← Book details Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 146

Sashe 9

Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zaune na tarar da ita tana kullin siga, da yake tana auno rabin kwano tana k'ullawa, idan an zo siyan koko ana siya. Ikilima tana gefenta tana faman barci. Na ajiye ledar a gabanta. Ta kalle ni ta ce "Yabi na sha fa'da miki, jikina na bani sha'aninku da Jabiru ba mai yiwuwa ba ne, ba sa'an auren ki ba ne, gara ki tsaya akan Abdulrashid zai fi mana sau'ki da kwanciyar hankali". Na yi shiru, amma zuciyata sai tsalle take yi. Babban tashin hankalina a duniya shine Gwaggo ta ce mini aurena da Yaya J ba zai yiwu ba. Na yi k'asa da kaina a hankali na ce "Gwaggo fa'da mini dame ya fini da kike ganin yafi k'arfina?" Ta murmusa ka'dan ta ce "Saboda Babanki ba shi da arziki, sun tsere mana, sannan uwarsa tana da buri a kansa, bayan haka ga Mama k'ut take da uwarsa, dan haka zata yi dukkan mai yiwuwa ta sake b'ata lamarin tunda akwai haske a tare da shi, ba zata so wannan hasken a tare da ke ba. Sanin kanki ne kuma mutanen gidan nan baza su dauke ki su ba shi ba, tunda kuna da yawa, zasu yi kwarya tabi kwarya ne a tsakani. Da ace ke din diyar Baban kasuwa ce to, da ba fargabar da zan yi". Na numfasa k'irjina ya daure ainun. Na dinga tambayar kaina shin zan iya rabuwa da Yaya J? Da gaske har lalacewar zumunci ya kai za a iya hanamu aure ba tare da wani dalili gamshasshe ba? Ashe har za'a iya ture karfin jini saboda kawai dan-uwanka ba shi da wadatar abin duniya? Na sauke nannauyan numfashi na ce "Ki daina damuwa Gwaggo! Ban tsananta ba, ban kuma dage sai shi ba. Ki cigaba da yi mini addu'a". Ta sake kafe ni da ido ta ce " Ina yi miki addu'a sosai Yabi, amma zata yi tasiri ka'dai idan kin barwa Allah ya yi miki zabi, kin kuma yak'i zuciyarki akan Jabiru. Ina nufin ki rage zurfafa a al'amariinsa." A sanyaye na ce "To Gwaggo". Sai kuma na zauna ina taya ta k'ulla sigan ina bata labarin yadda ta kaya a tsakanina da Dada. Ta nisa ta ce "Ba kya jin magana ne, ban da hakan mene ne zaki dinga janyo wa tana yi miki mugun fata? Kinsan kuwa bakinta zai kama ki domin ita ma uwa ce a wajen ki". Jikina ya sake yin sanyi, na dinga yin addu'ar Allah yasa na daina tanka mata akan Shehu tunda mafi yawa saboda hakan take fusata. Ta ke tsanata mini, har take yi mini mummunar addu'a. Washagari takwas saura muka d'unguma zuwa makarantarmu ta jeka ka dawo ta gwamnatin jahar Bauchi. Ajin mu hudu wato ss1. Ko wacce tana cikin tsafta, duk inda muka wuce sai an kallemu wataran akan kunnenmu mu ke jiyo yadda ake fadin "y'an Marina ne, kasan yawa ne dasu tamkar tsaki." Ko muji an ce "kai wato gidan Marina akwai zuka zukan zaratan y'anmata fa." Muna tafe ina tambayar Basira da Nazira jiya Dada ta d'ora musu karatun kuwa bayan na tafi?. Nasiba ta ce "Bayan kin bata mata rai yaushe zata iya yin karatu? Kin san kullum sai ta ce haramun ne yin karatun addini a cikin fishi ko a cikin rashin tsarki". Muka k'yal-k'yalale da dariya gaba'daya. Muka isa makaranta hatta Malamai kwarjini muke yi musu saboda yawanmu da kuma yadda muke kama da juna baya ga hakan tare ake ganinmu tamkar kashin awaki alhalin a gidajenmu babu wannan soyayyar da jin kai da ake gani a tare da mu. Lokacin tashi yayi muka dawo a jiga ce a dalilin rana ake yi duk da zafin ranarmu da sau'ki akan ta Bauchi da Jigawa. Wajibi ne idan zamu tafi sai mun shiga mun gaida Dada, haka nan idan mun dawo. Tsabar saka ido da kwakkafin baiwar Allan nan duk wacce bata je ba sai ta ga ne, hakan kuma na iya zama sanadin rikici a gidan, domin bai zame mata komai ba, ta kira uwar yarinya ta yi mata tass, ta ce da sa hannunta y'arta ta raina ta. Kuma abin mamakin idan baka kama sunanta ba, to da kai da wacce bata je ba daidai kuke. Ina tsaye suka dinga shiga suna fitobwa ba abin da ake ji sai "Dada mun dawo, sannu da gida" . Yayin da ita kuma take kama sunan kowa tana cewa "Sannunku da dawowa, lale da y'anmata Dada". Sanin da na yi garina da tsakuwa da ita, ya sanya nake jingirta wa sai na je gabanta sosai ta yadda zata shaida ni da kyau. Tunda kullum sai na je, amma idan ta so ci mana mutunci ni da Gwaggo sai ta ce ban je ba, ko kuma na yi mata gaisuwar gadara da wulakanci daga bakin k'ofa Dan haka da na k'ara wayo sai nake isa gabanta mu hada ido sosai sannan na yi gaisuwar. A gajiye na k'arisa k'ofarmu na tarar da bacin rai domin tsagwaya na tarar an yi a matsayin abincin rana, wani irin nau'in abinci ne da ake sirfa dawa sai a dafa a ci da manja. Na tsani abincin ba dan babu da'di ba, sai dan kawai bana so. Na zauna a tsakar d'akin Gwaggo ina kunci sosai. Ta shigo ta kalle ni ta ce "ban ga kin cire inifom din naki, kin yi sallah kin zuba abinci ba?" Na tumbatsa da fishi ban tanka ba. Ta kafe ni da ido ta ce "Yabi kullum aka yi tsagwaya sai kin tayar mini da hankali? Sanin kan ki ne mahaifinku ya saka takunkunmin siyo abinci a waje ko a ro'ko a wani waje. Me yasa ba zaki rufe ido ki ci dan ta yi miki maganin yunwa ba? Idan kin yi ha'kuri ai wataran barin gidan zaki yi, ranar da Allah ya kai ki dakinki komai kike so sai ki yi wanda bai wuce wadatar mijinki ba". Cikin bacin rai na ce "Ki taimake ni ki bar ni na jika gari na sha, Allah ya sani yunwa nake ji kamar na mutu". A sanyaye ta ce "To ki jika amma nafi son ki dinga ci tunda idan kin ci din ba illah take miki ba." Haka na jika gari na bu'de jakar makaranta na dauko gyada maro na bushe na zuba, ina sha, ina fa'din "ba dan na k'osa ba, da Iklima ta siyo mini madara, to aikenta bana me sauri bane ko wanda yake a matse irina, domin shad'arta ta yi yawa". Gwaggo ta girgiza kai ta ce "Ke dai duk salon k'wadayi kin san shi, ki dinga bin duniya a sannu sannu Yabi". Na yi dariya na ce "Gwaggo tuni aka daina bin duniya a sannu. Saboda gaggawar mutanen cikinta ba zasu bar mai binta a sannu ya kai ga gaci ba, yanzu da nake yin kitso na ha'da da lalle ba gashi muna d'an samun taro da k'wabo ba, da sannu nake bi iya kitson kawai zan yi Gwaggo. Yanzun ma so nake na koyi wata sana'ar na sake ha'da wa domin ina da burin na samu ku'di masu nauyi na jiyar da ke da'di, na jiyar da su Iklima". Ta girgiza kai ta murmusa ta ce "Na gode sosai Yabina! Allah ya ida nufi, amma dai ki bi a sannu da ikon Ubangiji komai zai saukaka a gareki, kullum sai na rokar muku kada a jarrabe ku da rashin abincin a gidan aurenku kamar yadda aka jarrabi Yayarku, ita ma ina fatan da'di ya biyo bayan wannan wahalar da take ciki". A sanyaye na ce "Allah ya amsa bakinki Gwaggo". Ina kammala wa na yi haramar sallar azahar, sannan na shiga wanka dan shirin tafiya Islamiya. Dai-dai lokacin Babanmu ya dawo daga wajen sana'arsa. Gwaggo ce mai girki ta hau hidimar kai masa abinci, a raina sai kiyastawa nake yi ina ma ina da hali na dinga soya masa miya mai d'auke da naman kaji ko na shanu zuk'u zuk'u a ciki. Din ya dinga ci da abinci. Na fito na gan shi zaune a rumfa akan tabarma jikinsa duk ya yi futu futu, ga alamun gajiya mai yawa a tare da shi. Tausayinsa ya tsirga mini, cikin rauni na ce "Sannu Baba, sannu da kokari". Ya dan sassauta ya ce "Sannun ka dai Yabi Asiya". Na dan murmusa domin shi ka'dai ne yake ha'da mini sunan guda biyu. Tunda ya fahimci ina bacin rai idan ba'a ce mini Yabi ba, sai ya kankare kirana da gayan Asiya. Na wuce shi na fa'da d'akin Mama wajen Nazira. Na tarar itama shirya wa take yi. Tare muka fito muka risina muna cewa "mun tafi Baba". Ya amsa da cewa "A dawo lafiya, ku kula da kanku". Muka shiga sashin Baban Tsakiya muka fito da su Firdausi da Saratu. Amma wani irin abu ya tsirga mini mai nauyin gaske, ba dan komai ba illah ganin da na yi Baban Tsakiya yana cin dafadukan shinkafa gefe kuma kunshin balangu ne, ga pure water mai sanyi a gefensa cikin yar bak'ar leda da alamu shi ya shigo da su. A banzan ce ya amsa gaisuwarmu tamkar ma bai ganemu ba. Na tuna gabzar da muka baro Baban Marina yana ci zufa tana yanko masa. A hankali na ce "Àllah ga Yabi! Ka buda mata hanyoyin arziki ta jiyar da iyayenta da'din duniya". Kafin muje k'ofar Baban kasuwa muka yi kicibus da Maijidda, ta fito. Na ji da'din hakan domin shi kam ma tsiyatakunsa sun fi na Baban Tsakiya yawa. Gaba'daya muka d'unguma k'ofar Dada dan yi mata sallama da kuma biya wa Nasiba. D'aya bayan d'aya muke gaisuwar tamkar masu neman tabarraki, kuma dole sai an kama sunanta idan ba hakan ba sai ta dauke kai tabbacin bata karbi gaisuwar ba. Abin da zai biyo baya kuwa ba mai sau'ki ba ne. **** An idar da sallar isha dukkan mun hallara a k'ofar Dada. Sai jiranta muke ta kammala nafilfilinta ta d'ora mana karatu, domin karatun nata ba k'aramin nisha'di yake sanya mu ba. Ta idar ta dinga jan dogon carbinta wanda kafin ka kammala jan k'afa d'aya ma lokaci ne mai yawa. Amma haka muka jira ta kammala. A fili ta cika addu'arta da salatil fatih. Dada tsohuwa ce da bata samu ilimi sosai
Chapter 9 · 0% Book details