Sashe 137
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
abin da zan ci. Na tabbatar ta dad'e da ajiye makamanta. Amma yadda nake tiritiri da rik'e musu gidan ya kara mini kima k'warai da gaske. Ahalin gidanne dai idan muka had'u ko idan na fita da nufin zagaye ake bina da kallon k'urillah da tuhuma. Yara basa iya ce mini komai ba. Amma da kunnena na jiyo matansu Baban Kasuwa da na Tsakiya suna gulmar cikin jikina suna fad'in "iyalin Tijjani bata yi shashanci ba, ai a yi mamaki, irin fasadin da ya yi a doron kasa, sai kurum." Na yi kamar ban ji ba. Domin a yanzu da nake fama da rashin Baban 2 mene ne bazan yi hak'uri a kansa ba? Baban Tsakiya kuwa fama yake da ciwon hawan jini. A dalilin mafi yawan y'aya'nsa sun kangare. Dama dai Jabir ne mai dama, to a lokacin da yake da dama bai bari ya taimaki kowa ba. Domin ko ni a farkon farkon rufe Baban 2 idan ya tura mini kudi sai ya ce "Ba sai an ji ba". Dan haka mafi yawa yanzu ba'a taimakonsa ko tausayinsa domin a lokacin da ya samu ba wanda ya more shi. Sai aka yi mutuwar kasko. Shi kuwa Baban Kasuwa manyan y'aya'nsa guda biyu na farkon mata ne. Amina sai Maijidda. Kuma dukkansu a yanzu kowa fama take a gidanta bare ta taimake shi. Gara ma Maijidda yanzu ne babu ta same su. Aminu na ukun sa'an Anas ne, yanzu suke tasowa. Gabadaya rayuwa ta yi juyin waina. Baban Marina da ake ganin babunsa a yanzu yafi su rufin asiri. Abincinmu yafi na kofofinsu. Ba kuma kudi ya yi ba. A a Y'aya' ne suka taso, muka hutar da shi fafutukar rayuwa. Har yau kuma idan Baban Marina ya samu damar da zai yi mana wasiyya sai ya ce "mu zama masu afuwa da manta sharri, mu kuma rik'e alheri komin kankatarsa. Ko waya ka yi masa sai ya ce "Ba jarumta ba ne fad'a a tsakanin yan'uwan juna. Ba kuma tsoro ba ne idan kai mai gaskiya ka janye ka barwa wanda ya karkace, masalaha ne da takaita rikici. Har ilah yau ba imani ba ne ka yi fatan ganin wani ya shiga mummunan yanayi duk yadda ya zalunce kuwa. Mafi yawan sakayya yanzu tun a duniya Ubangiji yake fara yinta. Matukar kana da gaskiya baka nufi kowa da sharri ba, to sai ka ga alheri komin dade wa. Iri iren wadannan nasihohin ne suka dagargaza mini tunanim son ganin su Baban Tsakiya a halin tagayyara, na huce da su nake nema masu gafarar Ubangiji. Na gamsu idan suna cikin tozarci dole dai jininmu ne kuma gidanmu daya. Nazira akai akai take ziyarta ta. Mu yi hira, ta daho mini abinci, ko ba zata zo ba sai ta aiko mini duk da gidan namu da abinci amma kullum sai ta ciko cooler ta kawo mini. Muna hira na ce "Adda Nazi wai ya ya Saiwowin dahuwar tattabaru din nan kuwa? Ni dai na ga kyaunsu. Ya sabunta ni a wajen Baban 2 sosai". Ta ce "hm kayya bari ke dai suna da kyau. Amma maigidan ne kuzarinsa ba mai yawa ba ne. Na yi dariya na ce ke kuma babu s'auki." Ta ce ba haka ba ne". Na ce To zan karbo miki moringa tea ya dinga sha a shayi ko a lemo, zai sha?" Ta ce "zai sha ba shi da matsa akan hakan. Amma dai Yabi kada ki saka na ba shi abin da zai cutu ko ya hallaka ni" Ta ba ni dariya ainun na ce "Kai Adda Nazi. Garin zogale ne fa sai sai saiwowi marasa illah. Yana da d'an kudi amma yana da kyau ainun". Ta ce shima a kano ne?" Na ce "eh a wajen mai saiwowin ne duka daga Chad take kawosu. *08032773332*. Ta ce "Tom shi ke nan. Na gode." Sai da muka yi wata biyu. Muka koma BAUCHI. A lokacin cikin ya shiga wata na hudu. Tun ina jin kunyar Babah har na hak'ura na ware a dalilin itama mita take yi. Wai a sadda muka yi abin da muka yi, ban yi zaton zan ji kunya ba, sai yanzu? Ranar da muka je Tijjani ya fahimci ciki ne da ni har ya yi k'wari ya kasa magana ya tafi ya yi sujjud shukur. Babah ta koma gefe ta yi kamar bata wajen. Ya dinga murna da yi mini addu'a. Gabadaya na danyace. Na ciko sosai. Duk wata ko ban je gidan gwamnati ba, sai Hajiya ta kawo mini kudin envelope tare da nanata basu manta maganar maigidan ba. Karamci kad'an na yiwa Hajiya, sai ya janyo mini sanadin alheri mai yawa. Na kuma fahimci tausayina take ji da gaske. A haduwarmu Allah kad'ai yasan adadin alherin da nake samu. Su Hamim ta mayar da su tamkar jikokinta. Suna bata sha'awa. Kullum a cikin kawo musu suturu masu kyau take, ga kayan wasa kala kala. A haka rayuwar ta cigaba da garawa har na shiga watan haihuwa. A lokacin kamfani ya sake biyan kudin filin Tijjani. Na yi siyyya mai rai da lafiya amma na kudire ba zan yi Taron suna ba. Ya fad'awa Aliyu yadda za'a yi masa da kudinsa. Yaya Aliyu Kuma Bai fad'a mini yadda za'a ba, Nima ban tambaye shi ba. Bayan ya ce a ware wanda za'a yiwa Baban Marina da mahaifiyarsa hidima. Da ragowar yan'uwan. Ya ce Aliyu ya dauko 250 ya yi wani abin. Cikin ikon Allah watan Muharram da kwana bakwai na haifo yarinya sankaceciya. Jawur da ita tamkar tsada. Wanda ya yi daidai da 1 ga watan goma miladiyya. Babah ce ta karbi haihuwar domin cikin dare ciwon ya tashi. Kafin Aliyu ya zo da mota tuni na haihu ta gyara wajen. Kawai mun je asibitin ne an duba ni. A daren muka dawo gida. Babah ta zuba yarinya ido ta ce "Ke kuma Aliyu kika debo?" Na kalle ta. Domin ni fa bana gane kamar yara. Aliyu ba sosai suke kama da Bulkachuwa ba, sai dai suna yanayi saboda jini d'aya. Ihisan ce suke kama da Tijjani kwabo da kwabo shi yasa su Hanif suke matukar kama da ita. Dan idan muka hadu kowa ita yake zaton ta haife su ba ni ba. Washagari Babah ta d'auki jinjira ta kai wa Tijjani da kanta. Aliyu ne ya kaisu. Tare da su Hamin da suke murnar sun yi KANWA tamkar su mayar da ita ciki. Ya karbe ta cikin kunyar uwarsu. Ya zuba mata ido yana jin sonta da tausayinta na tsaga shi. Zata girma babu soyayyar uba alhalin ba mutuwa ya yi ba. Ya tsinci kansa da ce wa "Allah ka mini sakayya da duk wanda ya k'ulla mini sharrin da aka nesanta ni da iyalina, na kuma rasa y'ancina. Aliyu ya juya domin idonsa ya ciko da k'walla. Babah kuwa tuni take sharbe. Domin ya bata tausayi k'warai da gaske. Murya na rawa ta ce "yi mata addu'a ka kuma yi mata huduba. Ya shiga jero mata addu'oin tsari da albarkar rayuwa. Ya Kalli Aliyu ya ce dauke ta ka yi mata huduba da duk sunan da kake so." Ya saka hannu biyu ya dauke ta ya yi mata kalmar shahada ya lakaba mata Hauwa. Ya mikawa Babah ita yana fad'in sunan ki na zaba mata ". Da sauri ta ce "Ba kuwa sunana zata ci ba. A saka mata Asama'u. Don Yabi tasan mun san alheri, muna kuma gode mata.". Aliyu ya ce "Hakane Babah. Ya sake sabuwar huduba ya rad'a mata Asama'u. Maimakon ya bawa Gwaggo sai ta mika mawa Tijjani domin ta ga bai gaji da kallon ta ba. Ya ce "Aliyu rago nawa zaka yanka mata? Domin gabadaya kai ta kwaso, kamar da ta yi da kai ta shahara." Ya ce "Haka na ga ni, Babah ma ta ce ni ta kwaso. Biyu za'a yanks mata. Ana yaye ta kuwa zan dauke ta". Tijjani ya ce "Yabi kuka zata yi Aliyu. Twins ne naka. Kai na haifawa su, ga shi nan kana ta tiri tiri da su babu gajiyawa. Ko yanzu idan kana so ka wuce da su, amma wannan barta, ita ce zata debe wa Yabi kewar zaman jirana". Babah ta ce "Uhum! Nan da nan ya kame bakinsa domin ya shafa'a da ita." Sun jima kafin su tafi su bar shi cikin alhini. Yarinyar ta shiga ransa fiye da twins. Suna isa suka tarar da mutanan Toro. Gabadaya ahalin Baban Marina ne sai Dada. Da murna ta fad'i sunan jaririyaya. Kowa ya yi murna take Yaya Salamatu ta ce sai a kirata Husna. Na ce "To". Farincikin sunan Gwaggo ya zangwanyar da alhinin da nake ciki. ** Na Dade da gane Dada ba k'aramin son Bulkachuwa take yi ba. Domin sai yanzu na fahimci kafatalin jikokinta tafi sonsa. Tunda bata iya boye son tagwaye. Ni kaina na sake samun daraja ne a wajen ta saboda Tijjani. Kullum ta gan ni sai ta yi kuka. Y'aya'nsa kuwa komai hannunta ya taba sai ta basu. Tana yi tana fad'in "Allah ka yiwa mai babban suna abin da zato bai yi zatonsa ba. Wanda duk ya k'ulla masa wannan salalar tsiyar Allahu ka dabaibaye duniyarsa da firgici da tashin hankali." Kaitsaye Babah ta bawa Dada jinjira. Ta zuba mata ido tana kuka ta ce "Mai sunan manya ya haifi Aliyu. Sai na tuna ranar da aka haife shi. Haka yake sak." Aliyu da yake tsaye a bakin k'ofar ya ce "Dada ikon Allah! A gaban y'aya'na da kannena kike maganar haihuwa ta?" Ta ce "To uwaka ma bana yi zancen haihuwar ta bare kai". Ya ce "Ai shike nan, dama ni ba wai kina sona ba ne . Yaya Tijjani ne na ki. Kin ga da kin bini a hankali gobe dia na zo na kai ki wajensa." Ta marairaice ta ce "A sannu ma zan bika Ali gadanga angon kilima". Ya ce "Assha kin batawa amarya ta sunanta. Amma dai zan zo, ya hau gaishe ta. Sannan suka gaisa da su Mama. Ya ce "Ummi ni da ke waye babba ne?" Ta ce "Mama fad'a masa". Mama ta ce "Ita ce babba ranar sunanta aka haife ka". Ta nuna shi da yatsa ta ce "To ka ji Wallahi ka kiyaye ni" Ya rik'e kiirji ya