← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 146

Sashe 105

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

***
Da azahar na dira a Bulkachuwa. Babah sai ganina ta yi kwatsam. A sanyaye ta shiga yi mini barka da zuwa. Sai da na yi sallah ta bani abinci da ruwa, na ta'ba ka'dan na rufe. Ta zuba mini ido ainun. Ta ce "Wai mene ne damuwar ki ne Yabi? Maimakon tunda yanzu ba shayarwa kike yi ba, ki murje ki cike, amma kullum sai fige wa kike yi tamkar wacce ake tsakurarki?."
Na yi k'asa da kaina, ba tare da na ce komai ba. A tausashe ta ce "Yanzu me yasa kika taho ba shiri ba komài?"
Na fara hawaye, ba tare da na bu'de baki na ce komai ba.
Ta ri'ke hannuna ta ce "Da ke da Ihisan daya nake jinku. Dan haka zan fa'da miki gaskiya. Gaba'daya aure hakuri ne. Ba yadda ake so ake ga ni ba. Idan Ubangiji yasa farin yafi ba'kin yawa a cikin zamantakewar sai a yi ta gode wa Allah. A kuma yi hakuri da inda aka kuskure. Idan kuwa ba hakan ba sai ki ga gidan aure ya zama tamkar kurku dan tsanani. Adadin mutuwar aure ya yi ta tunbatsa. Yin sassauci da kawaici babban jigo ne da yake rike da gidajen aure.
Cikin kuka na ce "Wallahi ina yi."
Ta ce "Na sani. Yanzu fa'da mini abin da ya yi miki har kika kasa hadiye wa"
Cikin kuka na tsara mata yadda muka yi da shi, ban yiwa al'amarin kwaskwarima ba. Da kuma kafewar da ya yi sai ta zauna da mu saboda tana da alkairai masu yawa a idonsa. Cikin kuka na ce "Ni kuma Wallahi bazan yarda na zauna da ita ba".
Ta yi shiru, na tsawon lokaci kafin ta ce "Tashi ki je d'aki ki yi kwanciyar ki. Kar kisa wannan maganar a ranki. Kina da gaskiya dan hakan zan tsaya miki, da kuwa baki da gaskiya da a yau zan mayar da ke dakinki".
Dad'i ya kama ni. Babah ta fahimci irin rad'ad'in da nake ji. Ina kwance ta shigo ta ce "Kuma sai kika bar mata yaran?"
Fuska ba walwala na ce "Eh". Ta ce "Da kin taho mini da su, ina cikin kewarsu ainun. Amma bar masa din da kika yi akwai hikima mai yawa tunda ba sha suke yi ba. Kukan Hamim kadai ya ishe su ai. Ki yi zamanki ba wanda zai san kina nan tunda Umman gidan nan tana garinsu tafi wata a can. Ko Nasiru ma baya gari. Aliyu ne ya ce zai zo yau, to kuma ya fasa sai satin sama, saboda zasu je Ibadan".
Ta dauki abin da zata dauka ta fice. Tana fa'din "Da ni yake zancen".
Sai da dare ya fara ja sannan ya koma gida. Bayan Nasiba ta masa text din ta sauka lafiya. Tunda ta kira shi ya fi sau biyar yana gani amma bai dauka ba.
Da asuba ya kira wayar Yaya Ummi.
A d'an tsorace ta ce "Yaya Bulkachuwa barka da asuba"
Murya na amo ya ce "Ummilolo taimake ni ki bani lambar mijinki na nemi izinin aikenki yanzu zuwa gidan Marina".
Ta ce yana jinka ma yanzu haka, na saka ta a sifika ka tambaye shi."
Ya bu'de murya cikin ladabi ya gaishe shi. Ya kuma roki alfarmar zai aiki Ummi zuwa gidan akan wani al'amari da tayar masa da hankali.
Nan da nan ya ce "Babu komai na amince ta je. Ya mika wayar ga Ummi.
Ta ce "Ya ya ne Yaya Bulkachuwa?".
Cikin zullumi ya ce "Asiya ce ta yi mini yaji Ummi! Tun jiya ta fice ta bar mini gidan da yara."
A zabure ta ce "Subhanallah a kan me Yaya Bulkachuwa?"
A sanyaye ya ce "Hmm! Kawai mu bar maganar tattauna wa ki tashi yanzu ki je gidan, ki duba ko ina. Idan kin ganta kada ki nuna komai kawai ki dawo gidanki. Ki fa'da mini sai na taho".
Yana rufe baki Ummi ta ce "Gaskiyar magana ban jin Yabi zata iya zuwa gidanmu da sunan yaji. Ta tsani yamididi, tana kuma matu'kar tsoron bacin ran Baban Marina".
Ya fesar da iskar damuwa ya ce "To saboda Allah ba kisan inda take ba Ummilolo?"
"Wallahi ban sani ba, ko waya bamu yi da ita ba. Amma bari na je sumame gidan Nazira".
Da sauri ya ce ",Yauwa Ummilolo, na gode, hanzarta dan Allah".
Ta ce "Zan sallami mutanan gidan da abin karyawa tukun".
Akan dole ya ce "To."
A hanzarce ta gama dumame ta sallami kowa.
Kusan da sanda ta shiga gidan Nazira domin ta tabbatar mijinta baya nan. Amma bata ga wata alama mai kama da rashin gaskiya ba. Suka gaisa ta tambayi yara.
Ta ce "Daga ina Yaya Ummi?"
Ta ce "Mafarkin ki na yi Nazira shi ne na taho dan na ganki, na ga lafiyarki".
Da'di ya kama Nazira. Ta ce "Madallah da Yaya Ummi. Kin kuma tarar da ni lafiya, har na karya na yi hidimar gida".
Ta mike tana fa'din "Alhamdulillah! Tunda na ganki lafiya bari na tafi".
Ta hanzari Nazira ta yi kicin dinta ta juyo mata dafadukan macaroni mai dan dama a madaidaicin filas. Ta ce ga shi ki kaiwa yaran nawa. Na maigidan ne bai tsaya karyawa ba. Ana ta jiransa zasu je Lame. Ya dai sha kunu a tsaitsaye."
Ta karba da godiya ta tafi. Maimakon ta zarce gidan ta, gidan Marina ta yiwa tsinke. Duk wani bin kwakkwafinta bata ga ko ganin wata alama da take nuna sun san Yabi bata gidanta ba. Dan haka suma ta yi musu sallama ta tafi ba tare da ta bu'de musu komai ba.
Sai da ta isa gidanta sannan ta kira Bulkachuwa ta tabbatar masa Yabi bata zo Toro ba. Ya lalube ta anan Bauchin.
A rikice ya ce "Yanzu Ummi abin da Asiya ta yi mini dai-dai ne?"
Kai tsaye ta ce "To ai bansan me ya faru ba Yaya Bulkachuwa".
Ya ce tsaya ki ji, ki fa'da mini inda nake da laifi, ki kuma fa'di shin ta kyauta mini kenan?"
Ta ce "To zan fa'di gaskiya tsakanina da Allah kuwa".
Ya numfasa ya shiga koro mata bayani tiryan tiryan na gaskiya.
Bata katse shi ba sai da ya gama tsaf ya ce "kin ji abin da ya faru".
Ta numfasa ta ce "Ka yarda gaskiyar magana zan fa'da?"
Da sauri ya ce na gasgata ki Ummi. Komin tasirin jini na sani zaki yi adalci domin ke din mai kauna ta ce na shaida."
Ta ce "Na gode sosai. Amma gaskiyar magana kai ne baka kyauta ba. Kasan Yabi tasan akwai tsohuwar soyayya tsakaninka da Nasiba. Yanzu Kuma bata da aure. Akan wanne dalilin zaka dauke ta da kanka ka kai ta gidanka da sunan ta zauna, ba zama irin na bakunta ba.? Me yasa da Yabi ta ce bakuntar kwanaki uku ta amince ta yi muku baka yarda kun fahimci juna ba? Me yasa ka ankarata ta hanyar ce wa Nasiba tana da darajar da ba zaka kore ta a gidan ka ba?. Tsakanina da Allah wannan maganar ta yi nauyi a zuciya. Ai da sai ka ce mata ita ta kore ta, shi kenan magana ta k'are."
A sanyaye ya ce "Na gode na kuma yarda na yi kuskure. Amma me yasa ta zarge ni?"
Kai-tsaye Ummi ta ce "Kai ka bada k'ofar. Me yasa dan Nasiba zata zo gidanka sai ta hannunka zata biyo? Ba Yabi ce matar gidan ba? Me yasa sai da kanka zaka kai ta? Me yasa ka kausasa harshen ka akan zamanta?"
Ya ce "Yanzu dai Ummilolo Yabi ta yi dai-dai da ta fice ta bar gidan babu izinina?" Ta numfasa sannan ta ce "A fuskar shari'a bata kyauta ba. Amma tunda ni mace ce nasan yadda take jin zafi a zuciyarta bata yi laifi ba, tunda ka nuna wacce bata zama dolen ka ba sai ta zauna mata a gidan ko tana so, ko bata so, ba tare da rarrashi ba".
Ya saki ajiyar zuciya ya ce "Na gode sosai Ummi. Na kuma gamsu da wannan gaskiyar ta ki babu son kai a cikinta. Kuma yanzu hakan tun jiya na saka Nasiba a mota ta dawo Toro. Na sallame ta a kurarerren lokaci ko?"
Nan ma Ummi ta ce "Eh, baka girmama ra'ayin matarka ba, sai da ka bari ta yi maka tutsu, hakan kuma zai haifar muku da tazara da tsatsar zuciya mai yawa".
Cikin karaya ya ce "Na gode bari na shirya yaran nan, mu fita nemanta, ki taya ni addu'a, gaba'daya yarinyar nan ta gigita ni. Wato Yabi jidalinta mai girma ne."
Ummi ta kwashe da dariya ta ce ni fa ban ga laifinta ba Yaya Bulkachuwa. Haka kawai za'a lallaba a yi mata kutse mai dafa zuciya, da saka jinya a gangar jiki".
Ya numfasa ya ce "Allah ya sauwake, ni Wallahi babu tunanin komai a zuciyata akan hakan".
Ta ce "Kai kasan hakan, mu ina muka san zuciyar ka?"
Ya ce "Shi kenan bari na saka d'ambar neman ta."
Suka yi sallama, ya kashe wayar tare da zurfafa a tunanin ta inda zai fara nemanta.
A daddafe ya yi wanka saboda azabar kukan Hamim. Domin a bakin band'akin ya zauna yake kuka na tashin hankali. Hanif kuma sai ri'ke shi yake alamun wai ya yi shiru.
Dan haka ko da ya fito a rikice ya shirya, ya dauki yaran da yake ta gunjin kuka.
Yasan kukan neman Amminsu yake yi. Allah ya zuba masa k'ulafacin uwa. Ya gama shawo kan Hamim ya yi shiru, sai kawai Hanif ya fa'di ya dan bugu a goshinsa. Ya fara kuka shi ma.
Hamim da dama kukan ba daina shi ya yi gaba'daya ba, sai kawai ya bu'de baki yana taya Hanif. Suka rikice masa ainun.
Ya jima kafin ya samu su tsagaita. Shi da kansa ya fahimci d'a sai uwarsa. Duk da yadda ya iya raino. Amma rashin Yabi a tare da su sai komai ya k'wace musu daga shi har y'ay'an sa.
Har suka bar gidan bai yanke shawarar inda zai dosa ba.
Amma yana hawa titi zuciyarsa ta fi rinjayar masa ya je Bulkachuwa.
Dan haka gidan mai ya shiga ya sha mai. Ya siya wa yaran yoghurt da cake. Sannan suka dau hanya. Yana yi yana daukar fasinja dan ya samu sau'kin tsadar mai.
Da walwala Babah ta karb'e su. Tana ta tambayar ya aka yi suka baro Yabi a gida ita kad'ai?
Ya dan diririce, bayan ya ga rashin wasa a fuskarta. Murya babu karsashi ya ce "Bata jin da'di ne shi yasa bamu taho tare ba, nima kayan miya na kawo nan Dambam".
Ta ce "Ayyah me ya same ta? Ko zazzabin damina ne da ko ina yinsa ake yi".
A sanyaye ya ce "zazzabin cizon sauro ne, amma da sau'ki rashin k'warin jiki ne kawai."
"To Ubangiji ya bata lafiya". Ya amsa da Amin cikin damuwar to ina Yabi ta fantsama kenan?
Ya kasa ko da shan ruwan da yake gabansa bare kuma abinci. Yara dai suna ta cin abincinsu.
Ta zauna tana fa'da masa sati mai zuwa Aliyu zai je Ibadan yin jarabawar zama likita, tunda karatun likitanci yake yi a jami'ar Jos.
A gajarce ya yi murna da fatan alheri. Ta fahimci rudun da ya shiga amma ta matse ta yi kamar bata gane ba.
Ya sassauta murya ya ce "Tafiya zan yi, zan bar yaran a nan, zuwa jibi zan dawo".
Cikin nutsuwa ta ce "Haka kawai ka dauko su babu shirin zasu zauna ka bar mini su? Uwarsu ba zata ji dadi ba".
Ya basar ya ce "Ko ba wajen ki na kawo su ba, har ta yi mini inkarin inda na kai su bare kuma wajen ki ne".
Da azama ta ce "Wallahi ba zaka bar su ba, tunda kai ma ba da nufin su kwana ka taho da su ba. Kaya kala daya ka sako musu a leda. Nasan kuma idan sun bata na jikinsu a sauya musu ne iya yau. Ka bari idan ka shiryo su da kayansu sai su zo mini, amma ba haka kawai a shiga hakkin uwa da y'ay'an ta ba".
Ya rasa yadda zai yi, a kan dole ya kwashe su suka juya.
Ni da nake mak'ale a daki, zuciyata sai tsalle take yi a kan na ga yarana. Da k'yar na daure ban fito ba.
Da suka tafi kuwa sai na ji tamkar na ruga a guje na ce "Ga ni nan".
Chapter 105 · 0% Book details