← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 146

Sashe 113

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kwatsam sai ga Maijidda a gida, wai ta yi yaji. Al'amarin bai yiwa iyayenta dadi ba. Domin ni da ake son ganina ina cikin tasku da jele da sunan bacin rai ba a tab'a ganin na yi hakan ba. Kuma abin mamaki Jabir din ne ya kawota gidan da kansa. Domin ta k'ure hak'urinsa a yadda ya fada.
Ya murje idonsa ya juya ya barta. Hakan ya kawo cece kuce da rashin jituwa a tsakanin Baban Tsakiya da na Kasuwa. Duk yadda suka so boye maganar kada mu ji. Sai da maganar ta fantsama domin aure zai k'ara ita kuwa ta ce bai isa ba, sai dai ya zaba ko ita ko amaryar. Ya so su fahimci juna amma ta tada balli domin da ta ga yarinyar da zai aura tunda dalibar kwalejin da yake koyarwa ce. Ai sai ta gigice domin haka take yar tsurut fara kal tamkar dai abokiyar tagwaitakar Yabi ce. Hankalinta ya rubanya tashi domin ta tabbatar ya sota ne a dalilin yadda suke yanayi da ex love dinsa. Ta kuwa ce ba dai ita ba. Shi kuwa ya ce bata da hurumin zaba masa wacce zai yi zaman aure da ita.
Watanni biyu basa cikin zaman lafiya, gabadaya ya murde mata fiye da yadda ta murde. A karshe ya kawo ta gida ya ce ta zauna ta huta tukun.
Da ya tafi ya kashe wayarsa da dukkan hanyar da za'a same shi. Baban Kasuwa ya dinga fad'a tare da fad'in tozarcin da Jabir ya yi, da shi yake. Kuma ubansa ya kasa tsawatar masa. Saboda yana jin tsoron sa. Rikici ya kaure a tsakaninsu Dada ta kasa shawo kan matsalar domin Baban kasuwa ya dauka da zafi, kuma dama tafi gudun zuciyarsa. Baban marinar da ba'a saka shi ba, shine ya tuntunbesu bayan Dada ta fad'a masa a dunkule ba a bude ba.
Abin mamaki kowa ya ce masa babu komai, duk da Dada ta fad'a masa. Shi kuwa sai ya hak'ura ya zuba musu ido.
Bai gane kan al'amarin ba sai da ta yi sati biyu. Da kanta ta je ta durkusa tana kuka ta fad'a masa yadda abubuwan suka kasance, sannan ta roki Baban Marina akan ya bawa Jabir hak'uri. Gabadaya ta shiga damuwa da tunani domin dukkan y'aya'nta uku suna can tare da shi. Mai shan nono kawai ya bar mata. Bata tab'a zaton zai yi mata hakan ba.
Duk kokarin Baban Marina ya amsa samun Jabir. Washagari ya tisa ta a gaba ya nufi Kaduna da ita. A ransa ya tabbatar dan tana son komawa dakinta ne. Ba dan hakan ba da bai isa ya yi irin wannan ikon ba.
Jabir na ganin sa ya ware fuska ya marce shi da girmamawa. Baban ya dinga yi masa fada tare da tabbatar masa ya yi tsaurin ido.
Cikin jin nauyi ya ce "Ka yi hak'uri Baba! Ta kai ni bango ne da yawa. Ni fa dama hak'uri nake yi domin ba hakan nake so ba, amma tunda kaddara da rabo ya ba ni ita, ban zalunce ta ba. Ga ta nan ta fada maka inda na kuskure domin nasan iyakar adalci ina yi mata. Aure kuwa bata isa hana ni yi ba, bata kuma da hurumin zaba mini wacce zan aura domin ni din ba makaho ba ba ne, bare ta ce zata zaba mini wacce zan aura".
Baba dai ya yi masa fada tare ce wa "Ka dauke ta ka kai mana ita, ka yi tafiyar ka ai rainamu ka yi Jabiru. Duk cikinmu ka rasa wanda zai maka maganin matsalar sai ta hanyar mayar mana da ita? Ko a lahira wani na cin arzkin wani. Kada ka sake irin haka. Kishi kuma ai dole ta yi, ka rarrashe ta, ka kwantar mata da hankali ba wai ka ankara ta ba."
Ya juya ga Maijidda take kuka sosai ya ce "Ke kuma ba ruwan ki da auren sa, matukar yana yi miki adalci, kawai ki yi hakuri ki yi addu'a. Ai kishiya yar uwa ce, ina ruwan ki da ita. Ban da ma sakarci me ya ka ki yin fitina akan wacce ma bata zo hannunsa ba? Kina ahalin gidan Marina ki ce ba kya son kishiya? To ko da kika ga gyatumar ki ita kad'ai ai mu kina ganin kofofinmu mata ne da yawa ba kuma wacce ta kori wata, ko ta hana ta samun arzikin ta."
A ranar ya juyo ya dawo.
Ba jimawa kuwa Jabir ya yi aurensa. Hakan ba k'aramin tasgado ya janyo a taskanin Baban kasuwa da na Tsakiya ba. Da k'yar aka samu suka fara gaisawa. Kunyar mutane da yadda aka san kansu a hade yake ya sanya suke gaisawa. Da kuma yadda Dada ta yi kuka sosai akan gabar da suke yi da juna.
A zahiri sun shirya amma kasan zuciyoyi babu dad'i. Ba yadda zasu yi ne kowa yana ganin shine akan dai dai.
Baban Marina dai bai ce kala ba. Domin yanzu da abubuwa suka fara warware masa a dalilin mafi yawa y'aya'nsa muna cikin rufin asiri. Muna had'a abin da za'a ci a k'ofarmu. Tijjani kuwa ya dauke masa cefanen kayan miya da kudin k'ananun bukatu.
Hakan ya sake janyo masa bakin jinin da babu yadda za'a yi sai zunde a bayan ido.
Chapter 113 · 0% Book details