Sashe 67
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
bu'de masa durowar na ce "Ka ga inda na bar maka fa, bana son na bu'de maka kaya ne baka nan. Da sai dai ka dawo ka tarar na jere maka". Ya saki fuskar ya ce "To shike nan. Amma kin yi sallah kuwa?" Na ce "dama d'aya zan k'arisa wa sai na yi kafin na fara yiwa wata". Ya kalli agogo ya ce kusan uku saura, kina neman duniya baki yi abin da aka halicce ki yi ba? Yau ne rana ta k'arshe da za ki ji ana kiran sallah baki bar k'unshi kin yi ba". Na ce "To". Ya ce "Je ki yi alwallah ki zo ki yi sallar a nan". Na fita ban ce komai ba. Yayin da Tijjani ya cigaba da ambaton *RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAIYYA MIN KHAIRUN FAQIRUN.* Cikin farin cikin ganin tasirin addu'ar akan lamarin Yabi. Domin tunda ya ga al'amarin ta babu ragayya, babu soyayyar sa ko kad'an sai ya nace wajen yin wannan adduiakan al'amarin. Ya kuma fara ganin sassauco mai yawa. Mata ku rik'e wannan addu'ar sirrikanta yawa ne da shi. Na idar, na mike na kai masa abincin falo. Na dawo na gan shi kwance shame shame akan gadona. Gabana ya yanke ya fa'di. Saboda ya tube riga daga shi sai gajeran wando. Wani irin tsoronsa ya kama ni a dalilin duk jikinsa gashi ne. Kirjinsa kuwa yafi ko ina gashi. Ranar da ya tub'e a gaban su Hajiya da yake a kidime nake ban ga gashin irin haka ba. Na dauka iya kirjin ne kawai. Murya na rawa na ce "Abinci yana falo". Muryarsa a dashe tabbacin yana jin barci ko wani al'amari daban. Ya ce "Sannu da aiki". Na amsa da ce wa "Na tafi". "Tom, idan na ci zan fita, nasan ba son na lekoku zaki yi ba". "Na ce "Eh. To sai ka dawo din". Na saki labulen na je na cigaba da yi musu. Bai fita ba sai da la'asar ta yi. Sai wajen biyar na gama yi musu tunda na yiwa mutum biyu kitso a cikinsu. Ina gamawa na karkade jikina na wanke hannuna da sabulu. Na shiga kicin, na ga akwai donot sai kawai na dafa shayi na cika filas tunda akwai ragowar abincin rana da na yi Ana kiran magariba suka tafi bayan sun bani kudina. Na kirga na ga alherin da na samu ba ka'dan ba ne. Na ha'dasu na adana. Na yi sallah, sannan na shiga wanka. Nasan sai ya yi isha zai dawo. Amma abin mamaki har goman dare bai shigo ba. Haka kawai sai na fara jin zuciyata tana b'aci. Sai shad'aya saura ya dawo lokacin na gama fusata. Ya shigo ya ga ban ko kula shi ba. Na hau na yi suntum. Ya ce "Asiya na yi ta kiran wayarki a kashe." "Uhum" kawai na ce na kame bakina. Ya ce "Wallahi Maijidda ce zata haihu, haihuwar ta zo da matsala, zan taho, Dada ta ce na kai ta asibitin ta gano ta. To abin ba da'di, ganin mawuyacin halin da take ciki ya sanya Dada kasa barin asibitin, nima kuma sai na yi alkunya na zauna jiranta kada ta ce dama a dole na kai ta". Na ce "Sannu! zaman jiran matar da kake jiran a mutu ka aureta ta haihu ai wajibi ne. Na mike zan bar masa d'akin. Ya yi maza ya ru'ko ni. Ya ce haba Asiyata wacce irin magana ce wannan?" "Na ce k'arya na yi, baka fa'da ba?" Ya ce "Allah ya sauwake, ai na fa'da ne saboda kishin hure miki kunne da yake yi. Amma ni ko d'aura mini wata macen aka yi ba fincike wa zan yi na zura a guje ba." Na saki raina ka'dan. Ya ce "Dazun nan Dada ta gama ce wa yau watan aurensu goma da kwana goma. Cikin Ikon Allah gasu da y'arsu a hannunsu. Baki ji yadda ake ta saka musu albarka tare da diyarsu ba. Su tun a ranar suka manta da komai suka rungumi junansu". Ban kula shi ba. Maimakon ya yi shiru sai ya sake ce wa "Ni da na duba key holder din aurensu na lissafe sai na ga a lissafin bature watansu tara ba kwana uku ma". Kuka ya kwace mini, na ce "Na gode sosai da yarfe Tijjani". Ya marairaice ya ce "Mene ne abin yarfe Asiya? ". Na k'wace na koma gefe ina gunjin kuka. Ya numfasa ya ce "Amma kin san dai bana son kukanki ko?" Na zabura zan ce a gidan uwar wa? Ai ina tuna barin makauniyar da yake yi mini idan na fa'di hakan, na yi maza na ha'diye maganar na buge da jan tsaki da kara k'arfin kukan nawa". Shi da kansa ya a fahimci da zaginsa zan yi, sai kuma na fasa. Ya murmusa ya ce "Ban da abin Asiya Toro wai mene ne abin kuka saboda Allah? Ina ce da kin ji duk abin da ake fa'da miki da yanzu kina da cikin da ya yi daidai da kwanakin auren ki. Kina haihuwa sai dai a fahimci ke ma kin yi biyayya, kin manta da wanda ya manta da ke". Na mik'e na bar masa d'akin. Kai-tsaye band'aki na shiga. Na juyo zan rufe k'ofar na hango shi ya daga labule yana kallona. Sai da na ci kukana, na wanke fuskata na fito. Na ga ya koma ya bar ba'kin kofar. Na lallaba na shige falo na saka sakata na yi kwanciyata akan doguwar kujera bayan na kure gudun fankar. Ina kwance ba abin da nake so irin barci ya sure ni. Amma na kasa, zuciyata sai k'unci take yi. Ban san dalilin k'uncin ba, tunda na laluba ba haihuwar Maijidda ce ta dame ni ba. Jin shiruna ya yi yawa ya sanya ya biyo sawu. Ganin da ya yi k'ofar bayi a bude, ya sanya ya shiga d'akinsa. Nan ma wayam bata ciki. Ya nufi falo ganinsa a rufe, ga fanka na kad'awa da k'arfin gaske ya tabbatar da tana ciki. A fili ya furta "Bilhiillazi an jarrabe ni akan wannan azinanniyar yarinyar. Allah ka hore mini ita". Ya koma ya kwanta, amma barci ya yi masa tutsu. Idan ya tuna jaririyarsu Jabir sai ya ji tamkar ya wayi gari ya ga Yabi ta haifa masa tasa. Ya saki ajiyar zuciya tare da cewa "Wannan yar darun ma, ko sai yaushe zata bari ta girma, rimi rimi na fara shawo kanta, ta sake botsare wa tamkar me bugun aljan. Ya muskuta sai kawai ya tuno uniform din ta da ya karbo sai kawai ya murmusa sosai. Tare da ce wa "gobe da ikon Ubangiji zan rage wannan tutsun na ki na iyashege. Na riga na gaji da kallon ki tamkar hoto".