← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 146

Sashe 126

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta dauko salatil fathi sai ta rikice ta dauko ashafa da k'yar dai ta fara karanta casa'a ta sauke ta. Tana yi tana ce wa "Rabbani a saukakawa mai babban suna, a tausayawa wadannan y'aya' nasa". Da k'yar Baban Marina ya hakurkurtar da mu aka daina kukan. A dakin Gwaggo na yada zango. Dakin da nake matukar samun nutsuwa a cikinsa. Amma a yau sai na ji ina cikin matsanancin kunci da zullimi domin sai nake ganin tamkar ana shirin raba ni da Tijjani ne. Na ga tsayin wannan dare tamkar dai ace gawa ce a dakin. Ban yi barci ba. Karfe uku na ga Gwaggo ta fita ta dauro alwallah. Duk yadda na ke cikin zullimi sai da na tuna irin wannan yanayin muka shiga a lokacin da aka zartar mini da hukuncin auren Bulkachuwa. Yau kuma ina kukan bak'in cikin nisanta ni da gidansa da aka yi. Gwaggo tana shigowa da alwalarta, nima na zabura na mik'e na doro alwalar. Muka dinga nafila muna shigar da bukatunmu. Ina kuka hannuwana na sama "Tijjani, Tijjani kawai nake iya fad'a gabad'aya kaina ya kulle. Domin dawo da ni gida ya yi matukar sake tsorata ni. Me yasa za'a raba ni da dakina? Kwanaki biyu kacal a gidan Marina na gane masu farinciki yadda na shiga cikin garari sun rinjayi masu tausayi da rarrashina. A k'ofarmu kam babu wanda yake takura mini ko habaici. Amma da zarar na fita da NIYYAR zuwa wajen Dada sai na samu wanda ya yi mini yarfe ana mini habaicin dama karyar arzikin da a muke yi ba mai tsarki ba ne. Har ta kai bana k'aunar na fita. Amma idan ban je ba sai ta aiko wai na je, a wannan lokacin k'warai Dada take tausayina ni da yara. Kullum a cikin sadaka da addu'a take yiwa Tijjani. Kuka kam bansan wa yafi yi a tsakaninmu ba. Ta damu k'warai har jininta ya hau. Ban sake samun damar gano Tijjani ba har aka yi sati da zuwanmu. A lokacin kuma na fara gazawa. Tashin hankalina na sake hauhawa. Baban Kasuwa da na Tsakiya babu wanda ya tako kafarsa da nufin yi mini jaje. Ashe wai na yi laifi da ban bisu kofofinsu na gaishe su tare da yi musu jaje tunda ai su d'ansu ne tun kafin ya zama mijina. Ni luma damuwata ta girmi tunanin zuwa gaishe gaishe. Sannan mafi yawa a wajen Dada nake ganinsu na kuma gaishe su a mutunce. A lokacin na sake fahimta tare da gasgata idan Baban Marina ya kauce bamu da wanda zai tsaya kai da fata ya tallafemu idan mun shiga cikin kalubalen rayuwa. Tausayin k'ananun y'aya'n Baban Marina ya sake rub'anya tashin hankalina. Gabadaya na zama tamkar wata zararriya, na k'are na fige tamkar kudin guzuri. Bayan addu'ar da nake yi wa Tijjani da y'aya'na, sai na sake tsananta addu'ar Ubangiji ya sanya soyayya da tausayi mai yawa a tsakanin y'aya'n Baban Marina. Domin kam al'amarin Baffaninmu sai shukuran. Kullum mutuwa na daukarmu daya bayan d'aya amma bata zame musu izna ba. Abin da na sake fahimta kawai shaidan da son zuciya gami da hassada ne suka yiwa zumuncin yau k'awanya. Sassaucin rayuwar da Baban Marina ya samu a dalilin y'aya'n sa ya zama wani abin tattaunawa. Kullum a cikin fad'in ai yanzu ya farfado suke. Na tabbatar ba za'a bar ni na ji da ibtilain da ya fad'o mana ba, sai an tusa ni gaba da muzanci kala kala. Dan haka na kudire da na yi sati biyu zan fad'awa Baban Marina zan koma dakina tunda dai Tijjani bai mutu ba. Washagari muka tafi Kano da ni da Nazira da Yaya Salisu. Gabadaya Tijjani ya fita a hayyacinsa. Ina kuka nake fad'in "Basa baka abinci ko?" Ya girgiza kai ya ce "Abin nan da nake fad'a miki. Da zarar hantsi ko yamma, ta yi sai gabad'aya na rikice, zuciyata kamar ta yi bindiga wajen son na tafi Toro na ga Nasiba. Masifar zafin da nake ji a zuciyata da kirjina ya wuce misali ina fatan na mutu kawai Asiya". Na kasa ce wa komai. Yaya Salisu ya ce "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun! Allah mun tuba." Nazira kuwa kuka take yi tana fad'in "Dama nasan ba haka siddan ka runtse ido ka kafe sai ka aure ta ba." Ni kuwa na zama tamkar mutum mutumi. Domin a yanzu na yarda Tijjani na bukatar na samar masa da nutsuwa. Tunda duk yadda yake cikin wannan tashin hankalin amma yana fad'in yadda yake ji game da al'amarin ta. Na tabbatar ba son zuciya ko tozarci ba ne ya sanya yake fad'a mini yadda yake ji akan Nasiba ba. Cikin tausayi nake kallon sa gabad'aya ya zube, ya yi duhu. Tausayi, so, kauna suka sake yi mini rubdugu a dukkan zuciyata da gangar jikina. Murya a tausashe na ce "Ka tsananta addu'a ka kuma yi hak'uri. Da kaina zan kawo ta ka ganta". Ya zuba mini ya ce "Yaushe?" Na ce "Gobe ko jibi". Ya yi k'asa da kansa ya ce "Goben dai." Da k'arfin hali na ce "To". Ya kidime ya ce "Wanne irin to kike nufi Asiya?" Na ce na gaskiya da gaskiyar magana ". Ya saki ajiyar zuciyar samun nutsuwa ya ce "Ina twins, me ya hana ki zo da su na gansu?" Idona cike da k'walla na ce "makaranta suka bi yaran gidan." Haka muka ba shi abin da zamu ba shi. Aka tafi da shi. Tuni kuma an saka ranar da za'a gurfanar da shi gaban kotu. Sai dai Yaya Ammar ya tabbatar mana BAUCHI za'a dawo da shi. Tunda a cikin jahar Bauchi aka kama shi. Ba'a san dalilinsu na kawo shi Kano ba tare da sun sanarwa da kowa nasa ba har tsayin kwanaki biyu. Da yammaci sosai muka isa Toro. Muka tarar da Nasiba a k'ofar Dada domin mijin babarta aka kwantar a asibitin koyarwa na jamiar Jos. Lokacin da abin ya faru tana can bata dawo ba, sai yau aka sallame su. Babar tata ta wuce gidanta da marar lafiya. Ni da Nazira muna kallon yadda gabadaya ta takure ta kasa sakat tunda muka shiga. Akwai alamun tasku a tare da ita. Na yi jarumtar ce wa "Nasiba Bulkachuwa na ta jajen ki. Ya damu da rashin ganinki cikin masu zuwa duba shi tare da jajanta masa. Gobe zan koma, sai mu tafi tare ko ya samu nutsuwa". Ta kasa amsawa. Hatta Dada ma na kashe ta da kunya gabad'aya sun rasa me zasu ce. Yanayinsu ya sa na gane suma tamkar an tursasu ne akan sha'anin Tijjani. Washagari kuwa na shirya yara na ce mun tafi Kano. Baba bai so ba, amma saboda lallaba farincikina yake yi bai hana ba. Sai ma ya ce "Ubaidun Inna ya raka ni. K'ofar Dada na dire. Na tisa Nasiba a gaba muka tafi a kan dole ba yadda zata yi. Domin na lura tsoro nake bata. Har muka isa Kano ba wata hira a tsakaninmu. Sai kuma muka hadi da tasgadon y'an sanda. Wai ba zamu gan shi ba, ana yawan yi musu zarya da sunan ganin Tijjani bayan shi mai babban laifi ne. Hanif ya fashe da kuka yana ce wa "Zamu ga Baban 2 dan Allah ". Hamim ma ya fara kuka sosai. Watak'ila tausayi suka bawa wannan babban dansandan sai kawai ya bada umarnin a fito da shi. Ga mamakina sama da mintina goma da isowar Tijjani bai kalli inda Nasiba take zaune ba. Tunda ta gaishe shi ya amsa hankalinsa na kan su Hanif da suke kan cinyarsa bai sake bi ta kanta ba. Ni da yara kawai ya ke kulawa. Na mike na ce "Bari na baku waje tunda idona yasa ka kasa yin hirar". A zabure ya ce "Zan ci mutuncin ki little! Jiya da yau ban ji azabar da nake ji ba. Akwai abin da ake yi mini wanda zalunci ne da k'eta. Alfarmar Annabi kuma Allah zai kawo mini k'arshen al'amarin tunda kwana nake ina fad'awa Ubangijin al'arshi ya warware mini wannan masifar. Ni ko wannan k'azafin da aka yi mini baya gigita ni, kamar yadda al'amarin ta yake gigita ni. Amma akwai Allah." Ba Nasiba ba, ni kaina sai da na ji babu dad'i ainun. Na yi tsuru tsuru na kasa ce wa komai. Domin na tabbatar k'arshen muzanci Tijjani ya yi shi. Amma na sake gasgata surkulle ake yi masa. Ban da haka jiya k'iri k'iri ya fad'a mini yau na kawo masa ita. Ko tunanin rikicin da zan yi masa bai yi ba, saboda an ringa an kidima shi a kanta. Na daure na rakito ta, amma bai ko kalli inda take ba, sai ya b'uge da cin mutunci. Jikina ya mutu domin nasan zata zargi na kwaso ta ne dan na saka mijina ya wulakanta ta a gabana. Tunda a hakan kafatalin gidan Marina sun tafi akan na gama da Bulkachuwa tsorona yake ji. Sai abin da na shimfi'da zai bi. Har fad'i suke idan bana son mutum to ko kallon arziki Tijjani baya masa saboda gudun zuciyata. Ta mike a kasalance ta ce "Bari na jira ku a mota Yabi". Murya babu amo na ce "To". Tana tafiya ya saki dogon tsaki mai karfi da na tabbatar zai je kunnuwanta. Na zuba masa ido ba tare da na iya ce wa komai ba. Da k'yar na ce "To da sun san zasu mayar da kai Bauchin me yasa suka kawo nan?" Ya kalle ni ya ce "Akasi aka samu. Sun tsayar da ni a farko ban tsaya ba. Shine suka harbi tayar motar ikon Allah ne yasa motar bata yi bari da ni ba". Zuciyata ta buga da tsananin gaske na ce "mene ne dalilin ka na k'in tsayawa Baban 2? Ta ya ya kana dan k'asa amma ka ce ba zaka girmama dokar k'asar ba? Ko dai kasan dama baka da gaskiya ne?" Nan da nan ya kidime ya ce "Wallahi Tallahi ina da gaskiya, bansan an saka mini wannan abin ba. Ban sani ba, ki yarda da ni Asiya!. Na saki karfaffan numfashi tare da ce wa "Rashin tsayawar ka ba k'aramin hujja zasu kafa da ita ba. Na yarda da kai". Ya nutsu ya ce "Idan har kin yarda da ni to kowa ma
Chapter 126 · 0% Book details