Sashe 3
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
sun kawo k'arfi, amma komai zasu kawo a boye ne, ita kawai zata amfana. Duk cikin yaran gidanmu tafi kowa shan wahala a gidan aure. Shi yasa take a ware, sai idan Yaya Rabi'u ya d'an figi wani abu ya kai mata a dalilin suma suna fama da rik'ewa Babanmu gidanmu. Rayuwar ta yi mana tsananin gaske, mahaifiyarmu ha'kuri take yi kan ha'kuri. Kuma wani abin mamaki da Mijin Yaya Ummi mai tarin dukiya ne amma fa baya iya ci, sai dai ya yi ta lissafin kadarorin da ya tara. Manyan yaransa sai fatan ya kauce su ci abin da bai bari sun ci ba suke. Gaba'daya tausayin Yaya Ummi nake ji, abubuwa sun yi mata yawa, ga tashin hankalin gidanta, ga azabar yan'ubancin da su Yaya Indo suke yi mata. Sun wareta, Yaya Salamatu ce mai sassauci kawai. Duk sadda ka je gidanta haka zaka ganta tamkar mahaukaciya. Wankau take yi, kamar me? yini take tana wanki. A hakan take samu ta wanke kayanta da na yaranta, ta kuma samu ku'din da zasu ci abinci da rana. Duk da dai bashi yafi yawa, sai ta yi wanki sau nawa ba a biya ba. Na kan yi mamakin yadda mutanen yau suka shagala da fa'din Annabi (S.A.W.) na cewa "Mafi adalcin mutum shine Wanda yake biyan hakkin Wanda ya yi masa aikin wahala kafin guminsa ya bushe. Amma a wannan zamanin sai mutum mai wadata ya bawa miskini aikin wahala amma biyansa hakkin wai sai ya zama bashi, abin kaicon ma idan an yi masa aikar a bayar da ku'din nan, sai ya zama laifi. Mace ma'aikaciya sai ta bari ku'din mai wanki, ko markade, ko kuma mai dakan hannu ya taru a kanta. Ba tare da yarjejeniyar sai k'arshen wata zata biya ba. Anya kuwa muna son ganin dai-dai jama'a? Wannan wahalar data taru ta yi mana k'awanya ya sanya na mayar kitsona na ku'di. Domin tun daga alhamis idan na fara k'itso har lahadi, amma ba wanda zai cire ko da sisi ya bani a cikin matan gidanmu da duk kusan sati nake yi musu kitson su da y'ay'ansu. Kuma na sani hakan baya hana su karbin ku'din kitson a wajen mazajensu, ko iyayensu. Bisa shawarar Nazira na daina yiwa kowa kitso sai ta biya. Iya y'an k'ofarmu kawai nake yiwa kitso kyauta. Mama kuwa bata yarda ta ba ni kanta dama. Amma ina yiwa Inna da Gwaggonmu. Da kuma yan'uwana na k'ofarmu. Ai wannan bijirewar da na yi akan sai an bani ku'din kitso ya sake jefa tsana a tsakaninmu, domin duk inda Mama ta zauna sai ta ce "Uwarta ce ta kitsa mata, me za'a yi da irin wannan haihuwar a ce ba zaka bari aci arzikinka ba?" Iyayenmu maza da suka san suna biya basu dauki al'amarin a wani abu ba. Domin suna k'yashin a ce mu d'in muna da mamorar da zamu yi musu alfarma. Domin fa'di suke yi "Idan ku'di ne ku bata kudinta daidai da yadda na waje zasu biya ta, ko kuma daidai da wanda idan kun je wajen bare zaku bayar. Ita ce bata gaji arziki ba". Yayin da muka k'udire a ranmu ni da Nazira ba wanda zai sa na yiwa yaransa ko matarsa kitso akan dole domin suma basu taimake mu ba, dai-dai da ku'din islamiya da bai taka kara ya karya ba, basu ta'ba ha'da mu da y'ay'ansu sun biya ba. An sha koro mu da sauran k'annenmu, akan ku'din islamiya. Yayin da sauran yaransu basu da wannan matsalar. Idan zamu yi wata a zaune, Mahaifinmu ko iyayenmu mata basu samu sukunin biya ba, ba wanda zai dube mu. Dada kuma ba zata ce wane biya wa yaran nan ba. Ita kanta ta manta irin da'din da Babanmu ya jiyar da ita. A yanzu kam ta mayar da shi da dukkan ahalinsa tamkar wasu barori a cikin ahalinta. Tarin Baban kasuwa ya fi maganar Babanmu sau dubu. Tunda shine yafi kowa rufin asiri, sai Baban tsakiya. A batun soyayya kuwa kowa shaida ne Dada bata ha'da lamarin Yaya Anwar, da Tijjani da kuma Nasiba da kowa. Sun fi kowa lasisi a gidan, gasu dai ba y'an gidan ba ne tunda iyayensu mata ta haifa. Amma sun fimu gata da gadara a gidan. Yanzun nan Dada zata hau ihu matu'kar aka ta'ba guda a cikinsu. Sai yaran Baban kasuwa, sai na Baban tsakiya. Hakan dai hawa hawa abin yake. Canjin da nake samu a kitso ba k'aramin taimakona yake yi ba. Haka Gwaggo tana yin kokon safe, muna samu mu sha a ciki, har watarana a aikawa Yaya Ummi. Asusu na siya nake tura dan wani abu, domin ina matu'kar jin haushin yadda mu da gwaggonmu muke koma baya a gidan. Yaranta maza an d'ora musu nauyi mai yawa. Yaya Salisu ne kawai ya yi aure, shima ba wai wadatar ne da shi ba, aikin gini yake yi duk da ya yi karatu amma aiki ya yi wuyar samuwa tunda babu hanya. Su Yaya Rabi'u kuwa koami na gidan sune, Mama fa'di take ai sune maza, sune zasu taimaki ubansu, ga karatunsu su suke daukar nauyin kansu. Dan haka Gwaggonmu bata samun komai, amma idan an nutsu za'a fahimci kowa a kofarmu yana cin arzikin yaranta. Duk yan dakinmu ni ce mai tsiwa, ban dauko sanyin halin uwarmu ba. A tsaye nake kan kafafuna cak, haka zuciyata bata daukar raini. Sai dai kuma bani da kullaci, ina da saurin afuwa. A duk sadda na kalli Gwaggonmu da Yaya Ummi sai na tsinci kaina da yiwa kaina da Iklima addu'a samun miji na gari mai wadata, ko muma ma shiga sahun masu mutunci. Tun kafin hakan kuma sai Ubangiji ya hore mini iya yarfa kitso. Duk wata matashiya yar kwalisa a yankin nan ni ce mai yi mata kitso. A hankali sai na fara gwada lalle. Nan da nan sai Ubangiji ya sake haska mini. Layi ake yi mini na kunshi da kitso duk satin duniya. Muka fara dan warware wa, domin muna samun yan kuda'den yin bu'katar yau da kullum. Hatta Yaya Ummi ta d'an samu sau'kin matsatsacin da take ciki. Domin duk sati sai na cire mata wani abu. Da ku'din asusuna ya yi auki na fasa na siya mana kayan kwalliya masu sau'kin ku'di ni da Ikilima da Nazira, har ma da Ubaidan Innah. Sai kuma na sake siyan wani na k'udire niyyar dinki zan yi mana idan kudi ya taru. Tsawon dauki lokaci ina zubi, kafin na samu na yi mana y'an suturu ni da Iki. Ai Mama tana ankara da y'ar nutsuwar da muka fara samun kanmu a ciki, sai ta tayar da ballin sai na bar kitso, domin gashi yana yawa a gidan, ba dama ta zubo abinci, zata yi ta ganin gashi. Ko ina gashi ne, ta gaji da wannan k'azantar. A wannan karon Babanmu ya yi jarumtar cewar ba zai hana ni yin sana'a ba, tunda shi da kansa ya sani ba k'aramin rufa masa asiri sana'ar take yi ba. Kusan kullum sai na ba shi naira dari hud'u. Maganar maganina kuwa idan ba ni da lafiya, na dauke wa kowa. Dan haka sai muka fara saje wa da su Maijida. Tunda muma yanzu muna samun yan suturu babu laifi, duk da bai kai nasu daraja ba. Idan akwai abin da ya yiwa Mama tarnaki rashin kintsuwar Yaya Musa ne. Gashi dai shi ne babba, amma gaba'daya ya lalace, ya zama d'an iska, hakan kuma yak'i ya zame mata izna, a kullum cikin aibata yaran da ba nata ba take. Ta kuma gasgata hannu aka sawa d'anta, da kuma bakin mahassada. Ta kasa fahimtar rayuwa har yanzu. Tsabar kyashinta ta hana ya'yanta mata su tallafawa Babanmu da d'an abin da zasu iya . Kullum fa'di take ai hidima ta y'ay'a maza ce. Dan haka komai yaranta mata zasu kawo gidan to nata ne, sai ko idan dafaffe ne sai ta samma wadanda take so, wadanda bata so kuwa ko ta yi babu. Sai nake mamakin idan tana habaicin ku'din kitson da nake kar'ba, wai Gwaggo ta kasa bari a mori haihuwarta, ko ita wa ta bari ya mori tata haihuwar? Ko Babanmu da ya yi mata hidimar yaran ba dai tasa su kawo masa wani abu na tallafin gida ba tunda yana da k'ananun yara. Idan ma sun yi hankalin kawo wa to fa ita ce a hakku a kan kayan, ta dinga gadara kenan duk ba wasu kaya masu yawa ba ne, tunda dai ba wai ku'din ne da su ba, rufin asiri ne kawai. Sai nake mamakin wai mene ne manufarta ne? Da na kasa gane wa sai na ha'kura, amma hakan ya ja hankalina har nake sha'awar yin bincike da nazari akan gidan yawa mai dauke da mabanbanta iyalai. *GIDANMU ne kawai kwamacala ta dabaibaye shi?* *A GIDANMU ne kawai ake yin kasafi irin na kashin dankali ma'ana na sama ya danne na kasa?* *A GIDANMU ne kawai ake mayar da babba k'arami saboda ba shi da wadata ko kuwa?* *A GIDANMU ne kawai ake ta'ba yan ubanci ko kuwa?* *Ba k'aramin caji kwakwalwata take yi ba dan neman sahihohin amsoshi wadannan tambayoyin*.