← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 146

Sashe 26

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama da zata dafawa Nazira kazar aure har da Maijidda ta hada ta dafawa. Ina kallo yadda ta samo tattabaru ta hada da saiwowi ta sake dafa musu. Haka Gwaggo ta maze kamar bata gane ba. *Mai bukatar saiwowin dahuwar kaza ko na tattabaru da sauran kaya na mussaman ta mini magana akan lambata 08032773332*. Ina ji, ina ga ni aka daura auren Yaya J d'ina, da Maijidda. A ranar kam buya na yi, a makwabta na yi kukan da ban ta'ba yin irinsa ba. Na dinga jin wani irin abu tamkar zai fasa mini zuciya gaba'daya. Fa'di nake "Ya Allah! Ya Allah". Idan na tuna nagarta da sanyin halinsa sai na ga ba karamar asara na tafka ba, wacce na saddakar ba zan mayar da irinta ba. Har dare ba wanda yasan inda nake, sai da na ji dirin isowar motar daukan amare sannan na fito. Dan ba zai yiwu ace ban raka Nazira d'akinta ba. Da na fahimci Nazira za'a fara kai wa domin motocin kai ta ne suka fara iso wa sai kawai na fa'da daya daga cikin motocin. Sai a dakinta muka ha'du. Duk yadda ta ke lullube a cikin mayafi said da ta riko hannuna ta ri'ke gam tana sake kankame shi tabbacin farin-cikin da take ciki bai sa ta manta tawa damuwar ba. Sai da kowa ya watse aka bar ni da ita, domin dai bamu da wasu kawayen da zasu kai mana dogon dare. Ta kalle ni ta ce "Mu yi ha'kuri Yabi, kara daure wa, idan muna ganin ki a hakan ba wanda zai samu sukuni. Kinga ma yunwa nake ji, tun jiya da muka ci abinci ban sake saka komai a bakina ba, ba wanda hankalinsa ya kai a bawa amarya abinci, na sani da kina kusa da ni da kin bani". Na ce "Afuwan Adda Nazi, amma ai yanzun nan Malam Yunus zai shayar da ke nama da madara". Ta galla mini harara tare da fa'din aku sarkin magana". Na mike domin na ji ana fa'din mai motar ya dawo. Da k'yar ta bar ni na tafi, tana kuka, ina yi. Kwanaki ukun da suka biyo bayan bikinsu Yaya J sun fi ko wanne tsauri a gare ni. Sa'ar da na yi ma ba a gidan aka yi masa gini ba, a can bayan gari ne da kansa ya gina abinsa sai dai da tallafin Baban Tsakiya. K'aramin gida mai fasali na ban sha'awa, ba burin da banci akan wannan gidan ba. Ko bandakin gidanmu da yake sani takaici, da zarar na tuno bandakina a cikin daki yake a gidan Yaya J sai komai ya wanke mini, na yi ta zumudin zuwan lokacin da zamu yi aure, ashe dai wasikar jaki nake tsara wa. Tayals a ko ina, ga furanni har da fasadabir ya shuka mini, ga bishiyar mangawaro da ni na bayar da kwallon ya shuka, ita ma ta kama sosai. Amma tashi guda aka ruguza mini komai, Maijidda na cikinsa an kuma sake kawata mata gidan da kayan alfarma domin takanas aka tafi Jos aka siyo mata furnitures, ko yaran Baban Tsakiya su Firdausi basu samu gatan ta ba. Haka na dinga rama tamkar ku'din guzuri. Ban samu sassauci ba sai da aka doshi kwanaki ashirin da auren a dalilin na koma zuwa makarantar boko mun shiga aji shida. Da k'yar Dada ta bari muka koma. Gaba'daya na zama shiru shiru, idan ba kure ni aka yi ba, na daina fa'da, ko yara na gani sai dai na rabasu na yi musu sulhu. Amma na daina rama wa wani duka, bare ni na doku da kaina. Duk da yadda na canja ba yaron da yake kuka sabo da ni, ban tsira a wajen mutan Gidanmu ba. Gaisuwata da kyar Baffanina suke amsa wa. Na rasa laifina, zamu gansu tare da Nasiba mu gaishe su, su amsa ta ta gaisuwar cikin walwala har suna ambaton sunan ta amma ban da ni. Na fa'dawa Gwaggo ta ce "Na cigaba da gaishe su kada na gaji suna da hakkin na mutuntatasu. A sanyaye na ce "Gwaggo ni bani da hakkin su sakar mini fuska su mua'amalance ni da mutunci tunda jininsu ce ba agola ba? Nasiba fa ba yar gidan nan ba ce, amma ace ta fini a wajensu?" A duk sadda na yi mata wannan k'orafin dauke kai take yi ta ce "To ai laifukan da kika yi musu ne, da yawa, sannan ita Nasiba ko ba y'ar gidan ba ce amma tana da wata alfarma tunda a ko ina ana son y'ay'an da yar'uwa mace ta haifa, ke ma ai har da halin ki ya sanya suke yi miki hakan". Idan ta fa'di hakan sai kawai na kalle ta na yi shiru, domin na sani ta fa'da ne dan kawai na fahimci girmansu. Ba dan suna yi mini adalci ba. Har sati uku sannan na warware na rungumi zuwa makaranta duk da karatun ma sai a hankali saboda kewar Nazira na damuna. Dada kuwa fa'di take na fito da miji domin wanda za'a bawa Nasiba ya ce "Kowanne lokaci zai iya gama gidansa ba sai bad'i ba, ita kuwa ranar auren Nasiba ita ce rana ta, ko na fito da miji, ko a bani Malam Nata'ala shine damo sarkin ha'kurin da zai jure wa dukkan iya shegena. Malam Nata'ala dattijo ne da yake zaune a unguwarmu mutumin kirki ne kwarai da gaske matansa biyu da yara da dama, tsanagaya ce da shi ma'ana Malami ne mai almajirai. Ban wani dauki maganarsa da Dada ta ambata da muhimmanci ba, illah k'anzon kurege. Kwanci tashi asarar mai rai har aka cinye kwanakin wata da auren su Nazira. Har lokacin kuma ban yarda na je gidanta ba duk nacin aikar da take akan tana nema na. Ikilima ce take zuwa akai akai duk sadda ta je kuma akwai abin da zata bata ta kawo mini na ci ko na sha. Ga wasiku birjik tunda bani da waya duk da an kawo mini har uku amma Baban Marina ya ce "Baya son mu ri'ke waya. Duk yadda Yaya J yake nacin mu hadu gaba'daya na tsike zuciyata, domin yanzu haushinsa nake ji ba ka'dan ba. Kan dole ya koma makaranta tunda ya kammala sawes din da yake yi a Jos. Ina cikin wannan yanayin da na cire komai a raina nake iyakacin bakin kokarina wajen mayar da hankali a karatuna, sai dai ba wani fahimta nake sosai ba. Na dai yi sa'a zan iya karatu da rubutu. Na gama fahimtar ni din basirata a wajen kirkirar abin ado ne, misali idan na samu kan mace mai gashi zan b'ata lokaci na yarfa mata kitson da kowa sai ya ce "wow". Haka kuma duk gunjin gashi sai na kitse shi, zana adon lalle kuwa tamkar wanda aka bu'de mini ido. To yanzu da nake sake koyon kwalliyar da ake ya yi, ban jima da fara koyo ba amma har hannuna ya fara fa'da wa. Dan haka na daina takura wa kaina sai dai ina ta kokari dan na samu na ci jarabawar kammala sakandire. Ranar asabar tun safe nake ta murnar zan je gidan Nazira, tunda muka zo duniya bamu ta'ba rabuwa na lokaci mai yawa haka ba. Mutum uku kawai na yarda zan yi wa kitso, duk masu zuwa lalle kuwa ha'kuri nake basu, sai d'aya da take unguwar Nazira, layinsu d'aya domin Naziran ce ta turo mini ita. Dan haka na saka mata lallen a gurguje na barta da nufin ta same ni gidan Naziran na yi mata kitso a can. Da murna nake komai domin Allah ya sani ina son Nazira, ina samun farin-ciki idan ina tare da ita. Har Malaminmu na tarar yana dakon iso wa ta, ga abinci an shirya mini tamkar wata babbar bak'uwa ta mussaman. Spaghetti ce da miyar kifi, saboda ita ce favorite dina. Ga kuma zobo ya sha ha'di an fasa masa k'ank'ara, gefe kuma babbar kula ce shake da pure water da aka jefa masa k'ank'ara yini guda aka yi mini tanadinsa. Da farin-ciki yake taya amaryarsa marabta ta. Ta rungume ni tana k'walla da mitar ashe zan iya yin watsi da ita na tsawon wannan lokacin? Da dariya na ce "Babanmu ne ya ce "Ba zan dinga yi miki sintiri a gida ba". Malam Yunus ya ce "Ba wani sintiri idan kin so ma ki tattaro kayanki ni bazan gaza ba". Na yi dariya ina fa'din "Na gode da karamci, Allah ya sanya alheri". Ya fice ya barmu tare da cewa "Ameen Asiya". Tunda muka zauna hira muke yi, ba a gama wani zancen ba za'a sake, a kama wani. Na bata labarin yadda muka yi da Dada akan Malam Nata'ala. Ta dinga dariya tana tintsira wa tamkar ta samu tab'i. K'wallar dariya a idonta ta ce "Lallai ma tsohuwar nan, ke ce za'a bawa wannan tsohon?" Na taya ta dariya tare da cewa "To ba namiji ba ne? Kuma ai ta ga ya dace da ni ne, tunda ana kore mini duk wanda ya zo da niyyar aure na". Ta yi shiru ta ce "Kawai lokacin yin auren ne da saura, amma ba dai Alaramma ba." Muka shiga hirar duniya, muka ci abinci, muna santi a fili na ce "Na ji da'din ganinki Addah Nazi, Allah ya kara miki kwanciyar hankali, ya kawo zuri'a dayyiba". Ta ce "Ameen Yabi! Yanzu addu'ata mafi yawa taki ce Àllah ya kawo miki miji na gari". Na yi shiru. Ta ce"Baki amsa ba?". Idona ya cika dam da ruwa na ce "Baban Tsakiya ya lashi takobin duk wanda ya zo sai ya b'ata ni, ya fa'di munanan dabi'una kin ga kuwa aure ai zai yi mini wuya tunda kanin mahaifina ne yake fa'din munanan kalami a kaina." Ta yi shiru sai kuma ta ce ",Ba abin da yafi k'arfin addu'a Yabi! Fa'da kawai yake yi ba zai yi hakan ba". Na hade fuska na ce "bana son haka, wanne irin zance kike yi? Kema kin san gaskiya, zai yi abin da yafi haka in dai Alle Badamasi ne" Dariya ta subuce wa Nazira ainun, tana yi tana nuna ni da yatsa tare da ce wa "Ho Yabi". Tsawon lokaci muna hira tana ta bani labarin aure. Na dube ta na ce "Ya ya maganar da ake
Chapter 26 · 0% Book details