Sashe 40
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyau, komai sai son barka, domin komin kushen mai kushe na zai kushe kayan ba. Amma gare ta babu wata murna. Dan ko dazun nan sai da na ga tana wanke wa Bulkachuwa kayansa. Ba kuma sata ya yi ba. Ajiye wa ya yi a inda ake wankin ita kuma ta jika ta wanke tare da na Dada. Kwanaki biyu a tsakani aka kawo lefena. Sun yi kokari kwarai da gaske domin duk ha'duwar kayan Nasiba, nawa sun zarta nata da ka'dan. Amma abin mamaki ahalin gidanmu basu zuzuta kayana kamar yadda aka yi ta kuranta na Nasiba ba. A lokacin kuma Dada da y'ay'anta kullum sai sun zauna, Babanmu ne kawai ba'a sa shi a cikin zaman sai Baba ta Bulkachuwa ita kuwa ba a garin take ba. Saura kwanaki goma sha biyar auren Dada ta zaunar da Babanmu. Bamu san me ta ce masa ba, amma dai mun ga ya shiga cikin rashin sukuni har washagari. Ashe ce wa ta yi auren Yabi da Nuru ba zai yiwu ba matu'kar tana da iko akansa. Ya nemi sanin ba'asi ta ce ya saurare ta zuwa jibi. Bai sanar da kowa ba, har sai ranar da ta ambata. Dukkansu suna zaune a dakinta. Cikin rashin damuwar komai ta ce "Alhaji! Yanzu ya kyautu ace an bar mai sunan manya yana gararanbar neman aure ana hana shi, alhalin akwai yara a gabanku? Kullum da abin nake kwana, nake tashi, tare da zullumin kar'bar da zaka yiwa al'amarin. Sai kuma na tuna ikon da shari'a ta bawa uwa ". A sanyaye ya ce "Hakane". To maganar auren Yabi da wannan ba'kin yaron ba shirayayya ba ce daga Allah. Domin mai sunan manya za'a bawa ita." Wani irin zullumi ya shige shi. Murya a raunane ya ce "Dada ina ce Nasiba yake so?" Nan da nan ta ce "Nasiba ai ubanta ne ya yi iko a kanta ya ce dan k'aninsa zai bawa." Ya ce "Dada ina ro'kon arziki a ba shi wata cikin yaran Badamasi ko na Iliya tunda an riga an karbi komai na aurent a, akwai nauyi mai yawa a tsakaninmu da uban yaron nan ke ma shaida ce". Ta kai kallon ta ga Baban Tsakiya ta ga ya murtuke fuska. Nan da nan ta ce "Duk abin da yake tsakaninku da Tanimu ya kai da yar'uwar ka ne?" Da sauri ya ce "Ba kai ba Dada! Sai dai haramun ne neman aure a cikin aure." Baban kasuwa ya ce " Ai ba bisa son zuciya ba ne, biyayya ka yi, Allah kuma zai karrramaka tunda ka bi uwa. Idan ya so sai a bawa Nura Kaltume ba shike nan ba." Baban Marina ya kalli kaninsa da wani irin duba. Yana mamakin son zuciya irin tasa. Ya dauki y'arsa ya bawa Jabir yasan kuma saurayin Yabi ne. Yanzu kuma a kan idonsa yake fadin zai sake bawa Nura y'arsa tunda yasan akwai mamora a tare da yaron. A hankali ya ce "To ko zaka lamince na bawa Tijjani Kaltumen kawai?" Nan da nan ya ce "Ina! Ai ba ita Dada ta umarta ba, so ka ke na shiga fishin uwa?" "Shike nan Allah ya amsa addu'ar ka, Allah ya sanya albarka a cikin wannan ha'din , ya amintar da lamarin. Na bawa Tijjani Yabi, da dukkan zuciyata"! Baban Marina ya fa'da cikin wani irin yanayi mai ban tausayi. Dada ta ce "Allah ya yi albarka". Har ya yunkura zai tashi sai ya ce "Zan bawa shi Nuran kanwarta. Komai da suka kawo da sunan Yabi ya koma kan Ubaida". Ya fita yana ha'da hanya. A zaure suka yi kicibus da Bulkachuwa. Baban Marina ya kalle shi cikin wani irin yanayi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Dubi gashin kanka, kamar ba bahaushe ba, ka dubi wando jikinka, tamkar babu iyayenka a gidan, yaushe zaka zama cikakken mai kamala ne?" Ya sunkuyar da kai ya ce "Za'a gyara Baba" Domin kuwa da dukkan zuciyarsa yake ganin kimar Baban Marina fiye da su Baban Tsakiya. A dakin Dada kuwa Baban Kasuwa ya dinga fa'din"Dada ai da kin ce a ba shi Kaltume kawai, ina ce ta fi Ubaidan a haife?" A dan tsorace ta ce "Ga ni na yi zan takura da yawa, sannan dole hankalin mutane zai dawo kanmu". Ba shakka ya ce "To ya dawo mana! Idan ka daka ta mutane ai ko sallah ba zaka yi ba, domin kana yi suna kallon ka, ba dan su gyara maka ba, sai dan su gano na'kasunka su yi zundenka Bare kuma akan wani al'amarin duniya da bai zame komai a juya maka manufarka kyakkawa zuwa mummuna ba." A sanyaye Dada ta ce "Hakane". Suka tashi ba tare da sun so a bawa Nura Ubaida ba. Washagari sassafe Baban Marina ya zaunar da matansa ya shaida musu juyin da aka sake yi, da kuma hukuncin da ya yanke akan yin madadi da Ubaida. Daga Inna har Gwaggo abin bai musu da'di ba. Mussaman Gwaggo da take gani ita ce zata fi shiga cikin tashin hankali, domin matu'kar Yabi bata samu dacen aure ba, to komai ma zai kwace mata ne. Ga Ummi ita ma fama take a nata gidan. Shike nan a hakan zasu kare ita da y'ay'anta?. Shirun da suka yi gaba'daya shi ya sake sanyaya masa guiwa. Ya ce "Kun yi mini zuru?" Mama cikin walwala ta ce "To me zasu ce Alhaji? Y'ay'anka ne fa ka yi iko da su, sannan ba shawara ka nema ba, tunda an riga da an zartar to wace ce zata yi inkarin hukuncin Dada matu'kar tana son ka rabauta?". Maganar Mama ita ta sanya wa Gwaggo k'warin guiwa domin ta sani so take ta ganta cikin rashin sukuni da tashin hankali. Nan da nan ta ha'diye damuwarta, ta murmusa tare da ce wa"Allah ya sanya alheri da albarka, ina fatan Allah ya sa ace gara da aka yi". Wata irin nutsuwa ta zo wa Baba domin dama uwar Yabi yake ji. Ya sani borin da Yabi zata yi ba zai yi tasiri ba tunda an yi sa'a ita din mai jin maganarsu ce mai kuma kishin kada su kunyata ne. Ya dinga yaba mata tare da sanya mata albarka. Ya juya ga amaryarsa Inna uwar Ubaida. Ya ce "Ke kuma fa?" Murya babu amo ta ce ", Allah ya sanya albarka". Ya sake numfasa wa tare da cewa"Yadda kuka kwantar mini da hankali a lokacin da aka jefa ni cikin matsanancin hali, ina rokon Ubangiji ya kewaye y'ay'anku da farin ciki da kwanciyar hankali a wannan aure. Allah ya sanya alheri mai yawa ya biyo baya. Allah ina rokon a azurtasu ta inda muka zata da ta inda bamu zata ba". Suka amsa da ameen cikin juriya. Amma Mama bata ce uffan ba. Ha'din kai da ya samu daga wajen matansa ya taimaka kwarai wajen kwantar da hankalinsa. Har dare muna namu yi, ban samu labarin komai ba. Sai dai na lura da rud'anin da Gwaggo take ciki, gaba'daya ta zama wata iri, ta yi zuruzuru. Na tambaye ta ta ce mini gudawa take yi. Take na gasgata na tura Anas ya siyo mata filagil. Da daddare bayan dare ya d'an fara tura wa Baba ya kiramu ni da Ubaida. Na cika da mamakin ha'damu da ya yi. Muna durkushe a gabansa, shi kuma yana kan kujerar ba'kin karfe irin ta da, da take dakinsa. Ya kalle ni ya ce "ku zauna sosai. Ina bu'katar hankalinku da nutsuwarku". "Muka nutsu kuwa, amma gaba'daya zuciyata ta shiga rud'ani sosai. "Shi da kansa ya jima bai iya yin maganar ba. Ya jima yana juya maganar yana tunanin ta yadda zai iya fa'dawa Yabi a karo na biyu za'a bawa wata saurayinta. Babban damuwarsa irin yadda ya ga ta sanya Nura a ranta. Ransa ya baci fiye da jiya. Ba'kin cikin y'anuwansa ya mamaye shi. Wai me ya tsare musu a wannan duniyar ne? Da k'yar ya yi k'arfin halin cewa "Yabi kinsan ce wa a duniya ba wanda zai so ki, ya so cigaban ki irin ni da gyatumarki ko?" Ba haufi na ce " "Eh Baba". Ya ce "Madallah! Sannan kuma ba wani abin kaico da zai dunfaro d'a mahaifi ya zuba ido ya cimmasa, sai idan abin ya gagare shi. Ina son ki fahimce ni, ki mini adalci, ki kuma ninka biyayyar da zaki mini a wannan karon.". Jikina ya fara tsuma, zuciyata ta shiga zullumi, idanuwa suka cika da ruwa. Na kasa bu'de baki na ce komai dan tsananin bugun da zuciyata take yi. Ya numfasa sosai ya ce "Ina son na fa'da miki auren ki da Nura ba zai yiwu ba, ba kuma na son ki kalli hakan a matsayin shirina ko shirin wani, ki yarda shirin Allah ne, shi kuwa idan Ubangiji ya jarrabe ka, ka yi ha'kuri a farkon al'amarin kana da lada da sakamako mai girma". Take ruwan da ya cika a gurbin idona ya tumbatsa ya fara zuba. Ina jin nauyin da zuciyata ta yi ba zai kwatantu ba. Wacce irin Bak'ar kaddara ce nake gudu take bina da gudu shigen na fanfalaki? Na kasa bu'de baki na ce uffan domin sai na fara hasashen mafarkin da nake yawan yi ne akan aurena da Nura zai iya ruguje wa. Jin shiruna ya sanya ya ce "Na sani kina sona, son da yake sanya ki son duk abin dana haifa, ko nake so. Ina ro'ko ki taimake ni, na yiwa mahaifiyata biyayya, ni kuma zan dauwama ina miki addu'ar wanye wa lafiya da kuma rufin asirin duniya." Cikin rishin kuka na ce "To Babanmu". Ganin irin rudin data shiga sai wata dabara ta zo masa. Sai ya ce "Babanku Iliya ya bu'kaci na bawa Nura Kaltume a madadinki". Na d'ago a matu'kar birkice na ce "Wai me na yi muku ne Baba? Yan'uwanka suna azabtar da ni, kai kuma ka zuba ido kana kallo, ka kasa kare mini darajata! Ko dai da gaske karayar arzikinka tana damfare da zuwana duniyar nan mai cike da ba'kin ciki mai tsanani?" Na fa'da ina kuka sosai. *Auzubillahi! Na yafe miki Yabi! Na sani kina cikin ki'dima ne, ni kaina da na haife ki kiris ya rage ban zautu ba a dalilin wannan al'amarin. Allah ka sassauta, Allah