← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 146

Sashe 66

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya maze ya ce "Ni nasan hankalin ki yawa ne da shi ai". Na sake ce wa "Ban da dai ina tsoron fishin Baba ai da tun ranar da ka sanya aka shigar mini kicin da tun ranar zan bar maka gidan, ita sai ta zauna kawai a madadina". Da sauri ya bar kan kujerar ya gurfana a gabana, ya ru'ko dukkan hannuwana ya sassauta murya ya ce "Asiya" cikin wani irin yanayi. Na kasa amsa wa, karon farko da ya ri'ke ni ban fizge ba. Domin gaba'daya maganganun Baba ya dagargaza ni, ya fahimtar da ni zama da Tijjani tilas ne. Zamana lafiya a gidan aurena yana nufin farin-cikin mahaifina na tabbatar Gwaggo ma ba zata so ta gan ni a gabanta da sunan mutuwar aure ba. Na zum'bura baki na ce "Uum". Ya yi kasa da murya ya ce "kalle ni". Na sake juyar da fuskata ba tare da na kalle shi ba. Da wata irin murya ya ce "Pls mana Asiya Toro". Na zakuda da sauri, na fara kokarin cire hannuna a nasa. Ina ce wa "Ai dai kasan bana son gatsa mini sunana da kake yi." Da azama ya ce "Indai zaki daina yi mini rashin kunya ai daga yanzu na daina fa'da miki. Kwanaki kin ce mini bana goge kaya, bana saka turare. Yanzu na fara yi dan kisan ba abin da bazan yi dan na samu aminci da nutsuwar ki ba. Amma ko ki nuna kin gane na canja, balle ki yaba mini na ji dadi". Na bata rai na ce "Akan me zan yaba? Bayan ba dan ni ka yi ba. Ina ce jiyan da ka fita sai da dare ya raba kana zan ce, idan ta yaba maka ai shike nan" Ya kame baki ya ce "Tabdi jam! Ya bar maganar ya canja da ce wa "Yanzu zan sake ba ki hakuri, ki manta maganar shiga kicin din ki. Na yarda na yi kuskure, dan Allah ki shafe ta a zuciyar ki. Nima na yafe miki zargina da kika yi jiya. Kin ga dai murna da addu'ar da Baban Marina ya yi. Kamata ya yi mu ha'da kanmu mu zauna lafiya". Na bata rai na ce "To ai kai abin haushin ka yawa ne da shi Tijjani. Bana son na ga namiji ya cika kule kulen mata, kai kuma kana tafiya a mashin ma kana iya tsayawa ka yiwa mata magana ko baka sansu ba". Ya sake ru'ko hannuna sosai ya ce "Billahillazi a da ne Asiya. Tunda muka yi aure bana yi, na rantse miki da Allah. Mussaman da kika ce mini mai kamun kai kike so, sai na sake kame wa sosai". Na yi shiru ya ce "shike nan komai ya wuce zamu zauna lafiya, zaki yarda na zama mijin gaske ba na wai ba?" Na ce "Sai ka yarda wanccan dakin ya zama zan yi yadda nake so a cikinsa". Ya ce "Kin san ban iya yaudara ba. Idan kin yarda na zama mijinki na sosai, ai gaba'daya ma ya zama naki, to me zan yi da shi?" Na ce "Ban gane ba?" Ya jima yana kallona har sai da jikina ya amsa sannan murya a dashe tabbacin ya shiga cikin shauki sosai. Ya ce "Idan dakinki ya zama shine nawa, kayana sun koma ciki, kin adanasu tamkar yadda kika adana na ki, sannan a ciki zan dinga kwana, a ciki zan yi komai. Shike nan dakin ya zama na lallen ki da duk bak'on kwana da zamu yi". Gabana ya yanke ya fa'di tamkar yanzu na fara jin ya kamata ya dawo dakina". Na yi k'asa da kaina na kasa ce wa komai. Ya marairaice fuska ya ce "Ki ce to Asiya, na matsu ki zama matar aure ta sosai, na k'osa ki zama babba." Kunya ta kama ni, na rasa yadda zan yi, sai kawai na fara kananun kukan shagwaba tare da ce wa "Ai yanzun ban girma ba kake nufi?" Da sauri ya ce "kin girma mana, shi yasa nake son na sake mayar da ke babba sosai". Na sunkuyar da kai na k'asa domin kunya ce ta sosai ta yi mini k'awanya. Ya dinga murza mini tafin hannuna wanda hakan ba k'aramin abu ya haifar mini a gangar jikina ba. Haka shima gaba'daya ya yi sanyi ido ya canja. Kunya ta sake kama ni. Kan dole sai da ya sake wanka kafin ya tafi sallar la'asar. Nima dai abin da na gani na kasa gane wanka zan yi ko tsarki. Dan haka sai na yi wankan gudun kokwanto. Na dinga mamakin lokacin da muka cinye bamu nemi ko abinci ba. Na shiga kicin na dauko plask din abincin wanda jallof din shinkafa ne. Na koma na dauko plates da cokula. Ya dawo ya tarar da abinci. Ya ce "Kamata ya yi muci a plate daya Asiya". Ga mamakinsa sai ya ji na ce "To." Na zuba mana, muna ci yana yi mini hira kala kala. Muna gamawa ya kalli agogo ya ce kwaso kayan ki na wanke miki". Na girgiza kai na ce "Bar shi zan wanke da kaina". Ya mike ya na ce wa "Bari na debo da kaina. Kan dole na bar masa wankin nan ya yi, ina baranda yana ta faman zuba mini hira. Ni kuma na kasa tanka masa, sai dai eh ko a a. Da daddare yana tafiya sallar isha na rufe k'ofata. Da ya dawo ya ga na rufe. A hankali ya dinga buga mini tare da kiran sunana, amma na kasa bu'de masa. Wata irin fargaba ta dinga ratsa ni. Kan dole ya hakura ya bar ni. Da safe da na fito ya amsa sallamar da na yi masa, kansa na kan doguwar rigata da yake goge wa. Tausayinsa ya tsirga mini, duk yadda na rufe masa k'ofa, kuma ban yarda na bu'de masa ba, bai sanya ya fasa goge mini kayana ba. Gasu nan birjik a gabansa da alamu ya jima yana yi. Tunda rigar da yake kan yi ne ta k'arshe. Sai da na yo brush na ce masa "Ina kwana?". Ya amsa babu yabo babu fallasa" Da ya gama zai fita na ce "Zaka dawo ne da rana?" Ya girgiza kai tare da ce wa "To me zan dawo na yi?" Na yi shiru sai na ce "To idan an zo k'unshi zamu shiga d'akin, kada ka zo ka dizga ni." Ya girgiza kai alamun bai yarda ba. Ya bu'de baki ya ce "Ban yarda ba. Kada ki fara, idan kuma kin ki ji, to ki tabbatar zaki ga abin da baza ki so ba". Na Kwakkabe fuska tare da fa'din "Amma dai kai ne ka ce zai koma nawa". "Na fa'da tabbas. Amma ai na fa'di sharadina. Baki yi abin da na ce ba, dan haka kada ki sake ki kai mini mutane d'aki". Daga hakan ya fita. Ina gama abun da zan yi. Na fara tunanin yau laraba, zan samu masu kunshi sosai har zuwa gobe. Ina matu'kar son sana'a ta, ina samun nisha'di da walwala a cikinta. Sannan ina son na dinga aika wa iyayena wani abu. Idan bana sana'a kuma bazan samu wannan alherin ba. Na tabbatar kuwa matu'kar da kayan Tijjani a dakin da nake son ya zama na zaman sana'ata, to kuwa da sannu zai kore mini jama'a. Na zabura na shiga dakin na dauko jakar kayansa. Na kai ta d'akina. Na sake dauko kwalin makorinin da ya zuba takalmansa a ciki. Na fito da shi tsakar gida na bu'de. Kafa hudu ne da alamu biyu a lokacin aurenmu ya siyesu tunda sabbi ne. Na goge su na kai su daki. Jallabiya da tawul din da suke rataye, na fito da su na shanya tunda da danshin ruwan wanka a tare da su. Bargo da filon kawai na ninke na barsu gefe daya. Na dauko kaskon turaren wuta da yake ci a dakina na saka na sakayo k'ofar. Cikin sauri na d'ora shinkafa da wake. Na kammala na ji almajiri yana bara. Na kira shi na bashi naira dari ya siyo mini salak da kokomba, domin kayan ganye sau'ki ne da su a Toro tunda muna kusa da Jos. Nan da nan ya siyo mini, na bashi guntun burodin jiya. Ina tsaye na yanka na wanke na rufe shi. Na ha'da kwanukan da na bata na wanke. Na shiga wanka. Na shirya cikin doguwar riga cotton mai gajeran hannu. Na saka hular da ta dace da rigar. Na kalli agogo na ga shad'aya ne da rabi. Ai kuwa sai ga wata ta zo kunshi da kitso. Na bude dakin muka shiga, na fara yi mata lallen, cikin kankanin lokaci na gama saka mata. Na dauko kujera a kicin muka fara kitson. Mun yi rabi sai ga tawagar yan mata wajen su bakwai har da amarya. Murna ta kama ni, domin ku'di zan samu ba ka'dan ba. Sannan bana cikin zullumin wula'kancin Tijjani. Ina gama kitson na fara yiwa amaryar tunda nata yafi wahala na salatif ne. Na gama yi mata, na fara yiwa daya cikin kawayen na ji k'arar mashin dinsa. Ya shigo da sallama. A zabure na mike na fita y'an dakin suka bini da kallo. A bakin kofar na tare shi da ce wa "Sannu da dawowa". Bai amsa ba ya sha kunu ya fara kokarin shiga d'akin duk da na tare k'ofar. Baki na rawa na sake ce wa "Sannu da dawo wa, muje ka sha ruwa, ka ga ni". Bai musa ba. Ya yarda ya bini zuwa d'akina. Na nuna masa jakar kayansa da take gefe akan kwalin takalmansa. Na ce "Babu kayan ka a dakin Wallahi. Ka ga tawul dinka ma?" Na d'aga labule ya gan shi akan k'ofa. Ya daure fuska ya ce "Indai a hakan zaki bar mini su, to kawai ki mayar mini abina can." Idona ya ciko da hawayen takaici. Murya na rawa na ce "Kawai dai sana'a ce baka son na yi Tijjani. Ban da haka, ga yadda ka ce na yi, zaka bar mini d'akin, na yi kuma ka ce ba haka ba". Ba wasa ya ce "Ai ba ki adana mini su kamar yadda kika adana na ki ba. Kin ajiye su tamkar suna wancan d'akin dan haka mayar mini su can din kawai." Da sauri na
Chapter 66 · 0% Book details