Sashe 58
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*KUN TUNA MAI GYARAN GUDUYO?* *INA NUFIN FASEELAT BABBAR DILA TA G.H.T.* *KO WANNE NAU'IN KAYAN GHT TANA SIYAR DA SU AKAN FARASHI MAI RANGWAME* *KAWAI KU TUNTUBE TA A WANNAN LAMBAR DAN GANIN JERIN KAYAN DA TAKE DA SU* *TUN DAGA KAN SUPPLEMENT, SABULAI DA LIPTON*. *MASANIYA CE AKAN KAMFANIN DOMIN TA SAMU KARRAMA WA DAGA KAMFANIN A BANA, HANZARTA KI TUNTUBETA DAN SIYA DAI DAI KO SARI.* *IDAN KUWA KINA SON YIN RIGISTA DAN FARA KASUWANCIN KAWAI KI TUNTUBETA DAN KUWA DA KYAKKWAR ZUCIYA ZATA MU'AMALANCE KI* *07039269802* Da zafin rai na ce "Kai ne ka fitine ni, irin fitinar da ko maki'yata bana fatan a fitine ta irin haka." Na sake rushe wa da kuka tamkar an fa'da mini mutuwar mahaifina. Ya ki'dima ya ce "Me na yi miki? Fa'da mini dan Allah". Takaicinsa ya nemi sark'e mini numfashi. Na kasa magana illah hawaye da yake zuba tamkar famfo. Tsawon lokaci ya yi shiru yana sauraron shesshekar kukana. A sanyaye ya mike, murya babu amo ya ce "ki k'arantawa kan ki k'iyayya ta Asiya! Bai kamata ki kuntata wa zuciyoyinmu irin haka ba. Ki cigaba da addu'a da sannu komai zai wuce." Har ya kai bakin kofa ya ce "kin ci abinci kuwa?" Cikin fishi na ce "Bazan sake cin abinci ba, sai yunwa ta mayar da ni gawa In sha Allah! Ya girgiza kai ya ce "Babu laifi". Maimakon ya yi kwanciyarsa sai na ji yana ta buruntu a kicin. Shude war mintina talatin sai ga shi da bowl yana fa'din "Ki dubi Allah da ma'aiki ki tashi ki ci, ba dan ni Tijjani ba. Dan Allah". Na sassauta kukan domin Gwaggo ta cusa mana yin uzziri matu'kar aka ce saboda Allah. Ya zauna kusa da ni sosai ya miko mini. Cikin rarrashi ya ce "Allah ka yarda da Asiya, ka sata cikin bayin da ka yarda da su". Jikina ya yi sanyi. Na kar'ba, na fara cin indomien da ta yi da'di tamkar ba girkin namiji ba. Ni da nake fa'din bazan ci ba, sai gashi na share ta tas. Da hanzari ya karbi kwanon ya mik'o mini ruwan hannunsa mai rangwamen sanyi. Take na nemi jirin da nake ji na rasa. Na yi gyatsa. Sai kawai na gayra na kwanta. A hankali ya ce "da kin daure kin dan yi tattaki kafin ki kwanta". Ban kula shi ba, a haka barci ya sure ni. Bansan sadda ya tafi nasa makwancin ba. Washagari mirsisi na k'i yin abin kari. Bai matsa mini ba. Ya siyo kosai da kunu ya kawo mini. Kwanaki suka yi ta shud'e wa, har na samu sati a gidan aurena. Har lokacin kuma ban yarda na sake d'ora tukunya ba. Shi kuma ko ya yi fishi, ba ya jure ganina ban ci abinci ba. Kan dole sai ya nemo mini. Ranar da na cika kwanaki goma ya fara gazawa da al'amarina. Ga shi ku'din hannunsa sun tasar ma k'are wa. Ya zaunar da ni ya sassauta murya ya ce "Asiya yanzu a ce abincin da zamu ci ba zaki dinga girka wa ba? Kina kallon kayan miyan can da yawa sun lalace. Ya kike so na dinga yi ne? Idan na fita tun safe na dinga bulayin abin da zan yi na samu taro da sisi dan asirinmu ya rufu amma bazan dawo na tarar da kwanciyar hankali ba? Yini nake cikin zullumi da fargabar halin da kike ciki, da abin da zan dawo na tarar. Me yasa bani da wata alfarma ne a wajen ki?" Na zum'bura baki ainun. Tsawon lokaci ban ce komai ba. Ya numfasa ya ce "Pls Asiya na roke ki, mu zauna lafiya ki kwantar da hankalinki dan Allah". Tsawon lokaci ya dauka yana rarrashi, akan na ce masa na yarda zan dinga yin girki. Amma ban yarda na ce masa komai ba. Ya harzuka ya ce "Allah kai ne shaida ta." Ya tashi ya bar ni. A hakan na cike sati biyu. A wannan lokacin kuma aka fara zuwa mini lalle da kitso. Na rasa a inda zamu dinga zama. Domin tsakr gidan babu bishiya kuma babu rumfa. Baranda kuma idan rana ta bude babu dadin zama. Dakin da kayansa suke nan ne yafi dace wa ya zama dakin da zan dinga yin sana'a ta. Dan haka na shiga na tattara masa kayansa gefe d'aya, na kunna turaren wuta a dalilin kayansa masu datti na zube a k'asan. Na ha'da na d'aure su waje guda. Yini na yi ina lalle. Sai yamma ya dawo gidan da ledar abincin da ya siyo mini. Kallonsa kawai na yi, na gane ya ji haushin cika masa daki da na yi da mata. Ya ajiye abincin ya juya. Sai dare ya dawo lokacin babu kowa. Tuni kuma na share dakin na kintsa shi tamkar ba'a ciki muka yi ba. Fuskarsa a daure ya tarar da ni ya ce "Asiya Toro kada ki kuma shigar mini daki da nufin yin kitso ko lalle". Na cuna baki na ce "Idan na kuma fa?" Ya girgiza kai ya ce "To ki kuma din". Washagari da hantsi sai ga Rafi'a ta shigo mini. Da walwala na karbe ta. Ta dinga fa'din "Amarya ashe haka kika iya kunshi da lalle?" Da murmushi na ce "Ina koya dai, idan kina so sai ki zo na yi miki". Da babbar muryarta ta ce "Ai kuwa na gode sosai". Tijjani na fita na shiga d'akin muka fara yin kunshin. Kafin na gama mata har mutum ukun sun zo. Da azahar ya dawo gidan, ko d'ar ban ji ba, balle na yi fargabar na karya dokar sa. Ga mamakina bai shigo ba, bare ya dauki matakin da nake son ya dauka. Amma sai na ji ya bu'de murya yana kiran Rafi'a daga falon. Ita kuma ta shiga da saurin ta. Wani irin abu ya d'an mintsini zuciyata. Amma na sanya jarumta na boye abin dana ji din. Ina dan jiyo maganganunsu, har na fahimci sun saba dama tunda yayanta abokinsa ne. Bansan me ya ce mata ba, na ga ta fito ta shiga kicin. Abin ya sake buguna. Ban ankara ba na ji ta fara jajjage. Wata babbar mace da na gama sanya wa lallen. Ta kalle ni babu alamun wargi ta ce "Je ki karbi hidimar mijinki a hannun waccar yarinyar tun baki janyo wa kanki sanadin bacin rai ba". Na yi yak'e na ce "Ai tare muke da ita, k'anwarsa ce." Ta saki gauron numfashi ta ce "Tau ya yi babu laifi, na dauka babu sidi bare sadada a tsananinku. Amma dai kada ki fara saka wani lallen, tashi ki je ki marabce shi, ki bashi ruwa sai ki dawo. Ki kula da auren ki da kyau kin ji". Ganin ta haife ni, dan na tabbatar tana da yaran da suka zarta ni. Hakan ya sanya na tashi na yi tamkar na je wajensa, nan kuwa dakina na shiga na zauna bakin gado. Tamkar mai jirana sai gashi ya shigo mini. Ya kaurara murya ya ce "Asiya Toro ba ki ji kashedin da na yi miki ba akan shigar mini daki da mata ba ko?" Na murguda baki na ce "Ban ji ba Tijjani! Ba kuma zan ji ba". Ya ce "Shike nan" Na riga shi barin dakin. Ina kallon yadda ta shirya masa abincin a tray, cikin flask mafi kyau a kicin din. Plate din na tangaran ta saka. Maimakon da ta kai ta fito, sai ta yi zamanta suna hirarsu. A daddafe na kammala lallen. Dan da wata ta zo ma ha'kuri na bata, na ce ina da ayyuka mai yawa ga kuma maigidan na nan. Wani irin makakin ba'kin ciki nake ji har cikin mak'oshina. Duk da bana son Tijjani amma na ji zafin kiran Rafi'a da ya yi. Mussaman umarnin yi masa girki da ya bata. Ina da eani irin kishi tun ina karama ta. Har ta kai Gwaggo kullum cikin yi mini addu'ar samun sassauci take yi. K'asan zuciyata kuma ban yarda kishinsa nake yi ba. Tunda ba wai ina sonsa ba ne. Kawai wula'kanta ni da ya yi ne ya mini ciwo.🤣 Sai da ya gama ta fito da kwanukan abincin. Da murmushi ta ce mini "Na gode sosai Amarya. Sai na sake shigo wa". Ga mamakina na kasa yi mata ko da yak'e ne. Murya a dakushe na ce "Madallah". Da daddare ina falo, ina kallo ya dawo. Sai da ya yi wanka, sannan ya shigo ya zauna. Cikin nutsuwa sosai ya ce "Asiya na ce kada ki kuma shiga mini daki da nufin yin lalle ko kitso amma baki ji ba ko?" Yana rufe baki na ce "Tijjani ban ji ba, ba kuma zan ji ba, ka yi abin da zaka yi marar tsoron Allah kawai". Ya yi mini k'uri ya ce "Me na yi miki na rashin tsoron Allah? Ni ban fa'di hakan akan ki ba, sai ke zaki fa'da mini hakan?" Babu fargaba na ce "Ina da tabbacin bana aikata kaba'ira, kai kuwa kaba'irori nawa kake aikata wa? Tsabar shaharar da ka yi a BAKAKEN TA'ADODI har gidan auren ka ma bai tsira da sharholiyar ka ba". Ransa ya baci. Amma da ya fahimci kishin Rafi'a ne ya k'ume ta, sai farin-ciki ya maye gurbin bakaken kalamanta. Da alamun da Rafi'a zai yi amfani ya dinga rama wula'kanta shi da take yi. Ya girgiza kai ya ce "Sharri dai dan aike ne. Mussaman wanda aka ginasu akan zato da jita jita." A kufule ainun na ce "Ba batun sharri a lamarinka. Iya karshen cuta an yi mini. Amma na barwa Allah al'amurana" Na fa'da hawaye na subuce mini". Ya kasa cevwa komai. Tsawon lokaci mun yi jigum jigum! Sai hawaye da suke tsere a kan fuskata. Babu kuzari ya taso ya dawo kusa da ni sosai ya sassauta murya ya ce "Kinsan bana son kukan ki Asiya! Na tari numfashin sa a zafafe na ce "A gidan uban waye baka son kukan nawa? Makaryaci, mugu, bunsuru..! Ai ban karasa ba, na ji wani irin gigitaccen mari a fuskata. Wanda ya sanya na zunduma ihu a matu'kar ki'dime. Cikin fishi mai yawa ya ce "Kin ci uwar karya kin kwana da yunwa Asiya. Kin yi ka'dan ki zagi ubana, ki wanye lafiya. Ashe togaciyar da na yi