← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 146

Sashe 17

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

na zo sannan ya mayar ya shigo ya kalli yadda na tumbatsa ya ce "Anya Asiya ba dusa kike ci ba kuwa? Ace har kin doshi hamsin? Gaskiya ina taya Baba ba'kin cikin asarar ku'din taran da ya wanzu yana baki". Cikin rawar murya na ce "Bulkachuwa Yadda ka tozarta ni a gaban wanda suke son na tozarta in sha Allah sai an tozarta budurwarka fiye da yadda ka mini, da ikon Ubangiji sai ka ha'du da sharrin mace, sai ka muzanta a idon duniya". Ya make kafa'da alamun ko a jikinsa tare da cewa "Yabi yanga mai kwakwalwar kifi". Ganin hakan ya sanya Maijidda ta mike tana jin karfi yana shigar ta tunda ta ji abin da take son ji. Ta mini gwalo tare da cewa "Na ji dai, dama nasan baki tsinana komai ba". Ta shige wajen Dada da saurin ta. Yayin da ragowar suke fa'din "Yi ha'kuri Yabi, ai kin nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane. Ba gashi ta tsere ba". Na jijjiga kai na ce "Ai dan ta ga Bulkachuwa ya tsaya mata ne". Yayin da shi kuma ya ce "Ba dole na tsaya mata ba, tunda ke din karfinki na aljanu ne, na tabbatar ba ke ka'dai kike fa'da ba, kina samun tallafin aljani mai kilabo da gwaigwai". Duk wajen aka fashe da dariya illah ni dana sake fusata na daga murya "Ina ce wa "Allah ka dora wa matar Bulkachuwa aljanun da zata dinga daga shi sama tana danfara shi da k'asa". Ya wuce yana fa'din "Duk bala'in aljani ba zai shigo mini gida ba, domin hafiza zan aura mai hazakar gaske a ilimin boko da na addini. Safiya da marairaice ta yi ta tofe mini gidan da azkhar, idan kin ga aljanu sun yi tasiri, sai a gidan wanda basa mayar da kai a wajen bautar Allah irin ki". Na wuce shi zuwa shashin Dada. Na tarar da Maijidda tana ta kuka yayin da Dada take sakacen hakori da tsinken zabori hankalinta a kwance. Na bu'de baki na ce "Dada sannu da gida, mun dawo". Ta amsa ba alamun damuwa a tare da ita. Na juya na tafi sai na ji kukan Maijidda ya karu tana cewa "Kin bar ta tafi baki bi mini kadina ba?" Na yi tsam dan na jiyo amsar Dada. Kamar ba zata tanka ba sai kuma na ji tana ce wa "Na k'i na yi mata maganar. Yar kankanuwa a gabanki, sannan kin bata kwanaki arba'in cif amma kin kasa kwatar kanki a hannunta sannan dan asaranci ki ce na tare miki fa'da? Ai kinsan fa'dan ta baya mutuwa akan me zaki tsokano abin da yafi karfinki?" Maijidda da bata yi zaton haka Dada zata ce ba, domin mun saba yin fa'da da yan k'ofarsu ta basu gaskiya ko da kuwa ni ce mai gaskiya. Dada ta ja tsaki ta ce "Sadda nake cikin shekarun kuruciyata haka nake nima duk girman mace bata bani tsoro, haka nan duk wanda ya mini kan ice sai na yi masa na kara. Sai yanzu na fahimci wannan tijarar ta Yabi sawuna ta biyo domin komin sharrin mai sharri ba zai ce ubanta mafadaci ba ne ko kuma uwarta. Dukkan iyayenta sanyin kalau ne, dan kuwa inta sune kiyama ba zata tsaya ba." Kukan Maijidda ya tsananta ta dinga yi tana ce wa "Ai dai kinsan bata isa ta kai ni k'asa ba, dunbular mini kirji ta yi ta yakushe ni a wajen." Salati Dada ta dauka tana cewa "Ikon Rabbani, tarihi na maimaita kansa ni Fadimatu. Wallahi Maijidda sadda aka mini auren fari ina kankanuwa aka kai ni babban gida, matar wan miji ta saka ni a gaba, duka, kyara zagi. Har na fara girma a cikin fargabar wannan baiwar Allah na ke. Ai kuwa da tura ta kai bango na fara rama abin da take yi mini. Har muka kai jallin da muka fara dokuwa, sai dai kashi take bani da yake ta fini sosai, ai sai kawai nake fakar ido idan muna damben ina mintsinin nonuwanta ko na na cije su. Shi kenan na yi maganin gallazawarta, ta shiga kiyayata. Yau ga Magajiyata na samu a haulata". Ta fa'da tana tafa hannu tana sake jan salati. Na wuce ina son yin dariya amma ba'kin cikin Bulkachuwa ya dabaibaye ni. Na wuce shashinmu ina jaddada wa kaina ko a gaban Baban kasuwa ne Maijidda ta tsokano ni sai mun sake cire raini, bare Dada. Bamu jima da dawowa ba sai ga mahaifiyar Maijidda da kanta ta kawo togaciya. Fadi take "Tura ta kai bango kullum Yabi sai ta yi mini sanadin bacin rai jiyan nan ma sai da ta dakar mini Kaltume akan sun samu sabani da Ismail, akan me zata tisa mini yara a gaba irin haka?" Ha'kuri kawai Gwaggo take ta bata, Inna da ta rage tsananta gaba da ni a dalilin ina yiwa yaranta hidima tamkar yan dakinmu, sannan ba mai tab'asu a waje matu'kar ina wajen sai hakan yayi tasiri, ta rage daukar zugar Mama. Dan haka sai ta ce "Ban da ke ma Abu da shiga shirgin yara ina ce Maijidda ta girmi Yabi ne? Sannan idan kinsa ha'kuri anjima ka'dan zaki iya ganinsu tare". Nan da na ta harzuka ta ce "To Yabi ni kaina ai sai ta dake ni tunda fa'dan yan-iska take yi, ban da dai ta riga ta rik'a ta yaya zata dinga dumbular kirjin y'anmata, tabbas dayan biyu ne, ko dai niyyar kisa take yi ko kuma ta shiga sahun masu *Bak'ar Ta'adar* neman mata."
Chapter 17 · 0% Book details