Sashe 63
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba'daya y'anmatan suka bi shi da kallo. Wani irin mak'aki ya tokare ni. Na sani zai burgesu tunda Ubangiji ya masa kyakkawar sifa kwarai da gaske. Motsa jikinsa da yake yi, ya sanya jikinsa ya ginu sosai. Wanne irin wula'kanci Tijjani ya yi mini yau? Na fa'da a zuciyata. Matar ta ce "Cire mini lallen nan. Ai bansan maigidan baya so ba. Na tabbatar ba da izininsa kike wannan sana'ar ba. Shiyasa ya dauki wannan k'azamin matakin. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Yau na ga lukutar tsiya ni Hadiza." Ta fa'da cikin kad'uwa. Na fara kuka sosai, ina yi, ina cire mata. Ai kuwa ina gamawa ta ja ni jikinta ta mak'ure ta rufe ni da duka tana cewa "wanne irin shak'iyanci kike yi masa da ya janyo miki wannan d'anyen hukuncin. Shin baki da makusanta da suke fa'da miki gaskiya ne? Kowa ya kalle shi yasan yana tsananin son ki. Me kike yi masa?" Dama so nake na yi kukan sosai, ko na samu sau'kin zugin da kirjina yake yi mini. Dan hakan na bu'de baki na dinga canyara ihu. Ita kuwa sai dukana take tamkar ita din Gwaggo ce. Sai kuma ya fito a bazame. Dan ya ga me ya sani irin wannan kukan. Ganina a hannun Hajiyar ta matse ni tana ta mintsini na ya sanya shi ce wa "Na ha'da ki da Allah ki bar ta haka nan Hajiya, k'yale ta" Ai kuwa ta k'yale ni. Ya tsaya daga ba'kin k'ofar ya mika hannu ya d'auko jallabiyarsa da take rataye. Ya yi baya, ya sanya. Ya dawo ba'kin kofar ya ce "Darajar wannan baiwar Allah kika ci, tana gidan. Na rantse miki da yau kin ga k'arshe taurin kai da tsiya." Ya kalli Hajiya ya ce "Na gode sosai, amma dan Allah kada ki sake ta'ba ta. Ki yi ha'kuri". Yasa kai ya bar gidan gaba'daya. Y'anmatan nan suka kasa ce wa komai amma dai gaba'daya sun shiga rud'anin al'amarin da ya faru. Ta tashi, ta fita tana fa'din "Zan je har gidanku na sanar wa Gwaggonki baki shirya zaman aure ba. Gara ta sani kada rana daya ta gan ki kamar jifa kin koma gabanta. Ke ko tunanin halin da take ciki ba kya yi? Tare da kanwar ki aka aurar da ku. Tana zaune k'alau, amma ke kin fitini kanki kin fitine shi." Na dinga kuka ina bata hakuri akan kada ta fa'da wa Gwaggo fishi zata yi da ni. Da k'yar ta yarda ba zata fa'da ba. Bayan ta ce na kira mata shi a waya. Akan dole na kira shi. Na danna speaker. Yana dauka sai ce wa ya yi "Bebina kin daina kukan? Ki yi ha'kuri kin ji. Ai da nasan mutumiyar kirki ce irin haka da bazan yi hakan a gabanta ba". Ba'kin cikinsa ya nemi kassara ni. Na mika mata wayar cikin b'acin rai. Jin muryarta ya sanya ya shiga cikin nutsuwa sosai. Bai bari ta ce komai ya fara bata ha'kurin abin da ya yi. Ta ce "Tambayar ka zan yi. Baka son ta yi k'unshin ne?" Da sauri ya ce "Ina so. Ai bazan hana ta sana'ar da ta kafu da ita ba. Amma dai dole ta bar abin da na ce mata. Na ce kada ta kuma yi mini lalle a d'akina, ta je ta yi a nata d'akin. Shine kawai rikicina da ita". Ta ce "To shike nan. Magana ta k'are." Ta kashe wayar ta murd'e mini kunne tare da ce wa "Dama can dakinsa ne, amma kike masa k'unshi a ciki? Saboda ke tabbataciyar marar kunya ce? Amma yanzu ai kin ga 'karshen tsageranci." Ta saki kunnena ta tashi ta bud'e wadrof d'ina ta ga dukka kayana ne babu nasa ko daya. Ta sake kai kallo ga d'akin ta ga babu alamun hula ko wani abu na miji a ciki. Ta daure fuska ta ce "kwanta na duba ki, wato har yanzu ke budurwa ce ko?" Na rushe da kuka wiwi. Ina fa'din Dan Allah ki yi ha'kuri sanin da na yi ita din mai zafi ce. Sannan ba mai wargi ba ce, y'ay'anta ma shakkarta suke yi ainun. Ta cije ta ce "Kin san Allah sai na ga ni. Ko kuma yanzu na saka Salisu ya dauko mini Gwaggonki tunda ni ba ni da mutunci a wajen ki." Na sake tsananta kukana ina fa'din "Dan Allah Hajiya ki rufa mini asiri. Dama fushi suke yi da ni. Mussaman Babanmu, ki yi hakuri. Kuma ni akan wannan ba laifina ba ne. Na yarda na yi kuskure akan maganar d'akinsa, ba kuma zan sake maimaita wa ba.". Ta saki ajiyar zuciya ta ce "Shikenan na hakura. Amma na baki daga nan zuwa kwanaki uku ki kwaso kayansa ki dawo masa da su nan. Sannan ki kwantar da kai, ki roke shi ya baki iznin zama a d'akin tunda gidan naku babu bishiya ko rumfa. Ba sai na fa'da miki muhimmanci sana'ar ki ba. Komin wadatar miji neman na kai da'di ne da shi. Zaka yi harkokinka kai-tsaye ba sai ka jira an yi maka ba. Bare ke da kika saba yiwa iyayenki hidima a cikin sana'arki". Ina kuka na ce"To. Domin dai na gamsu da maganganunta. Ta sake ce wa "Ki ajiye komai ki rungumi auren ki, kowa da kaddararsa Yabi. Ke taki ma da kyua. Tunda mijin na ki yana son ki da alama kuma yasan me yake yi tunda soyayyar bata rufe masa ido ya sarayar da yancinsa na miji ba. Ki shiga taitayinki. Wadanccan y'anmatan zarata kallon so da fatan ace nasu ne suke binsa da shi. Ki ribaci damarki. Ki rike darajarki tun baki tankwabar da ita ba. Idan a yanzu da yake neman zaman lafiya da ke, kika yarda kuka zauna, to har tsufanku ya dinga kaffa kaffa da ke. Ban ce ba zai bata miki ba, ban ce ba zai kuntata miki ba. Amma dai zaki samu sau'ki, zai kuma din ga shakkar ki botsare masa. Kada ki yarda ki koya masa jure wa fishin ki Yabi". Cikin kuka na sake ce wa "To" Wanda ban san dalilin da ya sanya na kasa daina wa ba. Ta nisa ta sake ce wa "Ban da ma ke din sakarya ce ai cikin hikima zaki gaje can din. Da kin nuna masa nan ne dakinsa ai shike nan. Yanzu kuwa can din da kika raina sai ki ga ya samu wacce zata yarda ta zauna a cikinsa. Sai dai ki ji an kawo masa amarya." Ba k'aramin dukana wannan maganar ta yi ba. Na k'ara sautin kukan da nake yi. Ta ce "Sha sha a haka kamar wayayyiya amma bagidajiya ce. Baki iya komai ba sai kishi. To wai wannan kishin na mene ne tunda ba sonsa kike yi ba? Ya auro uku mana me zai dame ki? Na so bana gidan yau, ya tub'e ya zauna cikin mata na ga yadda zaki yi. Kin san kuma duk masu hankali baza su sake zuwa miki ba. Marasa tunani kuwa sun dinga zuwa, dan su k'ulla alaka da shi". Bata bar gidan ba sai yamma lis, bayan y'an matan sun cire nasu sun tafi. Sai bayan Isha ya dawo. Ya same ni a dakina ina kan abin sallah duk na takura tsabar takaicinsa da yake dafa ni. Ya zauna a kasa kusa da ni. Ya ce "Barka da gida Asiya Toro". Na kasa bu'de baki na ce masa uffan. Domin yadda zuciyata take tafasa sai na ji tamkar na yi ta k'unduma masa ashariya. Yasa dukkan hannunsa ya ru'ko ni yana fa'din "Ba kya gajiya da kuka ne Asiyata?" Ai kuwa ba zato na fara kai masa duka a ko'ina. Ya dinga fa'din"ki yi a hankali kada siraran hannuwan ki su ji ciwo." Na bar dukan domin tabbas hannuwana ne suke mini zafi tunda jikinsa a murd'e yake k'warai da gaske. Kawai sai na fashe da kuka tare da ce wa "Sai Allah ya bi mini hakkina da ka keta a gaban jama'a. Baka da buri irin ace an kai k'arata gaban iyayena. Ka je na barka da Allah ya bi mini kadin zaluncin da kake yi mini. Ban da ka mayar da ni banza ka yi mini hakan? Bayan kwanaki akan idona ka saka aka yi maka girki. Idan tak'amar kicin da kayan abincin naka ne. To kwanukan da tukwanen fa? Ai da sai ka siyo ka kawo mata, ko ta debo na uwarta." Da sauri ya ce "Amma Dada ai ta kashe wannan maganar. Na baki hakuri kuma." Na ja tsaki mai tsananin gaske tare da ce wa "Ri'ke ha'kurin ka bana so. Tunda ka nuna ba ni da iko a cikin gidan da ake ce wa wai nawa ne, sai ka fa'da mini inda zan dinga zama da jama'ata, tunda ka sani a gidan ubana ma ina da inda aka ware mini nake zama na yi sana'ata." Ya koma gefe ya ce "Gidan ki ne ba wai ba ne". Da rawar murya na ce "Wallahi ba nawa ba ne. Domin da nawa ne ba zaka tozarta ni irin haka akan d'aki ba." Ya nisa ya ce "Tsakanin ki da Allah sau nawa ina gargadinki akan dakin? Ai ba sana'a na hana ki ba. Dakin ne ba zai yiwu ace mata suna shigar mini ba. Tunda dai shine dakina zan yi iyakacin kokarina na ba shi kariya irin yadda ake bawa dakin mijin da yake da daraja. Ki zo ki yi anan dakin, ko a falo ba ni da matsala da hakan. Amma wancan dakin baki isa ba, ba ki biyo hanyar da zai zama k'arkashin ikon ki ba Asiya". Na ji tamkar na sharara masa mari. Amma da na tuna maganganun Hajiya. Da alwashin da ta yi na zata fa'da wa su Gwaggo halin da nake ciki. Ya sanya na ha'diye dukkan fishina na ce "Ai shike nan". Ya mik'o mini ledar awara tare da ce wa "Ga shi na san baki ci abinci ba.". Ban kula shi ba. Ya mike ya ce "Sai da safe, yau na gaji likis." Kwana na yi, ina nadamar yadda zan dawo da Tijjani dakin nan alhalin bai nuna yana son ya dawo ba". Washagari bayan na idar da sallah barci me nauyi na yi. Sai wajen goma saura na farka. Na tashi