Sashe 6
Bakar Taada Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wani ne cikin y'an k'ofarmu baza su bayar ba, daman kuma bamu isa mu ce a bamu ba. Haziki ne na sosai, kwarai da gaske yake ja, amma lalacewar da ya yi ya sanya da k'yar ya iya kammala Diploma a kwalejin Tatari Ali data ke cikin Bauchi. Ya riga su Yaya Salisu samun gurbin karatu a jami'ar amma yak'i mayar da hankalinsa akan karatun har sai da aka kore shi. Hankalin mahaifinsa ya yi tashin gauron zabi, domin zaryar da ya dinga yi tsakanin Bulkachuwa zuwa Toro ba ka'dan ba ce. Haka ya sake samo masa yin diploma akan shaanin tsaro da tafiyar da gwamnati wanda da k'yar ya kammala dan ma shekaru biyu ne. A hakan kuma sakamakon ya yi kyau, domin ya wuce fallasa. Duk da hakan Babansu bai bar shi ba, sai da ya sake samo masa gurbin karatun digiri a jamiar jahar Bauchi ta garin Itas-gad'au. Inda zai karanci ilimin halayyar dan Adam. Wannan kam da taimkon Ubangiji ya kammala domin ba ya zuwa sai an kusa fara jarrabawa, sannan bai fasa al'amari da y'an mata ba. Shekaru biyu da rasuwar mahaifinsa kenan. A kuma wannan shekarar ya tafi bautar k'asa, da shekara ta dawo ya kammala. Yanzu zaman kashe wando kawai yake yi. Sai dai yana yar buga bugarsa domin kusan kullum sai ya je Bauchi. Haka ya dinga satar jiki yana siyar da kadarorin da ya mallaka. Abin kaico kuma ba komai ya yi da kudin ba sai sharholiya da burga a mata. Wani k'aton fili a Bauchi kawai ya tsira da shi, shima dan an zuba masa matakan tsaro ne. Yau da wata sana'a yake da ku'din ko kuma wani gini yake fa'da'da wa da an samu sau'kin bacin ran da ake ciki. Ya zauna kusa da Nazira da take kusa da karshen tabarmar. Murya ba amo ya ce "Madallah da Dada da y'anmatantanta". Duk suka hau rige rigen gaishe shi Amma ban da ni. Ya amsa hankalinsa na kaina. Ya kasa ha'kuri ya ce "Asiya Toro how far?". Na yi banza da shi. Domin dai na tsani yadda yake gatsa ainihin sunana, dan kuturun wula'kanci har sai ya ha'da da Toro. Kusan kowa Yaya Bulkachuwa yake ce masa, ni da bama shiri bana ce masa Yaya Bulkachuwa. Amma sai nake mutuntunta shi wajen kiransa da Yaya Tijjani amma bai yaba ba, bare ya gode. Yabin da zai ce ne yake ganin asara saboda an cika zuciyarsa da k'yashi. Shi yasa nima na janye yayan tuntuni nake gatsa Tijjani gatsal wanda na lura shi ko oho. Ina nan, ina kallon wadanda basa ce mini Yabi, duk ranar da Ubangiji ya sanya na je Saudi akan girma da hankalina ko tsarabar abin da ba'a so ba zan basu ba. Tijjani na cikin sahun farko. Yaya Ummi ce mutumiyarsa, baya zuwa gidan kowa amma yana zuwa gidanta, har idan da ku'di a tare da shi ya yi wa ya'yanta alheri. Sosai suke d'asawa, mutimiyarsa ce ta sosai. Dada ta fusata ta ce "Mugun nufi ya k'are miki Yabi! Ko wacce ta gaishe da dan-uwanku amma ban da ke, bai yi fishin wula'kanta shi da kika yi ba, ya sake bu'de baki ya yi miki magana amma kina ji sarai kin k'yale shi, saboda ke din kina gaji nunkufurci da ba'kin hali ko?" Raina ya baci domin a kullum kalaman Dada a kaina kenan, bansan me Goggo ta tsare mata da a kullum sai ta jingina mata munafurci da ba'kin hali ba, ko da yake na taba jin labarin cewar tun haihuwar Yaya Ummi da dangin Goggo suka zo suna daga garinsu na Kangire cikin k'aramar hukumar Birin Kudu suka fuskanci wulakanci daga wajen Mama. Shikenan duk haihuwar da take yi basu sake yin gayya sun zo ba. Sai dai a samu mutum biyu su zo su ganta washagari su juya sassafe. Wannan matakin da suka dauka shine ya zama laifin da yak'i wuce wa a wajen Dada da take ta musguna mata da gorin ba y'ar babbar haula ba ce, sannan yan'uwanta masu k'ullaci ne, duk kuma cikin matan gidan mahaifiyarmu ce kawai bata da kowa a garin Toro shi yasa ma wani abin ake yi mata da gan gan. Duk da ba jin dadin zaman take yi ba, ta jure dukkan kalubale dan kawai ta zauna da mu yaranta, amma bata tsira ba tunda Babanmu ma haka siddan sai ya dauke mata wuta na tsawon lokaci mai yawa. Mama kuwa bata fasa yi mata yankan baya a duk inda ta zauna ko ta samu damar yin hakan ba. Ko yaushe Gwaggo a cikin mutuntunta Dada take hatta wankin kayanta har yau bata daina yi mata ba, amma babu gwaninta bare yabawa. Nan da nan na tunzura na ce "Da yake shi kina jin tsoron kada ya keta ki shiyasa kike fa'din hakan. Amma ni kin bu'de baki kina niyyar tozarta ni. Tunda ban gaishe shi ba, ya yi mini magana ban amsa ba, ba sai ya rabu da ni ba? Bana son harka da shi ne, a duniya na tsani sunan da yake kirana da shi. Sannan idan zai mini magana sai ya lanjare murya, kuma kinsan dai ba sosai nake ji ba, bare na ji shi da kyau". K'wafa ta yi tare da cewa "Kowa ya yi na gari ai dan kansa Yabi". Basira ta ce "Yi ha'kuri Dada d'ora mana karatun kawai". Ta rausayar da kai gwanin tausayi ta ce "Kayya Basira zuciyata ta jagula ainun karatun nan sai gobe kuma". Firdausi ta ce "Yaya Bulkachuwa saka baki Dada ta d'ora mana karatun, bata ha'kuri mana". Ya kalle ta ya ce "Dadarmu share kawai, nima na ha'kura ai. Kinsan hankalin Asiyan Toro a k'auri yake". Na sake hauro wa na ce "Tijjani ka bari, ka ga dai bana shiga harkarka akan me zaka nemi takure ni ne? Gaskiya bana son haka". Dada ta sake yin k'wafa tare da cewa "Yabi kin janyo muku, domin na lura tashen balaga kike ji, zan kuwa yi maganinki." Kafin wani ya yi magana sai ga Ikilima k'anwata da a yanzu take shekaru tara. Ta shigo cikin nutsuwa ta kalle ni ta ce "Adda Yabi ki zo". Da azama na mike domin nasan Yaya Jabir ne. Saurayin da yake gigita zuciyata da ruhina. Ban ce komai ba, na mike ina cewa "Sai da safenku". Dada ta bimu da ido tana cewa "Jabiru ne ko kuwa wani ne?" Ban kula ba, ba kuma wacce ta tanka. Domin dai na fi su farin jinin mane ma duk kuwa da ba finsu kyau na yi ba, asalima wasu sun fini kyau, sun kuma fini cikar mace. A bakin kofar Shashenmu ya jingina. Matashin saurayi mai cike da nutsuwa da kamala. Wankan tarwada ne, siriri mai matsakaicin tsayi, mai sanyi a halayya da kuma dabi'a. Bashi da kwaramniya tun tashinmu, mai hakuri ne na gaske, da wahalar gaske ka ga fa'dan Yaya Jabir. Sosai muke shiri da shi, duk kuwa da ni din mai tsiwa ce, mai kuma hayaniya ce. Amma jininmu ya ha'du sosai. Kusan tun soyayyar kuruciya ce ta rikide ta zama ta gaske. Dalibi ne a jami'ar tarayya ta Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Ajinsa uku sawess yake yi a cikin Jos. Sannan ya yi sa'a ma'aikaci ne a karamar hukuma da aka dauke shi aiki da sakandire a lokacin kawunsa kanin mahaifiyarsa kansila ne a yankin gundumar Toro. Na isa gare shi, yana sanye cikin farin yadi fari k'al. Wato duk samarin gidanmu babu mai tsabtar Yaya J. Ina jin da'din k'iransa da Yaya J. Na lura shima ba karamin son sunan yake yi ba. Ni ka'dai ce nake fa'da masa hakan kuma. Kusan halayyarmu daya ni da shi, domin nima tsabta ce da ni, har fa'di ake yi aljanun tsabta ne da ni. Baya ga haka muna da son y'anuwanmu, bama jin k'yashi wajen salwantar da duk abi da yake namu ne akan d'an-uwanmu, har rashin girman jikinmu iri d'aya ne. Shine d'a na farko a bangaren Baban Tsakiya. Mutane da yawa suna fa'din kama muke yi ni da shi, ni kuma bana ganin kamar kawia dai yanayinmu ne daya tunda shi din ba wani girma ne da shi ba, haka yake dan madaidaici avarage height ne. Haka nima duk cikin y'anmatan da muka taso ko wacce ta fini tsayi, bani da tsayi, nafi kusa da gajerta. Ina da gashi sosai, sannan ina da manyan idanuwa baya ga hakan fara ce sosai. Yadda nake yar cif cif sai nake matu'kar daukar hankalin mutane. Kullum idan zan fita sai Gwaggo ta ce ban da wulakanci Yabi, domin al'adar gidanmu ne yarinya bata kammala karatun sakandire. Shekaru sha biyar ake aurar wa, amma mu da alamu za'a bari mu kammala duk da dai Dada ta fara fa'din mu shirya dama kuma ita ce take matsa lambar sai an yi aure. Ya zuba mini ido babu walwala jikina ya yi sanyi na yi kasa da kaina ina fa'din "wannan kallon tuhumar fa Yaya J?" Ya saki gauron numfashi ya ce "kin kama kanki da kanki Yabi. Jiya ma fa sai da kuka tsaya da yaron nan dan gidan Sarkin k'ofa ko?". Na yi murmushi na ce "Ai dai baka ji me na ce masa ba". Na fa'da cikin shagwaba shagwaba. Ya sake yin kasa da murya ya ce "Ban ji ba, amma yanzu fa'da mini na ji". Na yi k'asa da kaina na ce "Na fa'da masa cewar ni bana sonsa akwai wani bawan Allan da ya riga shi yin wuf da zuciyar Yabin Marina". Ina kallonsa ya dan murmusa ya ce "Waye wannan bawan Allan?" Na dago amma ban kalle shi ba a dalilin hasken kwai na kanmu. Na juyar da fuska na ce "Yaya J mana". A wannan karon murmushi mai sauti ya yi. Ya nisa ya ce "Yauwa Yabin J, kin biya ni. Amma idan kina son ki burge ni, ki daina ma sauraronsa ba shi kawai ba, kowanne namiji ma. Sannan ki daina fa'da dazu ma sai da kika yi dambe da Saratu. Kin ta'ba gani na ina dambe?" Na girgiza kai tare da cewa "Ha'kuri ne ya yi maka yawa, ni kuwa bani da shi, domin duk wacce ta ta'ba ni ba zan k'yale ba" Ya girgiza kai ya ce "Ha'kuri fa