Sashe 10
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba, amma Ubangiji ya cika zuciyarta da son addini, ta rabauta da yawan yin istigifari, matsalarta guda tana da son zuciya, matu'kar zaka bata abin duniya to zata juya gaskiya ta koma karya. Hakan kuma ya yi tasiri a zukatan ahalinta, domin kuwa a tsakaninmu ma mun k'ullaci yadda take fifita Nasiba akanmu, ta yadda ta fimu gata da iko a gidanmu. Kowa yasan Dada tafi son jikokinta da y'ay'anta mata suka haifa, mussaman su Nasiba sannan Bulkachuwa. Saratu ta ce "Dada muna dakon karatun ne, jiya kin ce addu'ar tsari da makarai da miyagu zaki d'ora mana." Ta dan yi tari ka'dan ta ce "Hakkun Saratu". Ta numfasa ta ce zan biya sau uku daga nan sai ku dinga fa'da bayan na fa'da." Muka amsa da cewa "To". Ta yi Basmalah, ta yi salati ga Annabi, sannan ta nemi tabarrakin SHEHU. Na yunkura zan yi magana sai kawai na yi maza na saka hannu na kame bakina. Da karsashi ta ce *"Wa makaru, wa makaru, Wallahu kairan makirina".* Na amsa karatun nata ina ganin kuskuren ciki ka'dan ne. Muna saurare har ta biya sau uku kamar yadda ta fa'da. Sannan muka koma tana yi, muna amsawa har kuma ta ce mu yi da kanmu. Muka dinga yi har muka rike dama kuma mun biya ayar a islamiyya. Ina son na yi mata gyara amma ina jin tsoron abin da zai biyo baya. Ganin mun ri'ke sai ta ce "To zan baku addu'ar farin jinin samari, ku yawaita yinta atafe kuke, ko a zaune ko kuma a kwance". Muka yi shiru dan nuna kunya. Ta numfasa ta ce *"Ya tifa risubuha ragadan".* Muka k'yal-k'yalale da dariya, na kasa daurewa na ce *"Min kulli.."* kafin na karasa ta ce "Lah! Ai iya inda na tsaya, zaku dakata, duk wacce ta yi karambanin cika ayar to ta kuka da kanta. Domin maza kala kala zasu yi ta bin ta har mazan dabbobi sai sun bi'de ta da sunan soyayya saboda karfin addu'ar, kunsan Annabi Isibu aka saukar wa ayar." Muka kasa cewa uffan domin kowa dariya ce a bakinsa yake gimtse wa". Ta kalli Nazira, Saratu, da Nasiba ta ce ku dimance ta babu kakkautawa kune masu nauyin jini, ke Yabi ba sai kin yi ba, ku kuma ragowan saffa saffa zaku dinga yi tunda kuna samun mane ma." Nasiba ta bata rai ta ce "wanne irin nauyin jini kike magana Dada? Duka duka fa shekarunmu sha shida ne wasu ma basu cika ba, ban da dai ana auren wuri a gidan nan ina ma muka isa a samu a sahun y'anmata a wannan zamanin?". Dada ta ce "A wajena kun wuce y'anmata ma kun zama iyayen mata, tunda ba wacce bata yin wanki duk watan duniya, ni kam kullum sai na yi tuba sama da sau dari uku, tare da addu'ar Allah ya cika mini burina wajen sallar layya ace ko wacce maneminta ya tsaya duk sai mu tattara mu rabu da ku salin alin. Amma a duk sadda na hango zugar ku gabana faduwa yake yi, inta shiga firgicin yadda sallolimmu suke goriya a madakata basa isa gaban Zati". Cikin dariya na ce "Wai a ina kike koyon wadannan karatun naki irin na makafi ne?". Haka kawai na fa'da ta rusa ihun da ya janyo hankalin ahalin gidanmu, mu kuwa gaba'daya muka zuba mata ido muna mamakinta, yayin da jikina ya yi mugun sanyi, zuciyata ta shiga kaiwa da komowa cikin fargaba mai yawa. Cikin kankanin lokaci dukkan iyayenmu maza sun bayyana, wasu daga cikin matan gidan suma sai iso wa suke yi cikin zullumi duk da dai ta kan yi irin haka sa'i, sa'i. Tana kukan tana fa'din "Yabi ce, Yabi ta zage ni, ta mini gorin mijina makaho ne". Mamaki ya sake kama mu, domin sai a ranar muka san kakanmu Alh Garba wai ashe ya makance a karshe karshen rayuwarsa, duk cikinmu ma ba wadda ta san shi bare har a yi mata gori, sannan dama ana gorin ciwo ne?" Haka Baban kasuwa da yake jin shine a saman kowa, ya hau cin mutuncina yana fa'din ba zai yiwu kullum sai na tozarta uwarsu ba. Zai dauki mummuna mataki a kaina ya ga take takena so nake na gagari kowa, to shi ba zai zame masa komai ba akan mahaifiyarsa ya kore ni daga gidan, ko kuma ya dauke Dada su bar mini gidan, idan ya so iyayena su shata jan layi da shi. Baban Marina kuwa cikin sanyi yake fa'din "Haba Iliya yaushe zan haifi y'ar da zata shiga tsakaninmu, komai zaka yi mata ai ka isa ne". Baban Tsakiya ya ce "A a ai yaran yanzu basu da kunya balle mutunci baka ganin yadda ta saka uwarmu kuka to mu kuma idan muka ce zamu shiga shirgin ya'yanka ai sai dai su rufe mu da duka tunda a cikin idonsu muke ganin bakincikin da suke yi da mu, tamkar dai mune muka hanaka ka sake tara arziki, ko muka hanasu yin zuciyar tallafa maka. Ban da lalace wa Musa ka'dai bai isa ya ri'ke kofarka ba? Ya'yanka wajen hudu ko biyar ne a daki amma duk wula'kantattu ne, basa taimaka maka da komai, amma abin kaico sun raina kokarinmu akan ka." Baban Marina ya sunkuyar da kai kasa gwanin tausayi yana fa'din sai ha'kuri da yaran yau, ni kuma har yau din nan basu fiye mini ku ba". Na kalli Nazira na ga hawaye na tsere akan fuskarta, na sake kallon ragowar, su Firdausi kowa idonta a bushe tabbacin basu da kaico akan cin mutuncin da iyayensu suke yiwa ubanmu. Na kasa hawaye a dalilin ba'kin cikin da yake cina yafi gaban hawaye. Ba abu mai ciwo irin wanda ba za'a barka ka keta shi ba, ya tisa iyayenka a gabanka da cin mutunci akan idonka. Na sake kai idona kan Dada da take matsar hawaye, na dinga mamakin yadda ta tara mini jama'a haka. Na gama yarda kafatalin jikokinta ba wacce take jiran kiris akanta iri na. Duk yadda Nasiba take zage wa suna yin sa in sa, hakanan kowa a cikinmu tana mayar mata da magana amma ba wanda take mayar da laifinta garma sai ni. Tausayin mahaifina ya yi matu'kar kama ni ta yadda kannensa suka tsaya a gabansa suke fa'da masa maganganun da komin sanyin halinsa sai sun mintsine shi. Kirjina ya sake nauyi akan wanda ya yi dazu da naga Baban Tsakiya yana cin da'di a kofarsu amma mu muna cin abinci irin na yan fursuna, kuma suna da halin tallafa wa. Amma sun runtse idonsu. Haka Baban Marina ya dinga bawa Dada da sauran y'ay'anta ha'kurin katobarar da na yi tamkar dai shi din ba uwarsa ba ce. Sai lokacin hawaye mai ciwo ya goce mini, ina jin tsanar mutanan da a baki Baffanina ne. Maganar gaskiya kuma na fi jin ciwon Baban kasuwa. Haka suka fice suna kumfar bakin na fitine su, na fitini y'ay'ensu, tunda ba'a sati ba a doku da ni ba a cikin gidan. Rainin da aka yi mana ne ya sanya dukkan mutanan gidan suke ganin zasu mayar da mu gidadawa, shiyasa ni kuma na lashi takobin duk wanda ya nemi ta'ba ni, ko taba wani cikin yan k'ofarmu la shakka ni ya ta'ba domin zan siyi fa'dan ne ya dawo kaina, duk yadda nake yar shafal amma Ubangiji ya hore mini wani irin karfi tamkar shari'a, ko dan da dukkan zuciyata nake yin fa'dan ne oho. Yadda nake tare wa kannena fa'da da muke daki d'aya haka nake tarewa na yaran Inna amaryar Babanmu babu banbanci. Hatta Nazira da take yayata ni nake tare mata fa'da domin duk wanda ya fa'da mata maganar banza zan yi ruwa na yi tsaki na shiga na dinga yarfa bak'ar magana har sai abin ya juye kaina. Duk yadda nake jin haushin Mama bai shafi son da nake yiwa Nazira ba. Domin yar-uwata ce da uba ya ha'damu, idan da abin da na tsana ban kuma yarda da shi ba shine yan'ubanci. Ina matu'kar takaicin yadda wai gidanku daya da mutum, cikinku daya, gadonku daya amma babu yarda da amana a tsakaninku. Duk wani alherinka baka son dan-uba ya ji, zaka iya fa'dawa bare matsalarka amma ban da dan-uwanka da uba daya ya hada ku. Kuma mafi yawa iyaye mata ne suke bari yaransu su shiga cikin rikicin da ba nasu ba. Da ace Nazira tana biye hudubar Mama da tuni ta gurbata mana zumunci da soyayyarmu, mun koma muna adawa da junanmu. Wai uwa ce zaka ji tana zayyane wa y'ay'anta laifin kishiyarta, ko kuma laifin y'a ko d'an da ba nata ba. Da ace iyaye mata zasu dinga ha'diye rikicin kishi a tsakaninsu, suna boye rashin jituwarsu a gaban yaransu, sannan idan matsala ta faru suna barinta a tsakaninsu da an samu sassauci wajen yan ubancin da ake yi a yau. Idan d'an kishiya ya yi miki laifi ko ta yi miki, daure ki ha'diye ba sai kin baza wa yaranki da basu sani ba, gudun haddasa gabar da baki san iyakacinta ba. Ko wanne d'a a duniya gaibu ne, ba wanda yasan me gobe zata zo da shi, ba lallai d'an da kika haifa ya samu daukaka ba, wata'kila sai d'an miji ya samu daukaka fiye da yaranki, adalcin ki ne zai sa Ubangiji ya sarrafa zuciyarsa ya ji k'anki, haka nan ke ma babu jin kunya ko nauyin kin yi abubuwa a baya marasa da'di. Na sani mutanan yau bamu cika gode wa da yaba kokarin abokan zamanmu ba, muhimmi dai mu yi adalci a tsakanin zaman kishi da yaranmu, ko ba a shiri ya zama akwai sassauci da ha'diye bacin rai, shi adalci yana haifar da farin-ciki da yalwar arziki da hadin kai a cikin gida. Addinin musulunci cewa ya yi ko wanne musulmi dan-uwan musulmi ne, bare kuma wanda jini mai k'arfi ya ratsa a tsakaninku. Daga shakiki sai li-Abbi a duniyar musulunci da zumunci amma mutanan yau mun dauki wata irin *Bak'ar Ta'ada* ta mayar da dan-uba abokin gaba kuma makiyi. Da kaina na jinjina wa kaina da duk wacce bata da wannan mummunar manufar a ranta. Madallah da mutanan da suka yarda Ubangiji ne yake zaba mana mutanan da zasu zama iyayenmu da yan'uwanmu. Alhamdulillah, Allah ka bamu ha'kuri