← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 146

Sashe 89

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

iya goya ni, ya yi shara. Har k'aton baho ya siyo irin tafkeke na masu wankan jego. Ya cika shi da ruwa ya dauke ni ya tsunduma. Ya wanke ni tas. A shimfida kuwa irin murza ni da yake yi, da da'din da yake jiyar da ni dole ma na so shi na rikice a kansa. Domin har cikin zuciyata na fara tunanin da ba shi na aura ba dan ban more ba. Har jin haushin son da na yiwa Yaya J na fara yi. Gaba'daya na gama mutuwa a kansa, ba abin da nake so irin na gan shi a gida idan yamma ta yi. Yanzu da baya fita lahadi a gida yake yini. Da kaina na soke yin lalle da kitso. Komin girman mace bana yi a wannan ranar zan fa'da mata maigidan ya hana yi a wannan ranar. Dan na fahimci ba a daina zuwa ana katse mana jin da'dinmu ba sai nake yawan rubutawa a status d'ina cewar babu lalle ranar lahadi haka ma kitso. Mun yi kyau, mun shak'u da juna, komai yana tafiya dai-dai mussaman da na daina yi masa rikicin bai yi mini ciki ba. Da kansa ya dauke ni muka je asibiti da muka cika shekara guda da aure. Dukkanmu aka auna mu aka tabbatar mana lafiyarmu k'alau cikin ko wanne lokaci zamu iya haihuwa. Shike nan sai na daina damuwa illah iyaka ban daina addu'ar ma samu ciki na haihu ba. Muna cikin wannan yanayin mai da'di Rafi'a ta kammala karatunta na jamaia ta dawo gida gaba'daya. Kusan kullum sai ta shigo mini. A zuciyata bana so amma tunda uwarta ba k'aramin kirki take yi mini ba. Sai nake share wa mussaman ita din ma mai kirki ce. Amma haka kawai nake jin fargabar zakewarta a wajena domin na riga da na sani mijina yana son yan lukataye irin ta. Ni kuma yar firit ce. Sannan bazan yaudari kaina ba, zai iya sha'awarta tunda jikinta rugu rugu ne, kuma bayltw damu ta saka mayafi ba. Tunda tana ganin ba sai ta fita waje da ta shigo ba. Bugu da kari ba Hausawa ba ne. Wasu abubuwan nasu da namu akwai banbanci. Haka dai nake ta daure wa ina ta k'ok'arin ban bar shi da kewa ba. Komai yake so sai na yi masa. Ba kuma na tab'a k'osawa da al'amarinsa duk da nima ina son harkar. Amma bana ja masa rai saboda kada ya ga ni a waje ya yi sha'awa. Ba kuma na nunawa ya gundure ni. Ana cikin haka aka tashi bikin. Ihsan k'anwarsa. Tun saura sati biki na tafi, saboda a fara komai da ni, sannan ni ce zan mata k'unshi da kitso. Babah sai ina ka saka take yi da ni. Yadda ta ga na murje na yi kyau ba karamin da'di ta ji ba. Na sani kuma da a ce da goyo na je mata da tafi haka murna. Shi da kansa ya kai ni. Washagari ya tafi akan sai nan da kwanaki ka'dan zai juyo. Komai sai da na bar masa, hatta miya sai da na soya masa, na yi masa cincin. Kawai tafasa farar taliya ko shinkafa zai yi sai kuwa shayi. Ana gobe biki y'an Toro suka iso. Aka yi hidima cikin rufin asiri taro ya tashi lafiya. Kwanaki biyu a tsakani ya zo muka tafi shake da kayan biki masu yawa. Tunda muka yi aure bamu ta'ba nisa da juna ba sai wannan karon. Duk da dai a Bulkachuwan ma ranar biki sai da ya faki ido ya jani muka je wani waje ya yi abin da zai yi sannan ya dawo da ni. Amma muna isa gida ko hutawa bamu yi ba. Daki ya ja ni bamu fito ba sai da ya samu nutsuwa. Da daddare ina zaune a cinyarsa sai ce mini ya yi "Little baki da nauyi, shafal ban ji kin danne ni ba". Na zabura na kalle shi, gabana ya fa'di sosai. Da rawar murya na ce "Sai yau ka fahimci haka? Wa ka d'ora a cinyar da yanzu baka ji yadda kake so ba?"
Chapter 89 · 0% Book details