← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 146

Sashe 90

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?*
*INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.*
*KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME*
*KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU*
*TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*.
*MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.*
*IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI*
*07039269802*

Ya daburce ya ce "Wallahi babu kowa Yabi".
Fa'din Yabi da rudun da ya shiga sai yasa na kasa gasgata shi amma kuma na danne na ha'diye saboda babu kyau zargi.
Duk yadda na so na bar maganar amma a zuciyata sai wasi-wasi nake yi. Na kasa samun nutsuwa. Hakan ya fara shafar walwalata. Ban sauya masa ba, ba kuma na bijire masa amma kuma babu shiriritar da nake yi masa a baya.
Rannan na ce masa ina son na je gida na yini. Da rawar baki ya ce "To, yaushe zaki je?"
Domin ya takura da rashin walwalata.
Na ce "Duk ranar da ka ce".
Ya ce "To gobe sai na kai ki"
Haka kuwa da kansa ya kai ni, muka fara isa k'ofar Dada muka gaisa. Tana ta barkwancinta da karatunta. Ban wani jima ba na tashi na nufi k'ofarmu."
Ya shigo suka gaisa ya ce mini zai tafi da yaushe zai zo ya d'auke ni?
Na ce "ko yaushe ma".
A k'ok"arinsa na son ya kyautata mini sai ya ce "Tom idan an idar da Isha zan zo".
Na ce "Allah ya kai mu".
Ya tafi. Na yini cikin iyayena cikin nutsuwa da walwala.
Da yamma lis Gwaggo da Inna zasu je duba yar kanwar Mama da ta haihu kusa da unguwarmu ne.
Dan haka Baban Marina ya ce "Asiya sai ku je tare ki rakasu idan kin dawo sai ki shige gidanki".
Na amsa da ce wa "To Babanmu, domin idam Gwaggo ta fita ba jin da'din zaman zan yi a dakin ni ka'dai ba, tunda Ikilima ta tafi Islamiya, shima kuma Baban fita zai yi. Mama kuwa babu wata ma'amala mai yawa a tsakaninmu.
Dan haka muka tafi tare. Da muka dawo na yi lungun da zai sada ni da gidana, su kuwa suka mik'e suka koma nasu gidan.
Haka kawai nake jin nauyin jiki na saukar mini. Wani irin b'acin rai ya ziyar ce ni da na karyo kwanar da na fara hangen gidanmu. Haka nake tafe ina ta jin fargaba. Ina kuma ayyana abubuwa marasa da'di a zuciyata.
Nan da nan na fara ta'awizi ina kore shaid'anin da yake son yin wasan kura da zuciyata. Har cikin zuciyata ina son Tijjani, ina son na rayu da shi. Domin a zaman da muka yi na shekara daya da kusan rabi na tabbatar yana da kyawawan dabi'u. Na farko shi mutum ne mai mutunta sallar farillah. Sannan mai yawan tsayuwar dare ne na shaida hakan. Domin duk lokacin da zai shafe yana tiritiri da ni da daddare, to da zarar k'arfe uku ta yi kuma zai tashi ya yi wanka. Ya yi ta yin munajati da Ubangijinsa, wani lokacin ya matsa mini na tashi, wani zubin kuma ya k'yale ni na yi barcina. Sau tari kuma idan ban tashi ba, da asuba idan ya tashe ni sai ya ce "Tashi ki yi sallar farillah akan lokaci, na raba dare ina roka miki alherin duniya da lahira my little".
Bayan hakan na karance shi yana da matu'kar son ya kiyaye ka'idojin da shari'a ta d'ora masa mussaman na ri'ke gida da kula da tarbiyata. Sannan ba shi da mugunta ko ka'dan har yau din nan Tijjani bai ta'ba saka mini ido akan ku'dina ba. Asalima kullum cikin k'ara k'auwame kansa yake yi da abin hannuna.
Sannan ya iya Soyayyar da duk taurin zuciyar mace sai ya dargaza ta. Ga kuma girmama iyaye, yana mutuntata manya kwarai da gaske. Wadannan dabi'un da ya siffantu da su ya sanya nake hakuri da inda yake kuskure mini, hakan ne kuma dalilin da yasa na k'i yarda na k'arfafa wa kaina zargin ko ya koma Bak'ar Ta'adar sa ta baya.
Na shiga zauren na ga kofar tamu a rufe ruf. Na fara tunanin ai ban fito da mukulli ba, tunda mun yi shi zai zo ya dauke ni.
Na zaro waya da nufin na k'ira shi ya zo ya bu'de mini, sannan na wuce k'ofar Maman Safiyanu na jira shi. Sai na jingina da k'yauren k'ofar ga mamakina sai na ga ta bud'u.
Na tura a hankali na ga sakata a ture tabbacin an saka bata shiga ba ne.
Na shigo a hankali. Amma sai na ci birki na tsaya cikin tsananin tu'ajjibi da mastanancin mamaki mai yawa.
Jikina ya d'auki b'ari, zuciyata ta yi nauyi ainun. Amma idona ya bushe k'amas.
Na saka hannuna na murtsike idanuwana da tunanin gizo yake yi mini, tare da fatan ace sak'e sak'en zuciyata ne da wasi-wasi irin na shaid'an.
Amma ina zahiri nake ganinsu. Tijjani zaune akan baranda yayin da Rafi'a take kan cinyoyinsa da manyan mazaunanta. Ta kwanta luf a kirjinsa, shi kuma idonsa na kan k'irjinta yana kallonsu. A zahiri iya abin da na gani ke nan amma zuciyata sai ta shiga wassafo mini cewar yanzu ma suka sanya tufafinsu.
Na ki'dima ainun, amma na kasa yin kwakkwaran motsi, na tsaya cak ina kallonsu tamkar mutum mutumi
K'arar faduwar wayata ne ya ankarar da shi.
Ya d'ago da fuskarsa ai yana ganina ya yi wani irin zabura ya wancakalar da ita, ta hantsilo ta fa'do kan guiwowinta.
A matu'kar rude ya k'araso gare ni.
Ya rasa mai zai ce, sai kawai ya zube a gabana guiwa bibbiyu. Ya ru'ko hannuna na kalle shi na ce "Tijjani gizo idona yake yi, ko mafarki nake yi?".
A ki'dime ya ce "Zan so a ce mafarkin kike yi Asiya".
Daidai lokacin Rafi'a ta zo ta shige sum sum tamkar k'wai ya fashe mata a ciki.
Na dinga jin tukukin ba'kin ciki da tashin hankali. Amma kuma idona a soye duk yadda nake son hawaye ya zubo mini abu ya ci tura.
Na sunkuya na d'auki waya ta na k'wace hannuna na yi d'akina ina jin jiri na katantanwa da ni.
Kai tsaye na hau cire rigar cikina domin zafin da nake ji a zuciyata har jikina yake kutso wa. Zufa sai yanko mini take yi.
Na cire komai na d'aura zani. Na zauna amma ban daina jin zafin jiki ba.
Na fita har lokacin yana durk'ushe a inda na bar shi.
Na dauki botiki na nufi rijiya. Da azama ya tare ni, ya ce " Bana hana ki jan ruwa da kan ki ba?".
Ban ce komai ba na matsa gefe ya janyo mini ruwan. Ya kinkima ya kai mini band'akin.
Na shiga na yi wanka. Amma dana fito ina goge jikina da tawul, zufar na sake keto mini.
Na dauki rigar barci marar nauyi na saka, bayan na saka gajeran wando ta ciki. Na d'aure kaina da dan kwali mai taushi.
Kicin na fa'da na hau girki, ina yi ina hailala. Gaba'daya jina nake yi tamkar ba ni ba. Na yi matu'kar kad'uwa da abin da na ga ni a cikin gidan aurena.
Ban san falalar kuka ba sai a yau, domin gaba'daya hawayen ya k'i zuba.
Shi kuma ya takure, a gefe tamkar ka ce k'yat ya zura a guje. Cikin lokaci k'alilan nadama mai tsananin gaske ta bayyana a dukkan jikinsa. Ya kasa sukuni, da alamu kunya ce ta hana shi sukuni. Tunda ni dai ban bu'de baki na ce masa komai ba.

*Annur food Delicious*
*Da k'arfin zuciya da guiwa na ke muku shunen inda zaku samu kayan da na zano a kasa cikin saukakkan farashi.*
*Shaida nake yiwa kayan annur domin dadinsu da ingancinsu ya kai kurewa*
*HANZARTA ki nemi kayansu dan ki gasgata batuna*
*Garin kunun tsamiya garin danwake, garin borkono, yajin daddawa, man shanu, nikekkakiyar gyada ta kunu da ta miya*
*08039183880*

✍️
*Dandano*
*DAGA Littafin BAK'AR TA'ADA*
*NA SURAYYA DEE*
*MARUBUCIYAR HALIN YAU DA SABO DA KAZA*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GICSrs9TfxG1Q6FUXiu1Qg

*Ina tallata muku make up artist din Guduyo*
*Aisha Lame mai kayan kwalliyar yan gayu*.
*Jakadiyar oriflame, duk wani nauyin kayan oriflame tana kawo su cikin farashi mai sau'ki*.
*Ba iya kayan kwalliya masu daraja ba, ita din GWANAR sarrafa pop corn ce(gugguru), ni shaida ce ta hakika*.
*Sannan tana da spices kasaitatu. Masu mayar da girki ya zama na alfarma*
*07036662633*.

*INA SANAR MUKU ZAMU BUGA LITTAFIN KANA NAKA ZUWA HARD COPY*.
*MASU BU'KATAR MALLAKAR NASU SU TUNTU'BE NI, KO SU TUNTU'BI MARUBUCIYA JANAFTY*.

*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM*.
Chapter 90 · 0% Book details