← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 146

Sashe 133

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

bamu biscuit din naka" Ya kuwa bude ya bawa kowa a hannunsa. Suka had'a baki suna fad'in"Mun gode, Allah ya fito mana da kai! Ya ce "Oya ku je office din Uncle ku ce masa zaku tafi ". Suka ruga a guje, suka nufi office din Yaya Ammar. Ba jimawa ya fito rik'e da hannuwansu. Ya kalle ni ya ce "Zaku tafi Yabi?" Na ce "Eh Yaya mun gode sosai." Ya ce "Dafatan dai kin fad'a masa ya dinga cin abinci. Ba kasafai yake cin abinci ba. Kullum sai na taho masa da abinci daga gida. Amma baya wani cin na kirki." Na yi murmushin kunya na ce "Ina ce wa "Na yi masa". Daga hakan muka taho ya bude mana k'ofa, har titi ya kawomu. Ya tarar mana Napep ya biya sai da ya ga mun tafi sannan ya koma. Muka isa gida na fad'awa Babah ya amince amma ya ce mu je tare. Ta ce "To sai mu je taren. Allah ya tabbatar mana da alheri. Ai kuwa har kofar gida Hajiyar nan ta zo ta kwashe mu ni da zugata. Tunda yara na hutu. Sai gamu daredare cikin fadar gwamnati. Aka baibaye mu da abubuwan motsa baki. Ashe Hajiyar nan mai magana da yawun matar gwamnace. Ba'a bata mana lokaci ba aka yi mana iso zuwa dakin da zamu yi kunshin. Zuciyata tana harbawa na fara yi mata. Sai addu'a nake Ubangiji ya ba ni sa'a na yi wadda zai yi kyau ta kuma yaba. Cikin nutsuwa nake yi. Tana yi tana kallona. Na kammala kunshi. Na fara yarfa mata kitso akan dogin gashinta da ya sha gyara na garari. Na kammala. Ta ce hadinaeta ya dauko matso mata dogon console mirror din da yake gefe. Ta ga yadda na yarfa mata kitso. Ta murmusa alamun ta gansu da abin da ta ga ni. Ta kalle ni ta ce "Kin kammala sakandire ne?" Na kasa amsawa domin na tabbatar k'ank'anta ta ya sanya ta yi zaton ko ban yi Kandi ba. Ta lalli Babah ta ce "Hajiya kar dai bata zuwa makaranta?" A tausashe ta ce "Ta kammala tuntuni. Ta nuna su Hamim da suka lafe a jikinta ta ce "wadannan ai y'aya'nta ne ba kanne ba." Ta dauki salati tare da fad'in "Wonderful. Yanzu ke ce uwar wadannan samarin?" Babah ta ce "Ita ce kinga Kuma sai da shekara biyu a daki sannan ta haife su. Tana shatakwaas ta haife su". First lady ta sake tsananta mamakinta ta ce "Yanzu shekarun yaran nawa tunda masu garin jiki ne ba irin ba ne tsaba" Babah cikin dariya ta ce "Shekarunsu bakwai." Ta sakki ajiyar zuciya tana kallona ta ce "Shekaru ashirin da biyar a wannan yarinyar. Ikon Allah. Tunda na ganta na ce kyakkwar yarinya Allah dai yasa tana zuwa makaranta ba iya sana'a take yi ba. Ashe ba yarinyace ainun yadda na zata ba, ban zaci ta cika sha biyar ba ma." Ta ce kin yi karatu ne bayan na sakandire?" A hankali na daga kaina na ce "Na yi N.C.E a nan college of education. Na karanta Home economics " Ta fadada murmushin ta ta ce "Da kyau! Kina aiki ne?" Na ce "A a takarda ta ta yi kyau amma Ubangiji bai kawo mini sababin samun aikin ba". Ta ce "Ai kuwa kin samu yarinya". Ta Kalli Hajiyar da ta kawo mu ta ce "A buga mata upper. A kai ta women center mafi kusa da ita ta dinga koyawa yaranmu sana'ar kitso da kunshi, hadi da tattalin gida." Daga yau kuma na bata mukamin costume din first lady". Cikin farin ciki Hajiyar take godiya a madadinmu. Ni kuma mamakin murnar da take yi ne ya sandarar da ni domin dai na jima ban ga mutanan da basu da Bakar Taadar kyashi da hassada kamar Hajiya mai magana da yawun matar gwamna ba. Baba ta shiga godiya ita ma. Haka nima na shiga godiya mai yawa, kna hawayen farinciki. Na samu daukaka ta sanadin sana'a. Hatta aikin da na samu arzikin sana'a ne ya janyo mini. Alhamdulillah na dinga ambato babu sassautawa.
Chapter 133 · 0% Book details