Sashe 30
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bata zo hannuna ba". Na girgiza kai na ce "Ba za'a kai ga hakan ba". A hanzarce ya ce "To ki huce da ni, ki bani damar auren ki". Hawaye na zuba na ce "Na baka Yaya J. Nan da sati biyu ka fito, idan har ya wuce baka bayyana a gaban Baban Tsakiya da Baban Kasuwa da nufin ka je neman aurena gabansu ba, ka tabbatar magana ta k'are a tsakaninmu ta soyayya har abada, na kuma baka dukkan damar da zan iya, sai dai ka sani ba zaka ha'da ni zama da ita a gida guda ba". Ga mamakina sai gani na yi ya zube a kasa yana sujjada. Ya dago ya ce "Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Zaki ji sakona kuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. Sannan na miki al'kawarin a Bauchi zan nema miki inda zaki zauna kafin na samu halin gina miki naki gidan". Ya tako mini har titi ya tarar mini Napep ya biya, na tafi yana d'ago mini hannu cikin matsanancin farin-ciki. Ni kaina wani irin shauki ke fizgata mai danne dukkan bacin rai. Na manta k'iyayyar da Baban Tsakiya yake mini azima ce. Sannan Baban kasuwa ba yadda za a yi ya goyi bayan ayi wa diyarsa kishiya da ni. Amma dukkanmu hankalinmu ya gushe duk da ni din gatse na yi masa, amma TASIRIN soyayyar da nake yi masa ta taso mini haik'an ta saukar mini da farin-ciki mai tsananin gaske. Har nake fatan al'amarinmu ya kasance. Na isa gida na ci abinci na yi sallah na hau kitso tunda mutum uku na tarar suna jirana. Da yake a cikin nisha'di nake kafin ka ce kwabo duk na kitse musu. Hatta Gwaggo sai da ta fahimci irin walwalar da nake ciki, rabon da ta ganni hakan tun komai bai tabarbare mini ba. Ina idar da sallar isha na nufi wajen Dada. Na tarar ta idar da sallar ita ma tana jan dogon carbinta. Ni da Nasiba muke hirarmu, akan makaranta. Dada ta shafa addu'a. Muka gaishe ta ta amsa da walwala a dalilin yanzu shiri take yi da ni tunda tana samun alheri a dalilina. A sanyaye Nasiba ta ce "Kin daina d'ora mana karatu dai Dada". Ta murmusa ta ce "To kuwa yau zamu yi. Zan d'ora muku addu'ar da idan kuka lazumce ta babu ku babu yunwa ila yaumil k'iyamati, ina nufin duk tsanani, Ubangiji zai yassare muku abin da zaku ci". Nan da nan na nutsu domin idan na ji ingancinta na d'orawa Yaya Ummi domin ita kam tana wahala kafin ta k'oshi. Ta gyara zama ta ce " *ALLAHUMMA RABBANA ANZIR ALAINA MA'IDATUN MINAS SAMA'I TAKULU LAANA IDDAL LI AUWALI WAL AKIRI...*" Da sauri na ce "Ai mun haddace tuni, a cikin suratul ma'ida take Ashe haka take da falala Dada". Ta washe baki ta ce "Ai wani bajimin Malami ya tabbatar mana matu'kar zaka biya wannan addu'a to haularka ba dai su rasa abinci ba bare kuma kai da kake bitar ta". Na 'kyal-k'yale da dariya domin ni na dakatar da ita ne saboda kurakurai da na ji a ciki. Tunda ba yarda zata yi na gyara mata ba. Ta ce to "Kun ga ni, ni da ku ne anan zan d'ora muku wata muhimmiyar addu'a, sadakar da zaku bayar ku yiwa Annabi salati, ku nema wa Shehu karin karama". Cikin zakuwa muka ce "To". Ta yi kasa da murya ta ce " ku dimanci *Ya ladifu* Idan kun yi dari ba daya a cikon na dari ku rufe da fa'din *"Allahu ladifin bil ibadihi, yar-Razaku man ya shaa'u Wallahu Qawiyin Azim*". Karon farko da Dada ta biya karatun da babu kuskure, da haka na dage nake ta biya wa a zuwan koyo nake yi, ita kuma sai fa'di take, tana sake gyara mini". Muka kammala tana jaddada mu ri'ke adduoin nan falalarsu ta kai matu'kar shahara.Ya ladifu kundin sirri ne, gashi babu wahalar fa'da. Na maze domin tsokanar ta zan yi, dan na ga reactions d'inta. Na ce "Dada ki daina jan carbi fa, babu kyau Annabi ya ce mu yi da yatsun hannunmu domin su mana shaida ranar gobe". Ta b'ata fuska kamar ba zata yi magana ba, sai kuma ta kufula ta ce "Asiya tun kafin a haifi Ubanki nake jan jarbi, duk wani sabon addini da kuke son kawo wa na raini Wallahi ba zai yi tasiri a wajenmu ba". Nasiba ta fashe da dariya yayin da nake jira ta tara mini gayya irin wanda ta mini watannin baya, amma na ji muk'us. Na jijjiga kai a raina sai fa'di nake "Allah ka sake bawa Yabi tsaron da ba za'a dinga tozarta ta ba." Ta ja robar maganinta da Honarabil ya kawo mata na warwarewar gajiyar tsufa da kara kuzari. Sai kuma na daidaita siga da bugawar zuciya duka daga kamfanin G.H.T. Na murmusa ina tuna a wajen FASEELAT ba zai kai kudin da na ga ni a manne a jikinsu ba. Na Santa a littafin Guduyo. Nemi dukkan nau'in kayan ght daga gare ta cikin RANGWAME. *07039269802* Muna cikin haka sai ga Yaya J. Ya sha kwalliya da wani farin yadi, d'inkin ya zauna masa sosai. Ga kamshin turaren Dagmar ya baibayemu. Cikin farin-ciki Dada take fadin maraba da Jabiru angon Maijidda". Zuciyata ta buga da k'arfi, shi kuma ya dan diriri ce. Ya waske da ce wa "Angon Dada dai, ai ke ce ta karfen". Ta yi dariya ta ce "Yaudara ke nan." Ya gaishe ta ta amsa da walwala tana tambayar amaryarsa. Ya bata amsa da ce wa"Tana lafiya a gajar ce. Ya shige cikin dakinta yana cewa "Zo mu yi sirri Dada". Ta rarrafa ta bishi domin kuwa mutuminta ne baya rabuwa da kawo mata tsire da turare. Ita kuwa duk wanda zai mata ungo tana mutunta shi. Muka ci gaba da hirarmu wacce galibi Nasiba tana fa'da mini ciwon da take ji akan sharewar da Bulkachuwa ya yi mata. Fa'di take "Dan Allah laifina ne? Inda ya fahimce ni, da ya k'arfafa soyayyarmu ai komai za'a mini bazan kula kowa ba, amma daga maganar fatar baki ya d'ife, ya ce kada na kuma shiga sha'aninsa. Da yana sona ba zai yi irin wannan fishin ba." Ta fa'da k'walla na zubo mata. Jikina ya yi sanyi ainun domin kuwa Bulkachuwa ya riga ya yi rantsuwar ya yanke hulda da ita. Kamar daga sama na ji muryar Dada cikin karadi tana cewa "Ina! Jabiru ka zo da *BAK'AR TA'ADAH* Mai wahalar tabbatuwa, ta ya ya zaka ha'da mini jikoki kishi? Dama kuma ba jituwa suke yi ba. Ha'kuri zaka yi da Yabi domin tuni ta samu miji ita ma, dattijon arziki irin albarka." A sanyaye na ji yo shi yana ce wa "Idan ban samu goyon bayan ki ba akwai matsala Dada. Kin sani Yabi nake so tun fil'azal. Amma saboda na yi biyayya ya sanya na karbi auren Maijidda. Yanzu da nake son na cike wanccan burin nawa ba sai a taimake ni ba?". Ya dinga magiya, tamkar zai fashe da kuka. Cikin kad'uwa ta ce "Jabiru ka zo da babban al'amarin da yafi Dutsen dala nauyi. Bana jin iyayenku ma zasu amince maka, ka bar maganar nan tun baka tono wani bacin ran ba". Ba shakka ko nauyi ya ce "Ba zan barta ba Dada! Domin da zan iya barinta da ko ke baza ki ji ba. Idan ba zaki taimake ni ba, to ki mini adalci kada ki b'ata al'amarin a gaban iyayenmu". Ta ce "ita Yabi ta gamsu zata aure ka ka had'asu da Maijidda?" Da sauri ya ce "Ina da tabbacin soyayyarmu ba zata yi zangwayenwar da babu alfarma ko fahimta ba, ban tuntu'beta ba, amma ina da yakinin ba zata juya mini baya ba". Tsawon lokaci sun yi jigum jigum, muma da muka bar maganarmu muka kashe kunne muna jiyosu, jikinmu ya yi la'asar". Nasiba ta ce "Tabbas soyayyar da take ta gaskiya kuma k'arfaffa ce ake yin afuwa da sassauci a cikinta." Na kasa cewa komai domin hausa ta yi cikin hikima. Da Bulkachuwa take. Bansan ya aka yi ba, kawai sai ganinsa na yi ya fito ya fice a hanzarce. Sai ga Dada ma ta fito cikin rashin sukuni. Ta zauna jiki a sanyaye. Ta kasa jure wa ta kalle ni ta ce "Yabi Jabiru zai ballo wani irin tashin hankali, kada ki sake ki saurare shi. Ki rike Alhaji nan yafi miki, ina tsoron abin da zai biyo baya." Na yi k'uri ina kallonta a zahiri gaskiya ta fa'da tashin hankali zai iya biyo baya. Amma kuma a zuciyata sai nake ganin son zuciya ne kawai yasa ba zata goya masa baya ba. Dan kawai Maijidda d'iyar shalelenta ne, kuma mawadacin gidanmu. Dan sai yanzu na fahimci ba fa wai ku'di ne da Baban Kasuwa ba, kawai a gidanmu ne yafi kowa wadata, saboda talakawa ne mu na sosai. Me yasa a farko bata hana a bashi ita ba, tunda tasan ni yake so? Me yasa a wanccan lokacin ba ta yi zaton hakan zai zama tashin hankali a dalilin gaba da kullaci da zai shiga zukatan y'an gidan gaba'daya ba?. Duk yadda nake da ba'kin jinin a cikin ya'nuwana sai da suka yi kishin abin da aka yi mini, suka yarda ubanmu aka tozarta. Tashin hankali tuni an shige shi ai, kawai sa'ar da aka yi Baban Marina mai sassauci ne, shi yake ta tsawatarwa dan kada mu kullaci y'anuwansa ko muce zamu rainasu. Amma iyakacin wula'kanci da kaskanci an yi mana. Ba kuma wanda ya k'alubalanci hakan sai Baba ta Bulkachuwa ita ma kuma bata da power kamar Babanmu. Duk da a cikin rufin asiri take, dai-dai gwargwado tana dan tagazawa wajen yiwa Dada hidima. Haka nan ita ka'daice kafatalin yan'uwan Babanmu zata aiko da wani abu da sallah ta ce a bawa y'ay'ansa. Wani lokacin sark'a da yan kunne, ko hijabai, ko y'an takalma masu sau'ki haka. Dan ko sallar da ta wuce da hijabanta muka je sallar idi ni da Nazira. Amma Baba Maryo uwarsu Nasiba da bata iya tsinana komai har a Dadan ma ita take zuba mulki, haka nan komai aka yiwa Dada na dangin sutura ko wani abu mai k'yau karshe sai ya zama nata ko na y'ay'anta, ita kuma saboda auta ce da