← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 146

Sashe 88

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Watanni shida a gaba*. Zuwa lokacin duk kaucen kaucen Tijjani na kada na shiga harkar ri'ke masa gida ta ci tura. Duk yadda baya son ya karbi ku'dina abin ya faskara domin samun ku'di ba k'aramin wahala yake ga talaka a wannan lokacin da aka janye tallafin mai a Nijeriya ba. Mafi yawa masu kananun sana'u sun shiga halin ni y'asu bare kuma wanda sana'ar sa hab'o ce ma'ana sai an samu za'a yi. Duk da k'arancin shekaruna na fahimci matu'kar Tijjani zai fita ya dawo gida ba tare da ya ru'ko wani abu komai kankantar sa ba, to kuwa a wannan ranar ba zan gane kansa ba. Duk yadda zan yi masa rawar jiki da haba haba dan na samar masa da nutsuwlar bai gaza ba, ba kuma laifi ba ne dan ya fita ya dawo bai samo wani abu ya kawo mini ba. Kullum sai na fa'da masa cinikin da nake yi da nake samun makudan k'udade na yi imani mafita Ubangiji ya kawo mana, domin ba ni ka'dai ba ce wacce ta iya lallai a garin Toro. Amma duk macen da ta tunbatsa, duk macen da ta isa ko ta kai ta kawo to kuwa wajena take yin k'unshi da kitso. Sannan mafi yawa basa ba ni adadin ku'dina sai sun yi mini k'ari. Idan ya bu'de baki sai ya ce "Ko ke ce Zainab Shamsuna ai ba'a ce na zauna na nad'e k'afar wando ki yi mini komai ba. Ubangiji ya ce na ciyar da ke, na tufatar da ke gwargwadon k'arfina." Na nisa na ce "Haka ne! To a maimakon ka dinga tayar da hankalinka, nima kana tayar mini da nawa. Mu yi wata ka'ida mana". Ya zuba mini ido yana saurarona. Na ce "Ka dinga siyar da lalle da mahallabiya da salatip. Ni kuma sai na dinga siya a wajen ka. Pure water ma da nake siyar wa sai ya koma naka ne zan dinga siyar maka". Ya ce na yarda zan siyar da lalle amma ba zan siyar da ruwa ba tunda ai fridge din ba nawa ba ne". Na ri'ke hannunsa na ce "Ashe kayana ba naka ba ne? Rannan a kunne na wata cikin y'anuwana take ta fa'din matu'kar mace da namiji igiyar aure ta zarge su ai komai da suke da shi ya zama mallakin junansu. Ta kalli idona ta ce mussaman idan ta haifa masa y'ay'a to ba wani sauran iyaka a tsakanin abubuwan da suka mallaka." Na nisa na ce "Kana nufin wannan yarfen da aka yi mini, ni da kai ba kamar sauran ma'aurata ba ne? Abuna ba naka ba ne. Kai ma abin ka ba nawa ba ne saboda ni ban haihu ba?" Na fa'da da rawar murya. Jikinsa ya yi sanyi ya janyo ni jikinsa ya ce "Kina dai son ki yi mini rikici ne little ban da haka menene abin kuka? Duka ma shekarar ki nawa ne? Ni fa a halin da nake ciki ma ban shirya karban bebi ba. Hidimar ki ka'dai tana gagarata ina kuma da jariririn da bai san babu ba. Amma idan haihuwar ta zo ina so, kawai dai zan so ace bebinmu sun zo a lokacin da komai ya dai-daita mini ta yadda zan musu hidima sosai". Na yi shiru na ce "Ka sare da yawa ne. Amma da sannu Allah zai kawo mafita." Ya saki gauron numfashi ya ce "Ai al'amuran k'asar ne ya lalace komai sai da hanya, hanyar ma sai ka biya makudan k'udade kafin ka samu aikin gwamnati." Na ce "Idan Allah ya k'addara abu rabon bawa ne komin tsanani sai ya same shi". Da haka na lallaba shi na samu kwanciyar hankali, domin ni rashin ku'dinsa baya damuna irin idan ya takure ya k'i sukuni. Nafi son soyayya, nafi son walwala. Bana kuma samun hakan sai idan yana kawo wani abu, domin ya riga ya k'yamaci ace ni ce nake ciyar da mu. Washagari da wuri ya fita. Bai dawo ba sai yamma lis. Wani abun mamaki da buhun sabon lalle irin mai L din nan ya dawo har buhu uku amma d'anye ne. Na kalle shi na ga ya yi laga laga. Tabbacin da kansa ya shiga jeji ya samo. Tausayinsa ya yi matu'kar kama ni. Hawaye ya cika mini ido, a zuciyata sai addu'a nake yi masa akan Ubangiji ya hore masa hanyar da zai ri'ke gidansa cikin sau'ki. Da k'yar na ha'diye kukan nawa na dinga yi masa sannu. Ya zauna akan baranda ya ce "Asiya na gaji sosai ga k'aya ta yi ta suka na." Da tausayi na ce "Sannu, Ubangiji ya baka lada, ya kuma sanya wa neman ka albarka." Na dauko masa ruwa ya sha. Na kalle shi ya yi kaca kaca da shi. Har kan gashinsa k'ura ne. Na ce "Bari na juyo maka ruwa wanka ga shi akan gawayi. Da kai ya amsa mini. Na sirka ruwan na kai masa bandaki. Ya shiga ya yi. Ya fito ya jika kayan da ya cire. Sannan ya shiga daki dan ya shirya. Kafin nan kuwa na Kai masa abinci falo. Na zuba omo na sab'e masa kayan na shanya masa. Ya fito ya ga ina shanya. Ya murmusa ya ce "Ni ina ce Asiya Toro ce ta ce Aji dawun ta yiwa k'ato wanki?" Kunya ta kama ni domin na sani tsokana ta ya yi, tare da tuna mini sababin da nake yiwa Nasiba idan tana yi masa wanki. Na dara na ce "Ai har yanzu ma ba zan yi ba, kawai na yi maka ne a matsayinka na mijina kuma bebina". Ya shiga falon yana ce wa "zo mu yi maganar a zaune". Yana cin abinci ina masa fifita. Ya ce "Da wayo da wayo dai so kike ki dinga ce mini Bebi ko?" Na yi gajeriyar dariya na ce "A a ai sunan ka yana zuciyata lokacin kawai nake jira. Amma kai kanka ai kasan bebi ne. Domin abin da kake yi mini ai bebis ne suke yin hakan. Ba dama ka kwanta sai ina kusa da kai. Ko juyi zan yi sai dai mu juya kwanciyar gaba'daya, saboda kana.." sai na kasa fa'da. Ya zuba mini ido ya ce "Fadi mana marar kunya. Me nake yi? Na daure na ce zuke wa bebis din da zan haifa mana abinsu." Ya murmusa ya ce "Ai ba nasu ba ne, nawa ne, idan sun zo dai zan dinga sammu su, idan lokacin shansu ya k'are za'a cire su, su bar mini kayana. Ni ai ba zaki taba yaye ni ba". Na yi dariya na kawar da maganar da ce wa "Wai da kanka ka je yago lallen ne?" Ya ce "Eh. Baban Marina na tambaya ko ina zan dinga samun lalle ina sara. Sai ya kwatanta mini yankin da Ubangiji ya azurta da lalle. D'an na goro ake bawa digacin yankin sai ka je ka yi ta yanka. Shine ma ya bani dubu guda duk da shima fama yake da kansa. Da naki karba kin ga b'acin ran da ya yi? Wai raina shi na yi, shi yasa nake ganin ba zai iya bani abu na kar'ba ba. Nasa hannu biyu na kar'ba ina ba shi ha'kuri, shi kuma yana ta yi mini fararen addu'oin da suka k'arfafa mini guiwa.". Na rausayar da kai na ce "Allah ya bada sa'a, yasa a fara a sa'a". Ya amsa da "Ameen Little". Kwanaki ka'dan lallensa ya bushe. Da kansa ya zauna ya gyara abinsa tsab. Ya ha'de su a buhu biyu. Ya fita da su, ni dai bansan inda ya kai ba sai gani na yi ya dawo da shi ya zama gari mai laushi ainun, kuma ya yi auki domin ba k'aramin yawa ne da shi ba. Ya kusa yin buhu guda. Ganin hakan sai na auni kwano biyu na zauna na k'ulle shi tas. D'aurin hamsin, da d'ari. Duk wanda suka zo k'unshi sai na yi musu tallan ina sayar da lalle, ina k'wabawa mutum yasa a gidansa. Nan ma sai Ubangiji ya sanya albarka domin duk sati sai na k'ulla kwano biyu, nima kuma a satin ina k'arar da fin kwano uku ma. Kafin ka ce miye wannan sai jarin Tijjani ya kafu ya samu na siyo mahallabiya da kwalin salatip. Duk sati kuwa zai je ya yago domin ya gamsu ba k'aramin rufin asiri hakan ya yi masa ba. Tunda duk sati zan ha'da masa ku'dinsa a kalla dubu goma. Idan ya kar'ba kuwa zai siyo kayan abinci da k'ananun abubuwa. Maganar ku'din cefane kuwa da ku'din pure water muke yi. Duk da hakan nawa yana shiga amma ba mai yawa ba ne. A hakan kuma bai fasa fita ya yi sana'a ba idan ya samu. Hankalinmu a kwance yake, mun samu rufin asiri. Tunda ya samu ya biya ku'din gidan amma na watanni shida, rabin shekara. Duk nacin ya kar'ba ya biya na shekarar sai ya biya ni a hankali bai yarda ba. Da na matsa ma sai ce mini ya yi "Allah ya karbi ransa kafin ya ga ranar da zan biya masa ku'din hayar gidan da zai kwana." Daga haka na ja bakina na tsuke. Muna cikin wannan rayuwar mai da'di domin dukkanmu mun gamsu da kokarin junanmu. Na yarda ina amfani da duk abin da ya ba ni, ina iyakacin kokarina ban nuna masa ina bu'katar abu sama da k'arfinsa ba, na kuma ajiye dukkan burikana na son na dinga yin suturu masu tsada. Maimakon haka sai na tattara na sayi dan kunnen gold wanda shi da kansa na bawa ku'di ya siyo mini a Jos. Ko zan yi abu a gidan sai cikin dabara ko kuma na kara masa ku'din lallensa idan sati ya zagayo. Shi kuma tunda ya fahimci burina soyayya irin ta indiyawa sai yake ajiye komai ya yi ta kashe ni da kalolin soyayyar da ko indiyawa ma sai a shiri, tunda suma ai shirin fim ne. Shiri kuwa kowa yasan shirya shi ake yi. Amma a hakan yake lalace mini. Ya zama tamkar mai irin shekaruna. Ko a littafai ba kasafai ake samun irin Bulkachuwa ba. Domin ya iya shiririta kala kala da mata suke son ayi musu. Idan yana gida barin komai yake ya tarairaye ni. Cinyarsa ita ce wajen zama na. Goyo kuwa zai
Chapter 88 · 0% Book details