← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 146

Sashe 96

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

yi a zuciyata. Ina sake girmama sha'anin Ubangiji. Ba a taba ce mini tagwaye ne a cikina ba. Na tarar y'anuwa sun zo asibitin da yawa. Na dan ji da'di domin kaf y'ay'an Babanmu da aka aurar da su. Ba wacce ban ga ni ba, har Ubaida kuwa. Ko Yaya Indo da bata sake taka gidana tun ranar da aka kai ni ba, na ganta a wajen. Idona ya cika da k'walla ina ayyana duk yadda shaidan yake shiga cikin al'amarin zumuncin yau, jini yana da tasiri k'warai da gaske. Ina ta waige waige domin zuciyata so take ta ga jariraina, so take kuma ta ga uban y'ay'an. Amma ban gansu ba gaba'daya. Na ha'diye na yi shiru na cigaba da kallonsu d'aya bayan d'aya. Tare da amsa sannun da suke ta faman yi mini. Na jima kafin barci ya sure ni. Na dai farka na tarar da Babah ta Bulkachuwa zaune a gefena tare da Mama. Sannan Inna da Yaya Ummi suna ri'ke da jariran da aka nad'e su da zani iri d'aya. Dada na gefe tana mulmular goro a bakinta, tana kuma jan tasbaha. Da suka ga na farka, suka hau fa'din "sannu, sannu Yabi". Dai-dai lokacin kuma ruwan da ake k'ara mini ya k'are. Wata jamiar kiwon lafiya ta shigo a daidai ta cire mini, tana mini sannu. Da walwala ta ce "Mrs Bulkachuwa ina taya ki murnan samun wad'annan kyawawan jariran. Allah ya rayasu ya baki lafiya". Na yi shiru su kuma ahalina suka amsa da fa'din "Ameen mun gode". Ta kalli Mama ta ce "Zo ki ri'ke ta, ki taimaka mini mu zaunar da ita. Yaranta suna bu'katar nono". Da dabara suka zaunar da ni. Sai da ta tambayi na ji da'din zaman ko na takura a gyara ni?" A hankali na ce "Ya yi". Dada tana ganin malamar asibitin ta karbi yaron hannun Inna. Ta zabura ta ce "Dakata dafta". Kowa ya mayar da hankalinsa kan Dada da ta jawo ledar da ta zo da ita, ta fito da k'ok'o tare da gorar mirinda da kuma wani ruwan maganin a wata gorar daban. Ta yun'kura da k'yar tana dunduk'e ta nufo gadon. Ta kalli jami'ar kiwon lafiyar da take shirin kwantar da jaririri a jikina ta ce "gafara ka'dan". Cike da girmamawa ta kauce tana ce wa "Sannu tare da mamakin me zata yi. Sai dai su yan d'akin sun san me zata yi. Ta saka k'ok'o a cinyata, ta d'aga rigata. Duk da y'an k'ananun nono gare ni, amma tunda cikina ya fara girma suka ciko. Yau kuwa da ruwan nono ya zo sai suka yi girma suka tsaya k'yam tamkar kwakwa. Karon farko da aka bu'de mini nono a bainar jama'a ban kuma ji nauyi mai yawa ba. Ta daidaita ta dinga zuba ruwan robar ta kuma saka hannu tana wanke mini su. Sai kuma ta fara k'ok'arin matsesu tana fa'din sai an cire mataccen nonon da yake lalata jinjirai kafin a basu su sha. Dukkansu babu wanda ya yi inkarin hakan domin suma akan wannan Ta'adar suke. Nan da nan malamar asibitin ta ce "kin wanke Dada ya isa haka". Ta d'ago ta ce "Yarinya me kike fa'da ne? Kina son ki ce wai dak'ashin za'a bari su sha?". Cikin girmama wa ta ce "Eh Dada. Domin alfanunsa mai yawa ne a jikin jariri. Shine rigakafi na farko da Allah subhanahu wa ta'ala ya fara yiwa dan-adam da shi." Dada ta bar komai ta kafe ta da manyan idanuwanta ta ce "To sannun ki, amma su wadannan baza su sha datti ba. Kullum a cikin yiwa Allah da ma'aiki k'arya ku ke. Allah dai ya shiryeku idan zaku shiryu".
Chapter 96 · 0% Book details