← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 146

Sashe 76

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abokina yake kawo su daga China. Ta kusa dubu ashirin, sonta nake yi, saka kawai". Na ce "Tsakani da Allah da atamfa ka siyo mini, yanzu wannan ina zan saka na je da ita?" Ya ce "Ba dan ki sa ki fita na siyo ta ba. Dan ki saka mini na kalle ki a yadda nake son ganin ki ne". Ganin ya b'ata fuska ya sanya na juya na saka pant din. Ina juyowa ya bani sabuwar breziya yar mitsil kalar wando da alamu set ne tare suka zo. Ban ce komai ba na kar'ba. Ina ayyana wato ya riga ya gama gane wacce zata yi mini. Domin duk na lefena sun yi mini yawa duk da k'ananu ne sai dai ko nan gaba. Domin da na aikawa Gwaggo akan ta bayar, dawo mini da su ta yi, ta ce nan gaba zasu yi mini na adanasu. Sai da na shafa hoda na goga jan baki kalar ruwan hoda. Sannan na zura rigar. Ta shige ni tsab. Ta d'an zarce guiwata da ka'dan, kasancewar ba ni da tsayi. Ya ce "Wow This is Asi beauty lady". Na dan yi murmushi. Ban ce komai ba. Da kansa ya sa mini hular ya d'auko sabon turare a cikin kayansa da aka rubuta Active woman. Ya bu'de ya hau fesa mini. Kamshin turaren jikinsa da wanda ya fesa mini suka hadu suak bige ni. Suka isar da wani irin sako akan Tijjani a cikin zuciyata. Shi kuma ganin na koma masa wata yar yarinya kankanuwa ya sanya ya sure ni. Ya yi falo da ni. Yana ta sakin maganganun da suke da nauyin bayyana wa. Komai da barin jiki yake yi mini. Ya ajiye ni akan kujera ya ce "Bari na kawo miki abincin Little Angel." Har cikin zuciyata na ji da'din sunan. Duk sunayen da Bulkachuwa yake fa'da mini babu wanda na ji dadinsa irin little. Domin ya dace da ni k'warai da gaske. Shiru shiru bai dawo ba. Sai na yi kamar na leka shi, sai kuma na fasa. Can sai gashi da tray da ya jero kayan abincin. Da walwala ya ce"Sorry little na bar ki ke ka'dai, ga shi babu wuta bare kallo ya hana ki gundura da zaman jiran kukun naki" Na k'yal-k'yale da dariya na ce "Wai kai ne kukun?". Cikin gamsuwa ya ce "Ba ki aminta ba? To mene ne aikina ban da na fita na yi aiki tukuru dan na nemo miki abin da zaki ci. Idan kuwa ina gida, idai baki bata mini rai ba. Still aiki zan miki dan na hutar da ke shiga kicin kullu yaumin". Na murmusa ba tare da na ce komai ba, domin na yarda da dukkan zuciyarsa ya ke yin maganar. Ya bu'de kwanon abincin ga mamakina sai ganin fanke na yi subu-subu sun soyu sun bada kala mai daukar hankali. Na kalle shi da mamaki na ce "Tijjani yaushe ka iya fanke haka?" Ya saki murmshin jin dadi ya ce "Ki bari sai kin ci sai ki tambayi na iya ko kuwa makwaki na yi". Na sauko ya ha'da mini shayi mai madara da milo. Shi kuma ya zuba bak'i. Muka fara cin fanke wanda ba karamin dadi ya yi ba. Na kalle shi na ce "Ya yi da'di sosai. Na ji har da k'wai da madara ka saka. Maimakon ka bar madara ka zuba a shayinka." Ya rausayar da kai ya ce "Ke dai ki sha my little". Ya kashe mini ido sannan ya ce "Ai ina ganin amfaninta. Addu'a nake yi sosai na samu damar da zan daina siyo miki ta sacet. So nake kullum ki sha ta ruwa gwangwani guda. Ta yadda ba zaki dinga gazawa da al'amarina ba". Kunya ta yi matu'kar kama ni. Na sanya dukkan hannuna na rufe fuskata, ina wani irin murmushin da bansan ta inda yake bullowa ba. Da k'yar na cigaba da cin abincin bayan ya ce "Duk a wajen Baba na koyi girki. Yadda kika ga Aliyu da Nasiru suna hidima irin ta y'ay'a mata nima irin wannan goyon ta yi mini. Kullum fa'di take yi, tunda bata samu mace ba, ba zai yiwu a ce ba zamu tallafa mata da kaomai ba. Kullum cikin fa'da mana take yi mu koyi aikin gida dan wataran mu taimaki iyalinmu. Annabin Rahma da yafi kowa daraja yana tallafawa iyalinsa. Ba mallakewa ba ne dan namiji ya yiwa mace hidimar girki, wanki, ko ta shara ba. Amma kuma ta ce "Ban da wanke wanke wannan na yan daudu ne". Muka k'yal-k'yale da dariya domin kuwa munsan kawai ra'ayinta ne amma babu aibu idan mutum ya yi. Ya ce "rigar nan fa ta yi miki kyua my little. Tamkar na dauwama ina kallon ki". Na murmusa ka'dan tare da ce wa"Thank you" a gayance. Na marairaice na ce "Ya maganar tomfirint din?" Cikin nutsuwa ya ce "zuwa wani satin zan kai ki da kaina". Na fa'dada murmushi na ce "Na gode Tijjani". Ga mamakina sai na ji nauyin gatsa sunan da na yi, ta mamaye ni. Karon farko da na ji hakan a rayuwata. Na lura shi kuma yana cikin maza yan ka'dan da basu damu da a fa'di sunansu kai-tsaye ba. Tas muka cinye fanken. Na kwashe kayan dan nasan idan ya mike zai kwashe ne. Na kai wajen wanke wanke na ajiye. Na koma wajensa na ce "Wai da yaushe ka yi kwabin ne?" Ya nisa ya ce"kina barcin gajiyar da na tara miki. Ni fa duk kallon jaruma nake yi miki. Ashe a tsiwa da dambe da sana'ar k'unshi kike da jarumtar". Na girgiza kai na ce "oh haka ka ce? Ai shikenan next time zaka gane ashe dazu ba karamin jarumtar na yi ba". Ya jani jikinsa ya ce "Kin san bana wasa a wannan fannin tsokanar ki nake yi, idan akwai abin da yafi jarumta kin yi dazun". Na kalle shi cikin nauyi nauyi, kunya kunya na ce "ka ji tsoro?" Da sauri ya ce "Na ji". Bai fita ba sai da ya dawo daga sallar azahar. Muka ci abincin da tare muka yi da shi. Sannan ya fita zuwa gidan Alh Ado Naira zai yi musu gyaran satellite tunda aka kawo wuta suke ta yi masa waya. Kamar ana jiran ya fita aka fara zuwa lalle da kitso. Shike nan muka shirya da Tijjani. Wata irin soyayya yake gwada mini mai wuyar samu. Da ya ga na canja fuska zai fara susuce wa, ya dinga jaye jaye magana, ko fita ya yo sai ya dawo. Matu'kar ban ware masa ba, ba zai samu nutsuwa ba. Ni da kaina na sani an jarrabe shi a kaina. Domin gaba'dayana a tsaye ban fi iya ruwan cikinsa ba. Duk zafin ransa baya son mu yi fa'da. Cikin rarrashi yake tafiyar da ni. Komai da rawar jiki yake yi mini. Kullum safiya ya wajaba kansa share duka gidan. Ya sa tsintsiya ya wanke band'akin, sannan ya tashe ni na yi wanka. Mafi yawa da safe da burodi muke karyawa. Dan haka shayin ma sai dai na gan shi a filas ya riga ya dafa. Da nutsu sai na ga ne tunda na daina gudunsa a shimfida shike nan ya tattara dukkan hankalinsa a kaina da lamarina. Baya taba yin dare a waje. Ana idar da sallar isha zai dawo ya rufe gidan shike nan sai gobe. Idan kuwa uzziri ya yanko masa sai ya bugo waya ya sanar mini yana waje kaza. Na ce to tare da addu'ar ya dawo lafiya. Ranar da yan rikicin suke kusa kuwa, na botsare masa idan ya dawo. Ya yi ta barin jiki wajen rarrashi na. Tuni muka fara jarrabawa har mun kusa kammalawa. Da kansa yake kai ni. Idan mun gama sai na yi masa waya ya zo ya dauke ni. Muna tsaka da jarrabawa Nazira ta haifo d'anta lafiyayye. Dan haka zarya nake yi tsakanin makaranta da gidanta. Har aka yi suna yaro ya ci sunan wan mahaifin mijinta Ahamd. Ni da kaina na lank'aya masa Abid. Sosai na yi mata hidima ita da yaronta. Ranar suna wanda a lokacin watan Maijidda biyu da haihuwa, y'arta Sajida ta yi gubibi da ita. Tana hannuna ina kare mata kallo. Na rasa gane da wa take kama a tsakanin itayenta Jabir da Maijidda. Saratu da Firdausi suka shigo. Ita Firdausi ta haihu. Saratu ce ta ke ja itama yau ko gobe.
Chapter 76 · 0% Book details