← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 146

Sashe 94

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washagari muka yini cikin nutsuwa da walwala mai yawa. Tun safe kuma na yi status da cewar gobe idan Allah ya kai mu zan fara k'unshi.
Shike nan na ha'kurkurtar da zuciyata na manta komai.
Na rungumi mijina da sana'a ta. Illah iyaka na yanke mua'amala da Rafi'a. Mahaifiyarta kuwa ban fasa gaishe ta ba, ban fasa mutuntata ba. Illah iyaka shiga ne bana yi. Ita ma kuma Rafi'a din ta daina shigo mini.
Wata biyu da faruwar hakan na fara wani irin zazzabi mai zafin gaske. Domin kwana nake yi mutsutsukun ciwon jiki. Gaba'daya ji nake tamkar ana kwankwatsa mini kasusuwan jikina. Ga bana iya cin abinci.
Haka nake kwana ina yini cikin wannan halin. Sa'armu d'aya akwai kayan abinci tare da mu. Sannan yana k'ulla lallen da siyar da ruwa. Babu matsalar babu sosai a tare da mu. Kwana biyu ina ta shan maganin zazzabi da na rage rad'ad'in ciwo. Amma babu sau'ki kullum gaba ciwo yake yi.
Hakan ya sanya shi fita ya yi buga bugarsa ya samo ku'di ya ha'da da wanda muke da shi, ya kai ni asibiti.
Yini muka yi domin sai da aka k'ara mini ruwa. Aka yi mini gwaje gwaje.
Da yamma aka sallame mu bayan sun tabbatar ina da ciki na wata daya har da sati biyu.
Duk yadda nake jin rashin kwarin jiki amma sosai na yi murna. Ni da Tijjani ban san wanda yafi murna da zumudi ba.
Muna isa gida na dauki waya na k'ira layin Gwaggo.
Tana dauka ta ce "Yabi ya jikin dai?"
Da azarbabi na ce "Hmmm Gwaggo ashe duk wannan wahalar da murkususun da nake yi ciki ne da ni!"
Ta yi shiru, sai kuma ta ce "Ni kika kira ki fa'da wa hakan Yabi? Wacce irin marar kunya ce ke haka?"
Na yi sakare domin ni ban ga wani laifin ba. Ita ce uwata bani da wacce ta fita a halin yanzu. Ita ce mafi kusa na tattauna dukkan farin-cikina da ita. Zan yi kokarin na boye fa'da mata damuwar da nake ciki domin na yi amanna damuwata zata tsayar mata da dukkan farin-cikinta ne.
Na sanyaya murya na ce "Gwaggo ki yi ha'kuri. Ina cikin murna ne. Kin san kwanaki a gidan nan aka fa'da mini ce wa Tijjani ya gama zubar da yaransa a titi ni bazan haihu ba. Sannan kuma ke da bakinki kika ce sai na haihu da ki zo ki ga muhallina".
Ta sassauta ta ce "To ba sai ki bari na fahimta ba, ko na ji a bakin yayarku ko kuma Nazira".
Na ce "To sake yin hakuri Gwaggo ai yanzu na fahimta. Idan zan yi ta biyu, bazan fa'da miki ba. Sai dai kawai a ce miki Yabi ta haihu"
Ta ja tsaki ta ce "Allah dai ya baki lafiya" tare da kashe wayarta.
Tijjani da yake gefe yana ta faman murmushi ya ce "Burinmu ya cika.
Yanzu fa'da mini sunan nawa?"
Na yi dariya na ce "Ai sai na haihu".
Ya girgiza kai ya ce "Kin ce da zarar kin samu ciki zaki fa'da mini fa".
Na ce "Haka ne".
Ya ce "To fa'da mini na ji".
Na murmusa ka'dan na ce "Abbanta".
Ya kwashe da dariya ya ce "Wanne irin suna ne wannan? Duk yadda kika kwadaita mini zakuwar samuwar cikin a iya wannan sunan zan k'are?
Abbanta kuma. Wace ce?"
Na jingina a jikin kujerar na ce "Bebin mana."
Ya sake fa'dada dariyarsa ya ce "To idan namiji ne fa?"
Na ce "Ai kuwa sunan da zan fa'da maka mai wuyar samu ne indai namiji na haifo tunda na fa'da maka mai kama da kai nake so".
Dadi ya kama shi ya ce "Allah ka kula mini da Asiya. Ka taya ni son ta, ka shiga dukkan kasafinta. Duk al'amarin da zai dunfaro ta, Ubangiji kada ka bar ta da iyawar ta.
Na ce "Ameen" a gajiye domin wai maganar da na yi har na gaji na fara haki.
Haka nake kwana da yini babu lafiya. Duk dare bama barci kwana muke muna fama. Domin gaba'daya ni dai babu sau'ki. Kwana nake magogo. Haka kuma Tijjani baya runtsawa. Tausa yake yi mini, da fifita idan babu wuta. Tin a lokacin muka fahimci zama iyaye ba karamin al'amari ba ne. Duk yadda na zaku na samu ciki sai da na fara sare wa. Murnata ta fara koma wa ciki dan tsananin wahalar da nake ciki.
Al'amura suka fara yi mana tsauri a dalilin ku'di ya fara yanke mana.
Haka da safe idan ya tallafa mini na yi wanka, ya shafe mini jiki da man zafi zai fita ya dan yawata. Idan an yi sa'a ya samu aiki ya samo ku'di, zai siyo mini 'dan abin kwadayi. Watarana kuma hakan zai dawo.
Baya kuma nisan kiwo, ko ya fita hankalinsa na kai na.
Sai na samu sau'ki, sai kuma jikin ya sake rikice wa.
Na fara gazawa. Rannan Baban Marina da ya zo duba ni, ya ga yadda na koma gaba'daya na yi yaushi.
Ya bashi umarnin ya kai ni gida, ko shima ya d'an huta.
Bai musa ba kuwa washagari da hantsi ya dauke ni da jakar kayana ya kai ni gida. Har da siya mini su maltina da madara da indomi da zan dan yi kwanaki ina ci. Wanda na tabbatar ya ha'da da bashi.
Da k'yar na shiga muka gaisa da Dada wacce bayyana farincikin da ta yi a dalilin samuwar cikin bata lokaci ne.
Ya kira Ikilima ta ri'ke ni zuwa cikin gida. Na sani kuma dan ya mutunta iyayenmu ne ya sanya bai ri'ke ni da kansa ba.
Yadda Tijjani ya ha'do ni da shirgi da maganganuwana. Sai ka rantse har cikin zuciyarsa yake nufin na zo na yi goyon ciki a gida.
Kwana na biyu a gida na fara samun sau'ki tamkar a gidana ciwon yake. Domin ina barci, da safe kuma ina shan koko na ci dumame.
Sannan Gwaggo da kanta take daddana mini jikina. Har gasa mini jiki take yi da tawul. Ga shi duk abubuwan da nake son ci na gargajiya ina samu.
Kwatsam ranar da na yi kwana uku sai ga shi ya ce shi ya gaji da rashina sai dai mu koma gida.
Na tubure akan sai na ji k'warin jikina.
Shima ya kafe. Kuma wai ni ce zan ce ina son komawa gidana.
Nan da nan na rantse akan bazan fa'da ba.
Ya jijjiga kai ya ce "Shike nan tunda babu taimako da fahimta a tsakaninmu. Ni zan fa'da wa Baban akan na gaji ina son ki koma dakinki. Dama kunya da nauyinsa ne suka sanya na kawo ki."
Da yamma ya dawo akan na taimake shi mu koma gida. Ya kasa fa'dawa Baban zai tafi da ni. Na ce "Ni dai na fi son zaman nan".
Nan da nan ya tunzura ya ce "Saboda bani da ku'di ko Asiya?"
Na kalle shi a razane. Ya ce "Haka ne mana. Inba hakan ba wace ce ta taba zuwa gida dan bata da lafiya a gidan nan?"
Na ce "Ubaida bata dawo ba?"
Da hanzari ya ce "Amma duk jinyar da ta yi da ciki ai bata dawo ba. Sai da ta haihu. Ke kuwa ai ba haihuwa kika yi ba. Idan ba gazawa ta aka ga ni ba. Mene ne zai sa ayi mini wannan umarnin?"
Na sake kallonsa cikin tu'ajjibi na ce "Baban Marina kake fa'dawa hakan ko kuwa wa?"
A tunzure ya ce "Asiya na ke fa'dawa saboda ita ce zata ce masa ta samu sau'ki."
Idona ya ciko da hawayen takaici na ce "To".
Daga hakan na k'ulle bakina ban ce masa komai ba.
Ganin hakan sai jikinsa ya yi sanyi. Ya ce "Ya muke ciki?"
Ko kallonsa ban yi ba.
Ya gama zamansa ban sake kula shi ba.
Da daddare ma ya dawo, ban yarda na kula shi ba. Domin idan akwai abin da yake b'ata mini rai da shi idan muna magana ya dinga sako babun shi ne. Na kuma lura idan ban taka masa birki ba, ba wanye wa k'alau zamu yi ba. Tunda yana nema ya mayar da ita sara.
Washagari sassafe sai ga Babah ta Bulkachuwa ta dira a gidan. Ina daga daki na ji suna gaisawa da Baba. Ya ce " Hauwa kamar ba kwanaki ka'dan da suka shud'e kika zo duba y'arki ba. Me ya sake dawo da ke kuma yanzu? Mata kuna da son sabgar yawo.
Ta ce "Ba hakan ba ne Yaya. Shi ne ya mini waya wai jikin Yabi ya yi tsananin da ka ce ya dawo da ita gida. Sai ya ro'ki na zo na zauna masa da ita. Ni kaina hankalina ba kwanciya zai yi ba idan ba zuwa na yi na ganta ba."
Baba ya numfasa ya ce "Ai shi Tijjani bai gamsu zan kular masa da iyali dan karan kansa ba, sai ya zargi na yi masa fin k'arfi saboda y'ata ce?".
Ta diriri ce ta ce "Haba Yaya ni Wallahi har kasa na ji babu da'di."
Ya ce "To ki ji mana. Ban da dai ke ma kin banbanta ta ya ya zaki zo ki ce mini "Zaki dauki matar Tijjani a gaba na?"

✍️

*UMM NIHLA COLLECTIONS*
*Ta k'ware wajen kawo yadina masu kyau da sauki, cotton da silk, embroidered, Batik*
*A Malaysia take daga can kuma take turo su Kano direct. Dan haka kayanta akan farashi sari take bayarwa, daga guda daya har zuwa dari zaku samu*
*Kayan ta masu aminci da rahusa ne, ku tuntube ta Whatsapp dan ganin JERIN gwanon yadinanta da basa kode wa ko jeme wa*.
*07020695644*
*What's app only*.
Chapter 94 · 0% Book details