Sashe 85
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ce "A a kasan ni dakina daya ne. Zan dai rako ta, ko mene ne da safe zan dawo mu tattauna tunda dare ya fara yi". Ya yi shiru tabbacin bai gamsu ba. "Ka yi shiru Yaya Bulkachuwa". Ya ja gauron numfashi ya ce "Kunyar ki nake ji ne Ummilolo. Kada ki shiga wannan maganar. Ba ke ce zaki yi alkalancin nan ba. Domin ban dauki al'amarin da sau'ki ba". Ta sassauta ta ce "Ai tunda na gan ta na sani baka dauke shi da wasa ba. Amma tunda na yi maka waya ai sai ka mini lamini tunda ni da kai ai kasan tun fil'azal bata b'aci." Ya ce "To shike nan". Da walwala ta ce"Yauwa Yaya Bulkachuwa rabin raina na gode". Daidai lokacin kuma ku'din wayarta ya k'are. Ta ce "Ai bu'kata ta biya." Kafin ta yi mini magana, sai ga shi ya biyo bayanta. Tana dauka ya ce "Yi zaman ki Ummi ai ba zai yiwu ki fito b'akatatan a wannan lokacin ba. Bari na wakilce ki, na zo da kaina. Amma ki fa'da wa mijinki gobe, ki zo mu zauna". Ta ce "Na kuwa gode! Gobe da ikon Ubangiji da wuri zan zo". Ya ce "Na gode, ki gaida yaran namu". Ba a wani dauki lokaci mai yawa ba, sai ga shi ya k'ira ya ce ya zo. Ta raka ni har soron gidan sannan ta juya tunda k'ofar gidan nasu tamkar kasuwa yake shaguna ne reras gefe kuma teburan masu sayar da nama na gaba kuma masu kayan miya. A mashin dinsa ya zo. Na haye ba tare da na ce komai ba.