← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 146

Sashe 53

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

sauri yake kada ya yi latti tunda kayan Islamiya ne da jikinsa. Na kar'ba na tura kofar. Kicin ma fara shiga na dauko plate. Sai lokacin na lura da kwalin taliya, macaroni da galan din mai dana manja. Sai wani katon bokiti sosai mai murfi. Na bu'de na ga garin masara ne a tankade. Daga kantar kuwa an jere robobi masu dauke da kuka, kubewa daddawa da yaji. Sai kunshin bakar leda mai dauke da Maggi da onga da kuma gishiri. Na yi tsam da raina. Ina jinjina wannan kokarin. Na sani Kuma Babanmu baya irin wannan al'adar domin shima baya bari a dorawa ango hidima mai yawa. Na tabbatar a kaina aka fara irin wannan hidimar ni din ma saboda Tijjani ya yi. Daga can gefe na sake hango buhun gishiri a cike amma kuma d'aure bakin aka yi. Na saka hannu na ta'ba na ji don na tabbatar ba gishiri ba ne. Ina tabawa kuwa na gane shinkafa ce a ciki. Na girgiza kai ba tare da na furta komai ba. Na dauki abin da zan dauka, na fice. Na zauna ina cin abincin da ya yi mini da'di ya ji kifi da albasa. Na bu'de fridge ga mamakina sai n ganshi cike da pure water da lemon fanta da coke da kowanne zai yi shida. Take na fahimci katon daya ya siya aka hada masa kaloli. Na dauki ruwa da lemo na rufe. Ina ci ina nazarin yadda Tijjani yake ta rawar jiki a kaina. Wayata ta hau kuwwa. Kamar ba zan dauka ba sai kuma na dauka din. Da sauri ya ce "Network dina ne ya dauke. An kawo miki abincin, kin ci?" A shak'e na ce "Ni ban ci ba, yaji ya yi yawa, ga shi salam babu gishiri ko maggi ne oho". Ya diririce ya hau fa'din "haka Ummi zata yi mini? To a kawo miki yoghurt. Kafin na dawo na miki girkin da kaina". Na yi shiru. Cikin rarrashi ya ce "Pls Asiya Toro". Na tunzura na ce "Ai da zaka bar Toron baka tuna da cikina ba. Saboda bani da daraja. Akan me yanzu zaka fitine ni da buge bugen waya da tambayar na ci abinci ko ban ci ba. To bazan ci ba, idan na mutu ma ai baka da asara." Ya harzuka ya ce "Botsarriyar yarinya kawai! Ana taro ki, kina sake nausawa, to kar ki ci din. Allah ne shaidar na yi bakin kokarina". Ai kuwa na zunduma ihu tamkar gaske. Na katse wayar. Ya dinga kira amma naki d'agawa. Ya kira ya kai sau biyar ina gani ban dauka ba. Daga can sai ga text message. Kamar bazan bu'de, sai kuma na bu'de din. "Asiya Toro ki ji tausayina! Ki daina mini irin haka. Kinsan yadda zuciyata take bugawa a dalilin kukanki da kin daukar kirana? Ki yi ha'kuri bazan sake yin tafiya na barki hakan ba. Kuma indai na iso lafiya da kaina zan dafa miki komai kike so". Jikina ya yi sanyi. Tsawon lokaci na kasa gane yanayina, tausayi ya bani ko kuwa mene ne? Na bu'de what'sapp na ga anan ma ya turo mini sakonni. Na kasa bu'de wa domin bana son na sake jin fiye da kasalar da nake ciki. Da yamma lis sai ga shi ya dawo. Na bu'de masa kofa ya shigo dukkan hannuwansa ri'ke da ledoji. Ban yi yun'kurin kar'ba ba. Da walwala ya ce "Asiya Toro babu oyoyo sai kallo mai kama da harara?" Na gintse fuska na yi gaba, na bar shi. Ya biyo ni falon dana shiga. Ya ajiye mini a gabana. Ya fita da sauri sai gashi ya kinkimo kwanon satellite ya ajiye a tsakar gidan ina hango shi ta windo. Da'di ya yi matu'kar kama ni. Domin na kagu na fara kallo. Ya sake fita ya dawo rungume da kwali a kirjinsa da na yi zaton receiver ce. Dayan hannun kuma leda ne. Na yi maza na gyara zamana na yi kamar harkokina kawai nake yi. Ya shigo da sallama na amsa a hankali. Ina mamakin yadda Tijjani yake da yawan sallamah. Ya zauna a kasa a gabana tamkar uwargida da yaronta. Amma girmansa da cikar haibarsa ya sanya bai yi kama da yaron gida a gabana ba. Tunda ni din yar mitsil ce. Yanayinsa yafi kama da na wadda yake neman a amince masa, a gamsu da lamarinsa. Da barin jiki ya tashi ya dauko roba a kicin, da yar wuka hadi da bowl karami irin plastic din nan mai k'wari. Ya debo ruwa a cikin robar. Ya shigo, ya bu'de ledar da tafi kusa da ni. Apple ya ciro guda biyu ya wanke a cikin ruwan, ya saka su a bowl din tare da yar wuk'ar ya miko mini ya ce "Fara da wannan Asiya. Ki rage yunwa kafin na gama miki abincin. Maghariba ta kawo kai sai na dawo daga sallah zan d'ora miki. Me kike son ci?" Ban kar'ba ba, ban kuma tanka ba. Ya ce "Ki kar'ba mana, me yasa kike yi mini haka ne?" Yadda ya yi maganar a dan tunzure, bansan ya aka yi ba, na tsinci kaina da mika hannu na kar'ba. Ya sassauta ya ce "ko na yanka miki?" Ban amsa ba, illah hannu da na saka a cikin robar na wanke. Sannan na dauki Apple din na fara gutsura da bakina. Ya zuba mini ido yana kallon yadda nake cinsa cikin yanga tamkar me cin magani. Ya murmusa ya ce "Yabi yanga". Karon farko da kunne ya ji ya kira ki da Yabi. Na dauke kai na ce "Tsabar adawa da kake yi da hajjina shine ba zaka ce Yabi ba. Yau kuma da bakinka ya subuce ka fa'da din sai da ka ha'da da bita da k'ullin yanga?" Ya fashe da dariya sosai ya ce "Kamar kinsan subutul kalam na yi. Tun fil'azal nafi son ce miki Asiya domin sunan na matu'kar burge ni. Yanzu kuma tunda Jabir haka yake ce miki, na sake kauracewa sunan. Bana adawa da hajjinki, amma fa bazan kira ki da Yabi ba. Ina fatan na samu damar da zan kai ki sauke faralli Asiya. Sai ki zama Hajiya ta sosai tunda hakan shine burinki." Na dauke kai, na gutsuri apple na ce "Da wanne ku'din zaka kai ni Makkah? Ai indai ina tare da kai babu wani alherin da zai same ni, bare alheri irin na zuwa Saudiyyah". Tsawon lokaci ban ji ya ce mini komai ba. Na juyo da kallona gare shi. Na ga jikinsa ya mutu. Duk kuzarin da ya zo da shi ya gudu. Gaba'daya ya zama tamkar an kwara masa ruwan sanyi. Ni kaina sai na ji jikina y mutu lakwas. Tsawon lokaci muna haka tamkar masu zaman makoki. Da k'yar ya yun'kura ya mike ya ce "Na tafi masallaci". Na bishi da ido, ina jin abin da nake ji a kansa na sake mamaya ta. Na kasa gane tausayi yake bani ko kuwa menene? Nasan dai ko ka'dan babu digon sonsa a raina. Da zai dawo ya shigo da k'aramin gas (3kg). Daga bakin kofar falon ya tsaya bayan ya daga labule ya ce "Me zaki ci Asiya?" A hankali na ce "Ni na koshi, akwai macaronin nan a kicin". Bai ce komai ba. Ya saki labulen. Da kansa ya zubo abincin. Sai dai wannan karon a kujerar nesa da ni ya zauna. Bayan ya dauko ruwa da lemun coke. Na kalle shi tamkar wani mai wadata ya hakince ya saka ruwa da lemu a gaba. Ya kammala, ya dube ni bayan ya ha'diye fishins ya ce "Ki dinga jin tsoron Allah Asiya. Yanzu abin da kika yi ya yi daidai kenan? Ki saka na k'ira Ummi na balbale ta da sababin bata yi mini aikin da na saka ta da kyau ba. Ashe ma kin ci kin cika cikin ki, tsabar fitina, da son ki tayar mini da hankali shine ya sanya kike kuka da fa'din abincin bai yi da'di ba?". Na zum'bura baki, na kasa cewa komai. Ya yi k'wafa, bai ce komai ba. Ya sauko ya zauna kan kafet din ya bu'de reciver ya ce "Gashi na siyo miki." Ganin ban amsa ba ya sanya ya cigaba da bude ledojin da ya shigo da su. Kusan duk kayan abinci ne dangisu shinkafa, taliya da macaroni. Sai katon din indomie da kayan shayi. Sai kuma leda mai dauke da sabulun wanki da su omo, makilin da maganin sauro na kunnawa. A hankali ya ce "Ku'din da abokaina suka ha'da mini ne na siyo miki settlite da gas, shine na karo kayan abinci dan mu dan tura sosai kafin su kare." Na juyar da fuskata na ce"Madallah". Ya yi sororo murya a dakushe ya ce "Ba zan yi wani abu da niyyar na sanya ki farin-ciki ki nuna mini kin ji da'di ba Asiya?" Cike da iyashege na fara wage baki, dukkan hakorana a waje, ga idona na zazzarosu tamkar mai motsi a k'wak'walwa. Ina yin hakan, ina cewa "Na yi murna Tijjani. Ka burge ni Tijjani, na ji da'di Tijjani". Sannan na dawo yanayina na zuba masa ido na ce "shike nan?".
Chapter 53 · 0% Book details