Sashe 70
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba. Ina gunjin kuka har barci ya wuce da ni. Ya jima yana kare mata Kallo. A ransa yake tambayar kansa duk barnar da ya yi a baya sai a kuma aka bashi kamilar mace wanda wani namijin bai ta'ba kusantar ta ba. Wata'kila kuma dan ya yi sahihiyin tuba ne. Ya tsinci kansa da fa'din ", Astagafirillah". Ya shinfida sallaya ya fara salla tunda ya yi alwallah da ya yi wanka. Sannan ukun dare ta gota. Ba abin da bai roka ba, inda yafi maimaita wa a addu'ar tasa sai a hore masa lafiya da arzikin da zai sauke hakkin ciyar da Yabi da sauran dawainyarta. Ya dinga ro'kon a cika zuciyarta da sonsa kwatankwacin yadda aka cika tasa zuciyar da kaunarta. Har aka fara kiraye kiraye sallah bai runtsa ba. Yana gaban Ubangiji yana godiya tare da neman rabauta. Sai da ya sallaci raka'aitainil fijir sannan ya tashi Yabi. A hankali ya jata jikinsa ya rungume. Ai kuwa yadda ta yi barci da kuka. Sai kuwa ta tashi da kukan. Ya kankame ta ya ce "Is ok kukan ya isa hakan. Mu je ki yi alwallah, bana son na tafi ban taimake kin yi alwallah ba." Cikin kuka na ce "Da ina da band'aki a ciki ai da ko da rarrafe ne zan je da kaina, ba sai an taimake ni ba". A hankali ya ce "Ko akwai ma zan taimaka miki. Ai nuna kulawa da yabawa a lokacin da ka samu alheri a tare da mutum abu ne mai kyau." Ganin bai tunzura ba, da na yi maganar bandaki sai kawai na rushe da kuka ina cewa "Wayyo bandaki a d'aki nake so ni ". A raunane ya ce "Haba Baby girl, kin shayar da ni farin-ciki, ai bai kamata kuma ki rikita ni irin haka ba. Ki yi ha'kuri, zan miki daki mai bandaki In sha Allah. Amma yanzu ki yi hakuri kin ji". A daddafe dai na yarda ya kai ni, na yi alwallah. Sannan ya tafi masallaci. Ana idar wa ya dawo, duk da yau ba zai je gidan burodi ba, da wucewa zai yi atisaye. Amma ko tashi ban yi akan abun sallata ba. Da rawar jiki ya sure ni, yana ce wa "Barka da safiya My Asi beauty." Ya ta'ba jikina ya ji zafi. Ya fita da sauri, jimawa ka'dan sai gashi ya dawo da kofi mai dauke da shayi, hannunsa kuma da Panadol. Da magiya da ban baki na sha shayin, na ha'diyi magani sannan ya rungume ni tamkar jinjira, muka kwanta. Barci muka yi ainun. Dan kuwa sai bayan shad'aya muka tashi. Shi ya dafa mana indomie. Ya saka kazar jiya a ciki. Da lallashi ya sanya ni yin wanka. Da na fito duk yadda nake ture shi, sai da ya ware tawul din ya shafa mini mai Na runtse idona a dalilin kunya da takaicin sun yi mini rubdugu. Amma shi ko a jikinsa sai yaba laushun fatata da k'oda farina mai kyau ne irin nasa. Ni dai ban kula shi ba. Asalima runtse idona na yi tunda ya riga ya tube ni, yana kare mini kallo tamkar tsohon maye. Yinin ranar bai fita ko'ina ba, sai masallaci wannan kam da azama yake fita. Hatta wayoyinsa kashe su ya yi. Yayin da ni kuma na lanjare, ko motsin kirki na k'i yarda na yi. Yan k'unshi kuwa sai zuwa suke yi. Da kansa ya ke fa'din bata jin da'di, kuma tafiya ma zata yi sai satin sama zata dawo. Dana gaji da jin wannan bayanin nasa, sai na ce shin ina zan tafi ne?". Kansa tsaye ya ce "Hutun lalle zaki tafi. Dan ba zai yiwu muna amarci ana damunmu ba." Na girgiza kai domin kuwa zan ga yadda za'a yi na sake yarda ya gana mini azabar da na sha a hannunsa jiya. Na tabbatar da gayya ya nuna mini rashin tausayi. Kamar jifa ya tafi sallah la'asar sai ga Hajiyar nan. Tana ganina ta gane yanayin da nake ciki. Ta dinga murna tana ce wa "To ko ke fa? Yanzu zai kara son ki, zai kara manne miki. Ke kuma ki yi juriya, ki yi biyayya shi kenan sai ki damk'e shi a hannun ki. Duk wanda zai musguna miki zaki ga ba zai yi k'ima a wajensa ba." Na kasa jure wa na ce "Amma gaskiyar magana ya yi mini yawa Hajiya". Na fa'da ina rusa mata kuka. Ta yi shiru ta ce "Ke kam ranar da zaki haihu da kallo." Ganin da gaske nake kukan ta sassauta ta ce "Iya na yau ne. Da zarar kin zama y'ar gari shi kenan sai rawar kai da falli, da zai dauki lokaci bai nemi ta'ba ki ba sai an ji kanku". Da kuka na ce "Allah ya kyauta na yi hakan Hajiya. Ni bana sonsa, amma an takura, an tursasa ni" Jikinta ya yi sanyi ta ce "ki yi ha'kuri da sannu zaki so shi ne. Kuma ina tabbatar miki kina sonsa ko ya ya ne. Tunda na ga kishi a idon ki ranar da ya yi miki wannan iyashegen." Na yi shiru ba dan na gamsu ba, sai dan ta wuce na yi musu da ita. Ta dinga rarrashina da nasiha. Har ta samu na nutsu. Ta tafi tana ta yi mini addu'ar alheri. Na sani kuma saboda kirkin da Gwaggo take yi mata ne ya sanya ta damu da lamarina. Ta fito da leda a jakarta ta miko mini. Ta ce ki dinga shan wannan, wannan kuma ki dinga shafawa. Na zuba wa magaunnan ido na tabbatar masu daraja ne,na manyan mata ne mussaman da na ga G.H.T. product ne. Ta ce "suna da kyau a wajen wata baiwar nake siyansa, ita ce ta zaba mini su, yayarku Sajida nake siyawa. Shekaranjiya na siya, jiya ta Sako mini a mota. FASEELAT da cika alkawari take, ga shi zata baka kaya masu kyau. Ga lambarta Dan nasan watarana zaki so ki sake siyansu" *07039269802* Na dai ce na gode, amma ba wani abu da zan yi akan Tijjani. Ta tafi babu jimawa ya dawo da leda a hannunsa. Ya zauna kusa da ni. Ya bude kamshin hadadden tsiren da ya yi shura a garin Toro ya bugi hancina. Yawun bakina ya tsinke. Amma na maze tamkar bai bani sha'awa ba. Sai da ya dinga ro'kona sannan na yarda na ci. Da daddare muka kwanta, bai nemi komai ba sai rungume ni da ya yi. Washagari da zai fita sallah ya ce zai wuce wajen aiki sai ya dawo. Na amsa da adawo lafiya. Na bi shi na sanya sakata. Sai wajen tara ya dawo. Shi ne ya tashe ni tunda k'arar kiran wayata da ya yi ne ya tashe ni. Yau bayan madara da milo har da k'wai guda hudu a ledar. Sai da ya yi wanka ya shirya cikin shudiyar shadda da ta sha guga, ga k'amshin turaren da ya fara sanyawa mai da'din kamshi ya baibaiye hancina. Yauma shi ya shiga kicin. Ya soyo kwan. Ya hado shayin da burodi ya kawo gabana. Muka karya. Sannan na yi nawa wankan. Da yake tsamin da jikina ya yi da sau'ki, kwalliya na yi mai sauki. Na kalli fuskata na ga ta d'anyace. Na sake yin fari. Shi kuma baya gajiya wajen kawo hannunsa jikina. Tun lokacin na gane jarabarsa ba k'arama ba ce. Washa gari ya yi sammmako ya fita. Duk tunanina gidan burodi ya tafi. Amma bai dawo ba sai gaf da maghariba. Kayan jikinsa ya tabbatar mini ba a wajen aiki yake ba. Ya mik'o mini ledar hannunsa tare da ce wa "Ga shi in ji Babarki." Ina jin hakan na fasa masa kuka har da dirowa daga kan kujerar. Ya tarairayo ni a gigice. "Saboda Allah fa kin girma Asiya. Yanzu ai kin wuce irin wannan kukan." Da kuka na ce "Amma na ce maka za ni, shine ka tafi babu sallama?" Ya sake rungume ni sosai. Ya sanya kansa a kan wuyana. Cikin rad'a ya ce "Sorry Asiyata. Daga yau bazan sake ba. Takanas ma zan shirya mana zuwa Bulkachuwa. Kwana nawa zaki yi?" A hankali na ce "Sati biyu". Ya lank'awasa harshe yana ce wa "Sati d'aya dai Sweetie". Daga hakan ya dinga kissing dina, har sai da na ji jikina ya amsa sosai, na zame na koma kan kujera. A hakan muka kwashe kwanaki hudu ban yarda an sake ba. A wannan ranar kuma ya rikice akan ya yi iya ha'kurin da zai iya. Kusan k'arfi ma ya sanya mini. Sai me? Gaba'daya sai na ji babu banbanci da na farkon wajen zafi da radadi, na rasa yadda zan yi. Na tattaro dukkan k'arfina wai akan na ingije shi, amma abu ya faskara. A wannan ranar kam har cizo na yi ta gasa masa. Amma bai sanya ya k'yale ni ba, sai da ya yi yadda yake so ya gama. Kukan da na yi a wannan dare ya zarta na ha'duwarmu ta farko. Hankalinsa ya yi mugun tashi. Ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya gaji da rarrashi ya zuba mini ido. Can ya nisa cikin rauni sosai ya ce "Asiya irin wannan bacin rai kamar wanda na yi miki fyade. Kin san k'uncin da nake ji kuwa. Kin san yadda kika tayar mini da hankali. Me zan yi miki kin rangwanta mini k'iyayyar da kike yi mini?" Jikina ya yi sanyi. Amma rad'ad'in da nake ji ya hana ni na daina kukan. Ya numfasa ya ce "Ki yi hakuri ko wacce mace da hakan ta girma." Da rawar murya na ce "Billahillazi bazan yi hakuri ka sabauta ni a banza ba. An yi na farko, an yi na biyu to kuwa ba za'a yi na uku da ni ba. Na riga na sani, baka iya yi da y'an k'ananun mata irina ba. Ka saba danne tima tima masu manyan halittu shi yasa nima kake gwada mini rashin imani kana ganin tamkar babbar mace ka samu". Jin ya yi shiru ya sanya na d'ago na kalle shi. Zuciyata ta tsinke a halin da na gan shi. Gaba'daya idanuwansa sun yi jawur tabbacin zuciyarsa ta b'aci ainun da kalaamina. Bai ce komai ba. Ya tashi ya bar dakin. Wanka ya yi, ya dawo dakin ya shimfida abin sallah ya tayar.