" Idonta taf cike da hawaye ta ce "Da kin fahimci yadda na k'yamci al'amarin, da baki zo gabana da wannan maganar mai bak'i tamkar zunubi ba. Ban iya fishi ba, shi yasa nake kaffa kaffa da duk abin da zai ha'da ni rikici da jama'a, domin ni kaina ina tsoron fishina ina kuma yawaita neman tsarin Allah da shi. Amma zan fa'da miki, matu'kar kina son ganin fishina da barranta kaina daga al'amarinki to ki cigaba da yi mini wannan maganar da nake fatan ajalina ya riske ni kafin ta wanzu". Sai ta fashe da kuka sosai. Cikin kuma kukan take cewa "Yanzu duk ba'kin cikin da aka cusa wa ubanmu, duk yadda aka wula'kanta ki, dan ke ce asararriya har ki kalli dan Baban Tsakiya da sunan soyayya irin ta aure? Na rantse miki da Allah idan ace Jabir ne ka'dai namiji a duniya gara ki tabbata babu aure, ko ni na mutu ki maye wa mijina madadina da dai Yaya Jabir ya same ki. A haukanki Baban Tsakiya zai bar shi ne? Ko kuwa kwantaccen tunaninki ya fa'da miki Baban Kasuwa zai bashi aurenki alhalin tasa y'ar ce matarsa? Kaico da wannan maganar da kika nufo ni da ita. Nima cikin kuka na ce ",Takura mini ya yi shine na yi masa gatse dan ya shafa mini lafiya." Ta ja tsaki mai tsananin gaske tare da fa'din "Amma shine kike rawar jikin fa'da mini, idan ba kya so me ya sanya zaki yi mararin sanar mini?" Ta nisa ta zarce da fa'din "Idan zaki ha'kura da shi ki hakura Yabi. Domin Jabir ba mijinki bane, na tabbatar duk sanyayyar zuciyar Baban Marina ba zai ta'ba bawa Jabir aurenki ba, ban da dai ma mai k'arfin halin jure damuwa ne da kuma kawaici da tuni bai ha'du da ciwon shanyewar barin jiki ba a dalilin abin da yan'uwansa suka yi masa. Ashe duk zafin ranki, da kishinmu da kike yi a banza ne a kuma fatar baki ce? Wallahi matu'kar zaki nemi zama ahalin gidan Baban Tsakiya ki tabbatar kin fita daga namu ahalin Yabi" Ta tashi ta bar ni tana kuka sosai. Jikina ya mutu wato ba k'aramin gaba ba ce ta shiga dangimu ba kenan? Duk ha'kuri da kawaicin Nazira ita ce take fadin tsauraran kalmomi akan zumunta irin haka? To idan har Nazira mai sau'kin hali da k'ullaci zata yi hakan to ina ga Yaya Ummi shakikiyata kuma mai ra'ayin rikau?. Domin ita hatta zumuncina da Nazira adawa take yi da shi tana ganin ita ce tafi kusa da ni, ita ta cancanci mu yi irin wannan soyayyar, ta kasa fahimtar tazara mai yawa ce a tsakanina da ita, Nazira kuwa tare muka taso tamkar tagwaye, kuma Ubangiji ya jefa mana soyayyar juna duk da k'unbiya k'unbiya irin ta iyaye mata da kishi yake haifar wa. Bare kuma mazan Gidanmu. Yaya Rabi'u shine sa'an Yaya J tare suka taso, bayan jini da ya ha'dasu, abokanta suke yi sosai, amma Yaya Rabi'u da kansa bayan an yiwa J aure da Maijidda na ji yana fa'dar bai k'i wani a duniya har cikin zuciyarsa irin Baffanninmu ba, yana kuma fatan kada a k'addara auren zumunci a tsakanin y'an k'ofarmu da tasu ila yaumil k'iyamati. A sanyaye na bita uwar d'akinta na dinga rarrashinta da k'yar na shawo kanta ta ha'diye kukan nata tamkar yarinya y'ar k'arama haka ta koma mini. Wannan yinin bai yi wani armashi ba tunda zuciyarta ta riga ta baci. Har na dawo gidanmu a takure nake jin kaina, domin ban ji da'din yadda Nazira bata sake mini kamar yadda nake so ba. Na iso gida na tarar da Yaya J gurfane a gaban Baban Tsakiya kansa a k'asa da alamun kuka yake yana fa'din yayi masa alfarma ya bar shi ya yi abin da Allah ya hallata masa. Ba sassauci ko nauyin ganina ya ce "Na gama magana idan baka gamsu ba, ka je ka nemi wanda zai shige maka gaba, babu damuwa, amma fa babu albarkata a ciki". Na shige da sauri, ina ambaton "Innalillahi wa inna ilaihir Rajiun". Ina shiga gida sallar almuru kawai na gabatar na dauki waya na k'ira kwamishina na ce "Baba ya ce ka turo waliyyainka". Ya dinga murna yana sanya alheri da albarka, tare da addu'ar Allah ya sanya yadda na aminta da shi, kada ya kunya ta a idona. Na ajiye wayar ina mamakin ni kuwa a duniya me na tsare wa Baban Tsakiya ne? Na dinga Jin haushin kaina yadda na makance ina son Jabir! A yau na yarda na gamsu tazarar da take tsakaninmu tamkar tazarar sama da kasa ne . Ba zan ce bana son Yaya J ba, domin kuwa ikon zuciyata ba'a hannuna yake ba. Amma na yarda da maganar Nazira ko shi ka'dai ne namiji a duniya to haramun ne a gare ni. Bayan Baban Marina ya dawo gida bayan sallar isha a tsakar gida Inna ta shimfida masa tabarma a dalilin zafi da ake fama da shi. Ya kammala cin abincin da ta gabatar masa kenan. Ya kalli ni duk da muna da tazara ya ce "Yabi zo nan". Zuciyata ta harba da tsananin gaske. Na matsa kusa da shi kamar yadda ya yi mini umarni. Babu sukuni ya ce "Ya ya maganar Alhaji?" Kaina a kasa na ce "Na isar da sakon na ka". Ina rufe baki ya ce "Madallah da Yabi! Ubangiji ya tsare ki, ya sanya albarka a dukkan sha'aninki". Farin-ciki ya mamaye ni, na amsa da ameen da karsashi. Ya sallame Ni. Na shiga dakinmu na tarar da Gwaggo tana ta kulla siganta hankali kwance. A zuciyata ina ta jinjina mata na yadda bata raina riba duk kanknatar ta. Domin sigan nan mafi yawa sai ta yi ciko duk sadda za'a auno mata. Idan na ce ta bari, sai ta ce da bata siyar wa, da ba zamu sha yadda muke so ba. A hankali na ce "Sannu da kokari Gwaggo! Allah dai ya nuna mini ranar da zan hutar da ke zaman kullin sigan nan dan kawai mu saka siga a koko ya ji". Ta yi murmushi tana fa'din Yabi da dogon buri kike, dama ana wuce yin sana'a ne? Na ce "Indai bata kawo ku'di ba. Ta yi murmushi ba tare da ta ce komai ba. Na bu'de baki zan yi maganar sai kawai muka ji sallamar Yaya Jabir a tsakar gidan. Baba ya amsa masa tare da cewa "iso mana Jabiru". Ya zauna a tabarmar ya gaishe shi cikin nutsuwa. Baba ya amsa cikin sakin fuska tare da tambayarsa iyali da karatunsa. Tsawon lokaci Yaya J bai iya cewa Baban komai ba. Sai Baban ne ya ce "Akwai matsala ne Jabiru?". Cikin rauni sosai ya ce "Baba so nake ka bani Yabi na aura". Zuciyata ta buga, na yi matu'kar kasa kunne a kansu, ko kwakkwaran motsi bana son yi. Hatta Gwaggo tsaya wa ta yi tana saurare. Murya da walwala Baba ya ce "Jabiru ka zo inda za'a yi maka komai, ina tabbatar maka da a ce a wani wajen kake son auren da na je na nemo maka. Sai dai da yake y'ar tawa ce shiyasa bazan iya komai ba. Kana da siffar da za'a baka aure babu haufi. Amma akwai mishkiloli da baza su bari na baka Yabi ba. Farko matarka da take hannunka itama y'ata ce da kanina ya haifa. Kasan kuma matan yau basu dauki lamarin kishi da sassauci ba. Ha'dasu kishi zai iya ruguza komai ya mayar dasu abokan gaba, sannan zuri'armu zata dare ne, wasu na bawa Yabi kariya, wasu na bawa Maijidda. Da ace Yabi ka fara aura, ka zo kana son Maijidda daga baya to ina tabbatar maka da sai inda karfina ya kare, domin ina da tasirin da zan lank'awasa ta a zauna lafiya. Amma tunda ka riga ka auri Maijidda a farko, dole a ha'kura da maganar Yabi dan a samu a cigaba da lallaba zumuncin da ya dan yi saura." Tsawon lokaci ban ji Yaya J ya ce komai ba tabbacin ba haka ya so ji ba. Murya ba amo ya ce "Baba kai ne tsanin da nake ganin zan taka dan na samu cikar burina." Baba ya numfasa ya ce "Ai kuwa a wannan karon ba zan zame maka tsanin ba Jabiru. Domin ina sane da yadda Mahaifinka bai amince maka ba, ka yi kankanta da yawa ka jefa kanka a cikin manyan matsaloli, domin auren da kake son yi ba zaka samu nutsuwa da shi ba tunda babu