← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 146

Sashe 114

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

***
A hakan na cinye shekara d'aya da fara karatun. Na fara nisa a cikin ta biyu. Tun bai shiga jikina ba, har na sanya shi a raina na mayar da hankali, hakan ya faranta ran Tijjani tunda ban sami carry over a shekarar farko ba.
A hankali sai nake ganin Tijjani na d'an sauyawa. Sauyin bai shafi mu'amalata da shi ba. Amma yana yawan zuwa Toro. Kusan kullum sai ya je ko da ba zai je Jos ba.
Ina ta jin rade radin yadda yanzu yake zama ya yi hira da Nasiba da har yanzu bata yi aure ba. Sai ma kasuwanci da take yi sosai. Kayan gwanjo take siyowa a Jos masu kyau. Har ce mini aka yi yana karbo mata sakon kayan.
Tun ina daure wa ina dauke kai daga abubuwan da nake ji har na fara sike wa.
A dalilin kullum dare sai ya fita k'ofar gida ya shafe lokaci mai yawa yana waya. Haka nan kaffa kaffa yake da wayarsa abin da baya yi a da. Da na yi masa magana sai ya balbale ni da fad'an na saka masa ido ne. Ban da hakan me yake yi mini? Dan ya yi wayar da bata shafe ni ba a waje shine laifi?
Na kasa bude baki na ce komai domin ba ni da hujja.
A hankali muka fara samun tazara a tsakaninmu. Na sani bai canja daga kawo mini abubuwan abincin ko na bukata ba. Bai canja a hidimar makaranta ta ko hidimar y'aya'nsa ba. Sannan bai canja mini a mu'amalarmu ta auratayya ba. Har yau din nan a cikin mararina ya ke. Duk da ni din ma kullum a cikin gyara kaina nake da ingantattun kayan Surayya da basu da illah ga lafiya. Sannan ina amfani da kayan g.h.t na FASEELAT.
Amma yawan wayar da yake yi da sintirin zuwa Toro, da sabunta mu'amalarsa da Nasiba da nake ta jin rade radinta, tana matukar ci mini tuwo a k'warya. Na rasa wa zan fad'awa ya fahimce ni. Domin da na fadawa Gwaggo ce wa ta yi "Ina ruwan ki da jita jita? Sannan ai bai zai yi aure bai fada ba. Ki rage kishi mussaman kan abin da baki gani ba, zato ne da shati fadi kawai.
Haka na hak'ura na cigaba da zuba ido tare da hak'uri. Amma sai nake ta d'ad'are wa da shi. Ko a shimfida bana wani katabus shi zai yi kidansa da rawar sa. Wani lokacin ya tambayi dalilin sauyin nawa cikin kwanciyar hankali. Bana iya ce masa komai sai dai na ce "Ban canja ba, babu komai".
Wani lokacin ya ce "Allah ya sauwake. Wani lokacin ya yi tsuka ya juya mini baya tare da fad'in "Zan yi maganin wulakanta ni da kike haka siddan Asiya."
Gabadaya mun koma muna ganin laifin junanmu a dalilin kowa bai gamsu da kokarin d'an-uwansa ba.
A haka na kammala aji biyu. Twins sun yi wayo sosai tunda sun shiga shekaru biyar. Wani irin wayo da fikira a cikinsu tamkar wanda suke siyo dabara a kasuwa. Gabadaya sun juye ubansu sak. Ga shi suna girma suna sake zama iri d'aya. Ni da kaina ina gane su ne ta halayyarsu. Domin har yau din nan Hanif mai hakuri ne, magana bata dame shi ba. Sabanin Hamim d'an hayaniya kuma mafadaci irina. Har yanzu bai bar kuka ba.
Sau biyu ina yin bari. A yanzu haka ina zuwa ganin likita a dalilin hakan. Na karshen nan da na yi Bulkachuwa ce mini ya yi "Ina sane nake bararwa tunda na saka masifa a raina. Ya rasa me yake mini da nake gana masa azaba haka.
Kallon sa na yi kawai. Ba tare da na tanka masa ba. Domin na riga da na saka a raina ce wa hakurin da aka yi ta jaddada mini na yi a lokacin aurena. Yanzu ne zan fara shi. Dan haka na rungumi addu'a, y'aya'na da karatuna hadi da sana'ata. Na tattara shi na zuba masa ido yana yin almuransa yadda yake so.
Muna cikin wannan zaman na fallasa tafi yabon yawa. Kamfani suka sake biyansa kudin hayar filinsa tunda shekaru uku ta cika. A wannan karon har da kari akan wanccan. Duk yadda muke jin haushin juna sai da ya zauna ya mini bayanin komai. Ya kwashe mu ni da yara zuwa Kano. Ya yi mana siyayya. Muka kwana biyu, muka juyo da kaya niki-niki.
Yara na baya duk barci ya sure su. Ya sassauta murya ya ce "Zan canja motar nan. Zan siyo wacce ta fita."
A takaice na ce "Allah ya kara budi".
Ya zarce da fad'in "Ana mini cinikin wani gida mai kyau a Toro zan siya".
Nan ma a gajarce na ce "Allah ya sanya alheri."
Daga haka bamu sake magana ba har muka iso Bauchi. A dalilin ya fusata duk yadda ya kwashe ni ya mini hidima bai sa na saki raina ba. Ni kuma ina masa kallon a yanzu yana ganin yafi karfina tunda yana samun duk abin da yake so. Kasuwa tana gara masa ainun. Shi yasa gabadaya yake neman bijire mini. Duk abin da yasan bana so a yanzu baya jin komai ya yi a gabana. Jiya da daddare ina jin sa a waya yana ce wa "Ga ni kike ba zan iya bata wayar ba? Wai me kika dauke ni ne? Bari ki ga na sayi gidan da zan saka.ki a ciki, ki ga yadda zan fito da maganar gabadaya. Namiji dan zai k'ara aure sai a ce ba zai iya ba? Mata nawa ne a gidansu? Nima kuma mahaifina biyu gare shi. Da ba'a karin aure da ba'a haife ni ba, tunda tawa gyatumar ce amarya a gidanmu ".
Dai dai nan na fito a bandakin. Nan da nan ya katse wayar tare da ce wa "Zamu cigaba da tattauna wa da safe". Ya katse wayar tare da kashe ta gabadaya.
Tun lokacin na sake karaya da shi. Tabbas aure yake nema kuma a Toro tunda har zai sayi gidan da zai saka ta a can.
Sannan tun yanzu na dame ta tunda har tana masa shaguben tsorona yake ji ba zai iya aure ba. A raina na shiga yiwa mutanan da suke ganin Bulkachuwa tsorona yake ji Allah ya isa ta fi goma. Domin a yanzu da kowa yake mini kallon ina cikin rufin asiri da jin dad'i a gidansa. Ni kad'ai nasan me nake fuskanta. Nafi samun nutsuwa a lokacin da ba shi da ko sisi. A yanzu ba abin da bani da shi a gidan na cima, tunda ga kan nama, kifi, madara, dankali, doya, bare kuma kayan miya, da duk nau'in kayan abincin. Ruwa da lemo basa yanke wa. Komai baja baja yake ajiye mana. Haka sutura ta wadace ni ainun. Amma kuma bani da nutsuwar da nake da ita a da. Ba ya shiririce mini kamar lokacin baya. Dan haka sai na fi son waccar rayuwar da kowa yake mini kallon tausayi.
Babah ta kawo mana ziyara. Ta dinga rarrashi tare da shan cikina akan matsalar da ta sanya bana girma, da na fara murmure wa zan sake tsomare wa. Ban yarda na ce komai ba, saboda nasan ba zata yi masa ta dad'i ba, idan ta tafi kuma ya hau sababin ina had'a shi da uwarsa duk da ba komai yake mini ba, ni ce nake zaluntarsa.
Da kanta ta fahimci a yanzu ni da shi kowa harkar gabansa yake yi. Gamu nan ne dai, babu warkajabi irin na da, babu nishadi a tare da mu duk da ba gaba muke yi ba.
Da daddare bayan yara sun yi barci ta zaunar da mu tana bincikar matsalarmu a kokarin ta na son ta sulhunta mu ta dinke barakar da kullum take sake bunk'asa a zukatanmu ba tare da mun ankara ba.
Tsawon lokaci ban iya bude baki na ce uffan ba. Ta hakura ta koma kansa. Cikin kwanciyar hankali ta tambaye shi me yake faruwa. Ai tamkar gudawa haka ya b'arke da zano laifukana. Ya kaurara murya ya ce "Gata nan gabadaya ta ki sarrafuwa mini. Ko dariya take yi da y'aya'nta idan na zauna a cikinsu ta gintse dariyar ke nan. Idan tana zaune a falo na zauna sai ta san abin da zata kirkiro da zai sa ta tashi ta bar mini wajen. Ba zan mata abu ta nuna ta ji dad'i ba, zata dai ta ce ta gode a takaice. Gabadaya ta fitini kanta ta kuma fitine ni. Gara ma da Allah yasa kika fahimci masifar da d'orawa ranta. Gata nan ta fada miki mene ne bana yi a gidan nan da zata kwarzabe mu irin haka. Yanzu idan na fita har fargabar dawo wa nake yi tsabar yadda take shagulatin bangaro da ni, da dukkan al'amarina. Ban sani ba ko miyagun kawaye suke hure mata kunne. Na tabbatar cikin da baya zama idan ta samu ma akwai dalili, idan an tsananta bincike, tunda ta riga ta taurare mini, ita tasan me take nufi da zaman".
Na yi k'asa da kaina ina hawaye mai cin rai. Zuciyata tamkar ta fad'o k'asa idan yana danganta b'arin da nake yi ni ce da alhakin hakan.
Babah ta dawo kaina cikin tausasa harshe ta ce "Haba Yabi me zai sa ki abin da baki yi a da ba, sai yanzu da kike girma, kuma Ubangiji yake ta yi muku Alam nasharaha. Me zai sa ki yi haka?"
Na fashe da kuka mai ciwo na kasa ce wa koma a dalilin yadda nake gunji da shessheka mai nauyi.
Baba ta yi zuru tana kallon yadda nake kukan.
Ta koma kansa ta ce "Kai ne kake musguna mata, kai ne ka janye dukkan rarrashi da tarairaiya a tsakaninku saboda kana ganin kana ajiye mata komai na bukata."
Ya yi shiru. Ta sake juyo wa gare ni ta ja ni zuwa jikinta tana bubbuga bayana cikin rarrashi. Tsawon lokaci ina kuka su kuma ba wanda ya iya ce wa komai. Sai da na yi kuka sosai, domin tsawon lokaci ina ta son na yi ban samu inda zan yi ba. Shi yasa yanzu na yi shi son raina. Sai da na nutsu sannan ta d'ago ni ta ce ",Fada mini damuwowinki Yabi". Na ce "Babu komai Babah". Na saci kallonsa na ga ya kidime sosai domin ya sani idan har na ce babu komai to kuwa abin da yake raina mai nauyi ne. Irin kukan da na yi kuma ya saka shi zullimi.
Babah ta hau fad'in "Wato ban isa ba ko Yabi? Na zaunar da ku dan na ji matsalalolinku amma kin ce babu komai alhalin ko makaho idan ya ji irin kukan da kike yi yasan kina cikin bacin rai."
Idona ya sake cika da hawaye na ce "Wallahi Babah ba isa ne baki yi ba, ke ma kin san yadda na dauke ki. Kawai ban san me zan ce ba ne. Abin da na fahimta kawai yanzu ya fi k'arfina ne. A yanzu ya samu damar da zai auro daidai da ra'ayinsa, irin wacce ta dace da shi. Ai dole na ga komai! Dole komai zan yi masa ya zama laifi, dole ya janye dukkan tausayi da sassauci a tsakaninmu, Tunda bana birge shi. Yana zaune da ni ne a kan dole, gane hakan da na yi ya sanya na koma gefe dan na ba shi dama ya yi komai tunda Allah ya ara masa damar."
Na goge hawayen da ya zubo mini da hijabin jikina.
Babah ta yi shiru tana kallonmu tare da nazari sosai.
Ta kasa gane waye yafi gaskiya a tsakaninmu. Amma kalamaina sun yi matukar dukansu gabadaya, shi kansa kallona yake yi ya kasa ce wa uffan.
Karshe dai Babah ta rinjayar da gaskiya a tare da ni.
A sanyaye ta ce "Ban yi mamaki ba. Domin mafi yawa maza haka suke yi. Da sun samu wadata kuma sai wulakanci ya biyo kan wacce aka sha gwagwarmaya da ita. Ba ko wanne namiji yake yin hakan ba, amma dai masu yin sun zarta marasa yin yawa. Sannu Yabi!"
Ta fada cikin wani irin yanayi, mai wuyar fasaltawa.
Kalaman Babah suka sake fadada zullimiin da yake ciki.
Murya babu amo ya ce "Babah kada kalamanta su rude ki, ki bata lasisin cigaba da gasa ni da ruwan sanyi da take yi. Ubangiji ya bata iya sarrafa harshe. Wallahi ita take k'warata. Satin da ya wuce muka dawo daga Kano. Na kuma shirya mana tafiyar ne dan mu samu sauyin muhalli watak'ila hakan zai sa ta huce daga murdewar da ta yi. Jikina na rawa na dinga siya mata komai na ga ni. Amma Wallahi yadda kika san mugun abu na yi mata haka ta sake botsare wa. Tunda muka dawo ta sake taurare wa. Wai a ce yarinyar mace kankanuwa kamar wannan ta iya BAK'AR TA'ADAR gaba da miji haka siddan?"
Na kalle shi na ce "TA'ADAR da baka yi ta sharri a baya, yanzu so kake ka k'ware a kanta. Bana gaishe ka? Masharranci kawai!
Babah ta ce ",Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Ashe kina iya zagin miji Yabi? A gabana kika ce masa masharranci? Ta jijjiga kai tare da ce wa "Tun baku je ko ina da zaman auren ba kun fara zaman da babu mutunci a ciki?"
Ta dinga sababi ta inda ta shiga bata nan take fita ba. Gabadaya ta hadamu ta ki yarda da gaskiyar kowa.
Ta kalle ni ta ce "Da kam ni kad'ai nasan wulakancin da zan yi masa a kan abubuwan da yake yi miki. Amma tunda na gane ba ki d'auki tarbiyar gidanmu ta barranta daga zagin mijin aure ba. To ai bani da ta ce wa. Domin na gane dukkanku ne baku da mutunci, dukkanku ne kuke son yiwa auren tawili".
Ni da danuwana kuke son ku tozartawa, ku kunyata, ku jefamu cikin bak'in ciki da zunden jama'a ".
✍️
Chapter 114 · 0% Book details